← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 57

Sashe 3

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido Rufaidah ta fara bu'dewa a hankali ta saukesu ga mutanan dake cikin falon da take ganin mutanan bishi bishi ta dau tsawan mintina a haka kafin mutanan falon su ankara da yanayinta alamar ta fara farkowa daga doguwar sumar da tadau lokaci bata farko ba tun karfe biyu har yanzu da duhun yamma yayi Gaba daya suka fara yi mata sannu muryoyinsu ne suka fara yi mata amo a kunnenta cikin rashin tsammani wannan yasake tabbatar mata mutuwar AbdulWahid mijinta gaskiya ce idanunta tasake budewa tangaram ta maida dubenta ga Umminta da Gwaggonta da Momynsu sai kuma Luba da Yusuf kekan jinyarta tana jijjigasa dukkansu babu cikakkiyar walwala a fuskarsu Rufaida da sabon kukan da ta fara ya ruda mutanan dake dakin tuni zuciyar Hauwa wato Umminta ya kara tashi wanda dama tun bayyana musu mutuwar AbdulWahid hankalinta yake a tashe har sukazo Zariya da hankalin nata ya sake tsanantar tashi ganin 'diyarta ta Rufaida a cikin mawuyacin hali da yanzu hakan zuciyarta ta karaya na tausayin 'yar ta kuka itama ta fara cikinsu aka rasa mai lallashin 'dan uwansa Gwaggo ce take kokarin lallashinsu tana ban baki tana cewa duk fa wanda ya mutu baya dawowa kuma duk mai rai hakika mamaci ne muma lokaci kowannenmu yake jira hakuri zakuyi da yi masa addu'a halinsa na gari ya bisa danshi AbdulWahid tashi tayi kyau da izinin Allah,da wa'dannan kalaman ta cigaba da lallashinsu har ta fara janyo hankulansu,da haka tasamu kansu hatta Rufaidan shiru ne tayi sai hawayen dake bin kuncinta tanamai sake tuno rabuwarta da mijinta da hirarsu ta karshe yanzu shikenan mutuwa ta yanke kauna itada mijinnata yayi tafiya mai nisan da babu waiwaye tafiyar ta kasance a bigiren da ba'a dawowa har abada ba'a dawowa mutuwa kenan mai yanke buri wani irin hawaye masu dumi suka cigaba da zubo mata lalle mai rai ba a bakin komai yake ba duk wanda yamanta da wannan ranar saidai yayi maza ya koma ga Allah domin yau dai ga wannan bawan Allahn ya tafi ba tareda yasan yau zai mutu ba mutuwa kenan da bata kwankwasa kofa kome kake idan tazo haka zata daukeka Allah yasa idan ta mu tazo mu cika da kyau da imani

Bangaren Hajiya Jamila

Yasir dake zaune a falo ya takure a tsakanin kujera inda yake kallon Hajiya Jamila da mutane guda biyu dasuke kanne a gareta Kaltume da Haulatu da 'daya take aure a Kaduna daya kuma a makarfi hira suke Hajiya Jamila tana basu labarin yadda taga fuskar dan nata kafin rai yayi halinsa kai baza kace Hajiya Jamila bace da dazu take kururuwar mutuwar amma cikin awannin da busu kai ga kwana ba harta mance tafara bada Labarin mutuwarsa itada 'yan uwanta kuma a gaban karamin yaro,Kaltume ce da itama Umma take cewa Hajiya Jamila a matsayinsu duk ita ta rikesu harta aurar dasu,ni yaron nan bansan kukan da yake ba yabarmu muji da mutuwar da akayi mana yaki,Hajiya Jamila tace yaron da aka cusa masa kiyayyarmu taya zai daina Hajiya Jamila ta fashe da kuka,Haulatu ta miqe tayi kansa taja hannunsa da karfi ta cankadasa kofar da zai sadaka da dakunan gidan Hajiya Kubra da take kokarin fitowa ta zauna falon saboda masu zuwa gaisuwa makofta nan Yasir ya fado jikinta,Hajiya Kubra ta kalli haulatu tace Haulatu mai yayi zafi har haka,sai kace ba jikanku ba kuma maraya Zaki cankadosa yanzu da Allah bai kawoni ba kila har fasa baki zaiyi idan da tsautsayi,Kaltume dake zaune tace Mama sunan da suke fadawa Hajiya Kubra ta cigaba da cewa yaron da mahaifiyarsa da kakanninsa suka cusa masa kiyayyarmu a ransa,Hajiya Kubra tace yanzu dai komai yawuce wanda ake abun danshi yau ina yike bayanan,yanzu cigaba da maganar nan dawo da bara bana ne da jawo Bacin rai yanzu muji da mutuwar da akaimana babu ko daya daga cikinsu da tari ya sille masa saboda koba komai dai mutuwar su akayiwa amma zuciyar ko wannensu da tunanin da yake akan matakin da zasu dauka dan ita bangaren zuciyar Hajiya Jamila yadda zatayi ta fitarda su Rufaida daga rayuwarsu take dukda ga mai hadawa nan Yasir ya riga ya hadasu wanda ko ya mutu acewarta ya mutu ta rayayyun 'ya'yanta take a yanzu domin badan yadda taga gawar AbdulWahid ba to da hankalinta bazai tashi har yasa ta kasa maida raddi ba gurin Hajiya Kubra Hajiya Jamila macace mai matukar son duniya shiyasa ma mutuwar dan nata baisa ta rage kudure kuduren duniya ba da take yi kuma babu daya kwakkwara na gari da za'ace

Hannun Yasir Hajiya Kubra ta kama zuwa cikin gidan tana lallashinsa har dakin dasu Rufaida ke ciki ta kaisa inda yana zuwa ya fada jikin Rufaida uwa a garesa yana kuka itama Rufaida hawaye take sai dai bata bari ya gane ba ta cigaba da jijjigasa har barci ya daukesa,nan Hajiya Kubra ta cigaba da yimata nasiha a haka ta fice daga dakin tana goge kwallar tausayin yarinya karama Rufaida gashi ta zama bazawarar da yau Allah ya dauke mata mijinta da yabarta da da da yanzu yazama maraya dukda bazaman farin ciki tayi da mijin nata ba to ina sirikar tabarta tayi haka amma hakan baisa yarinyar korafi ba daidai da rana daya ba hakuri gareta mai yawa dukda wannan abun da yafaru wanda ake danshi baya duniyar baisa kiyayyar da Hajiya Jamila kewa su Rufaida raguwa ba batare da Hajiya Kubra tasan laifi 'daya kwakkwara ba dayaja hakan ba rayuwar dama haka ta gada wasu kome zakamusu bazasu kaunaceka ba

Abba Bukar da yake zaune gefen gado wajen karfe tara na dare da haske ya gauraye 'dakin na lantarki Hajiya Kubra ta shigo 'dakin dauke da sallama da Flask riqe a hannunta Abba Bukar ya 'dago fuskarsa da take cikin damuwa ya amsa mata kafin ya maida kansa ga inda yake kallo a kan lokar jikin gadon 'dakin Hajiya Kubra ta zauna ta fara magana cikin sanyin murya da cewa"Abba dukkan mai rai mamacine AbdulWahid ya tafi inda ba'a dawowa damuwar bazata dawo dashi ba Addu'a ce yakamata mudinga yi masa"
Kai Abba Bukar ya 'daga alamun ya gamsu da abinda Hajiya Kubra ta fa'da kafin yace" Kubra mutuwar yaron ce tazo shiba ciwo yayi ba rana tsaka yayi hatsarin motar nan ni koma a waya bai fadamin zaizo ba ashe ajali ne yakirasa,gashi kaf cikin yarana babu wanda kai tsaye zakace yabar abu ya bari kai tsaye inbashi ba gashi da kokarin kyautata mana dason yan uwansa"Abba Bukar ya karasa maganar yana zubda hawaye lalle duk abinda zaisa Abba Bukar koda hawayene babban abune tabbas duk abinda Abba Bukar yafada gaskiya ne saidai kuma ya za'ayi wanda yafimu sanshi a amshi abinsa,Hajiya Kubra ke wannan tunanin a cikin ranta Hakuri ta cigaba da basa kafin yace su Haulatu mungaisa sunyimin gaisuwa dazu kuma abin shirmen anan da mazajensu da suka kirani a waya yimin gaisuwa suka fadamin cewa sai anyi bakwai zasu koma saida ma na dinga fada tunda wanda ya mutu bazaidawo ba,amma ko wacce tabaro yaranta ta taho,kuma suda ba jin magana suke ba kafin su koma sai sun hargitsamin gida najima da halin yar uwartasu danike aure wannan ai shirmene da anyi uku duk kowa zai koma gidansa Hajiya Kubra hakuri ta shiga basa

Washe gari da wuri Kabir ya shirya zasu koma Abuja shida matarsa sai ana gobe addu'ar uku zasu dawo su kwana ayi addu'a su taho inda Luba zata tahowa Rufaida wasu daga cikin kayan sawarta Yasir ganin Kabir zai tafi yafara cewa Kawu akaini Dady na kukan da Kabir yake maqalewa yafarayi inda tun a falon da yaje musu sallama zuciyarsa ta karye da ya tuna cewa shida AbdulWahid suka saba zuwa muddin wani dalilin yakawosu Kaduna sai sun karaso Zariya kai kobama haka ba gidansu AbdulWahid kamar gidansu Kabir ne tun sanda suka hadu a jami'ar Ahmadu Bello University shiyasa yake tuno falon gidan dakoda yaushe zuri'ar gidan suke zaune a ciki bazaka rasa koda mutum daya ba a kowacce rana ta duniya ba barema zaman ake da yawa ana hira cikin so da kauna harda Abba Bukar uba garesu hakama idan sun biyo da Kaduna a wannan falon zasu zauna aita fira cikin raha da wasa da dariya da girmama juna yau ga yadda abun yakasance gasu a falon amma babu jigon da yayi sanadiyyar sanin wannan a halin da yayi yau yanacan a wani bigiren na daban da muma jiranta muke wannan bigiren na mutuwa da kowa jiran lokaci yake
Kabir da harya Shiva mota amma yanajin sautin kukan Yasir nan Abba Bukar da kansa yasa Yasir a mota su tafi tare da shi

Koda Labarin mutuwar yazowa gurin aikinsa sunji mutuwar sosai dan AbdulWahid mutumin kirkine yasamu shaida mota sukayi washe gari suka nufo Zariya suda wasu 'yan sandan da suke a cikin barraq din nasu buhun shinkafa katan din taliya couscous da kudi masu yawa suka kawo musu a riqa dafawa wani babba a cikin su nauyin karatun Yasir ya dauka da za'a bashi yaron da yafi kowa son hakan domin duk abinda zaiwa AbdulWahid bazai biyasa shi abinda ya masa ba sanda ya shiga matsala ya taimakamasa sosai sun nuna halalci sosai abokan aikin nasa sosai koda Kabir yakoma abokansa da suke aiki tare haka suka riqa yimasa ta'aziyya kwanansu daya su Kabir suka juyo saida aka lallashi Yasir cewa Abbansa yatafi wani aiki sai yayi girmaan za'a kaishi gurinsa da haka aka samu yafara hakura sai dai jefi jefi idan yana rigima ya riqa maganar mahaifin nas_JININMU DAYA_
(Labari mai dauke da son zuciya)
Na
Sadiya Ibrahim Khali

3
_A ranar da akayi ukun AbdulWahid ranar Abba Bukar yacewa su Haulatu kowacce tabi mjinta takoma saboda ya fahimci ganin cigaba da zaman nasu zai iya kawo hargitsi,koda Hajiya Jamila taji haka abinda Abba Bukar yace bata tada wata fitinar ba dan a yanzu ne mutuwar 'dan nata take dokarta don tafara zubar da makaman aiki saidai bata zubar dana 'kiyayyar da takewa Rufaida ba har yau kai bama ga ita ba harga jininta kiyayyar ta shafesa,wadda dama 'kiyayyar tadade da wanzuwa,_
Chapter 3 · 0% Book details