Sashe 37
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"ZARIYA"
"Wasila mikomin wayata naga tana kara an kirani"
Hajiya Jamila tayi maganar da suke zaune da sauran matan gidan a babban falo suna fira wasila da itace ta rage a gidan bata zuwa makaranta ta dauki wayar tana game
Wasilar ta danne wayar silent
"Umma bafa kira a kaiba sakone ke shigowa"
Aunty Amarya da take kusa da Wasila ta le'ka wayar
"Kai Wasila kema kin iya karya ko ga kirannan yana shigowa kin danne wayar a silent"
"Hajiya Jamila jin maganar Aunty Amarya yasata mikewa ta anso wayarta da har wani kiran ya shigo wancen ya katse,tsaki tayi ganin mai kiran Gwaggo Lariya ce kanwar surikarsu ,tasan tunda taga kiranta roko zatayi saida takoma ta zauna ta daga wayar da sallamarta saida suka gaisa Gwaggo Lariyar da labari ke cinta ta fara da cewa
" Gaskiya Jamila kin bani mamaki duk aminci na dake ace za'akai kayan lefen AbdulWahid saidai naji labari gurin Bukar"
Tsaki Hajiya Jamila tayi ka'dan ba tareda Lariyar ta jiba,ita to ta ina zata zama kawar Gwaggo Lariya bare suyi aminci bayan kanwar surikinsu ce itace Autar a gidan su surukin nasu ,shiyasa bata Gwaggo Lariyar bata girmeta ba,kuma Gwaggo lariyar takeso suyi aminci,saidai ita taki jinin mutum mai shishshigin da karya,da son abin hannun mutane, da Gwaggo Lariya dukta kware ta wannan fannin shiyasa yanzu ta kasa gasgata maganar Gwaggo lariyar ta dai daure tace
"Wacce irin magana kike ne,wanne irin laife kuma ni bansan wannan zancen ba"
Da mamaki sosai jin maganar da Hajiya Jamila tayi Gwaggo Lariya ta cigaba
"Kamar ya kina nufin ba kisan auren da Wahid zaiyi ba zai auri Rufaida ta wajen Aliyu"
Cikin firgici Hajiya Jamila ta ce
"Haba Gwaggo Lariya wacce irin magana ki kene"
"Abinda kika ji nace,Wahid zai auri Rufaida yauma su Hauwa'u zasu taho zariya gurin biki nufinki basu fadamiki ba..."
Ba tare da Hajiya Jamila takarasa jin zantukan Gwaggo Lariya ba ta kashe wayar ta mike zunbir
Mai yafaru ne Maman AbdulMalik ,lefen wa za'a kai"
Aunty Amarya tayi maganar cikin rashin sani ,dan itama ko kadan batada masaniya da saka ranar bikin"
Wani kallo Hajiya Jamila tayi mata da haka ta shige daki ta dauko hijabi da dan makullin motarta ta dawo falon tana kokarin fita Hajiya Kubra tayi kokarin riketa
"Haba Hajiya Jamila komai yayi zafi maganinsa Allah,mai Gwaggo Lariyar tace miki ko mutuwa akayi ne, ki fadamana"
Fisge hannun Hajiya Kubra ,Hajiya Jamila tayi daga rikon da ta mata cikin zafin zuciya ta fara magana
"Munafuka cikani,kunje an hada baki daku an munafurceni, wallahi yau sai na kashe waccen yarinyar da take kokarin shiga rayuwar dana,saidai nima yau akasheni ,dan dana hada zuriya dasu gwara na hada da kare"
Tana kaiwa nan ta fice daga falon gurin motarta ta karasa ta mata key ta bata wuta tavar gidan da wani irin gudu
Cikin sanyi jiki Hajiya Kubra ta dawo cikin falon Aunty Amarya ta kalleta bayan ta zauna ta soma magana
"Niko Maman Hussaini mu kira Gwaggo Lariyar muji maike faruwa,sai mukira Abban Wahid mu fadamasa,dan a yadda Maman Abdulmalik ta fita kinsan komai zai iya faruwa"
"Eh hakane kinyi tunani nima zullimin da nike kenan ,tunda gashi har tana kiranmu da munafukai"
Hajiya Kubra ta karasa maganar tana daukar wayarta ta lalubi numbar Gwaggo lariya
Wadda Gwaggo Lariyar tana can cikin zullumi dan sai yanzu tayi danasanin katobarar da tayi na fadawa Hajiya Jamilar dan tana tsoron hukuncin da zata dauka kan wannan maganar,tana wannan tunanin haka taji karar wayarta ta bugu daya ta dauka ta kara kunnenta,
Hajiya Kubra ta maida wayar a handsfree jin ta saga
Magana Gwaggo Lariyar ta fara
"Assalamu Alaikum ,Kubra lafiya kuwa,ina Jamilar ,muna waya naji ta katse ,dama batun auren Wahid fa Rufaida muke da za'akai lefe yau...."
Hajiya Kubra da bata bari Gwaggo Lariyar ta gama maganar ba tayi hantsarin katse wayar ta sake danna lambar Abba Bukar a kidime tana gudun mai zaije yazo,dan tana da yakinin gidan Gwaggo Zainabu Hajiya Kubra ta nufa
shima ringing daya ya dauka da sallamarsa
Ba ta jira sallamarsa ba tace masa
"Abban Wahid yanzu Gwaggo zainabu ta kiramu,tace ka aje duk abinda kake kaje tana san ganinka" da haka ta katse kiran dan bataso ta fadamasa gaskiyar lamarin saboda gudun kada hankalinsa ya tashi,lamarin suke tattaunawa akai bayan gama wayar tasu dan ko ita Hajiya Kubra ba tasan maike faruwa ba itada take 'yar uwarsa ,a ranta tana fadin amma Gwaggo Lariyar bata kyauta ba ,a matsayinta na kanwar mahaifiyarta shiyasa bata fito ta fadawa Aunty Amaryar ba don kowacce matsayinta daban ne agurinta
Tunanin kiran Gwaggo yake da yaga ita bata kirasa ba ta shaidamasa ba,kuma bata Saba yi masa kiranba ma,to mai yake faruwa ganin tunanin ba zai anfanesa ba ya sashi mikewa ya dauki makulle ya fito daga office dinsa ya rufe,massinjansa da ya tare sa,Abba bukar yace
"Ba tashi nayi ba,zanje wani guri na dawo,idan anzo ne mana kace ba nisa nayi ba su jira ni"
"To Allah ya kiyaye hanya masinjan ya fa da ya koma inda yake zaune"
"Amin kawai Abba Bukar ya iya anbata yabar wajen gurin aje motoci ya karasa ya shiga tasa ya tayar ya fito daga cikin makarantar ABU Zaria da a ciki yake aiki da tunani a ransa
****
RUFAIDA
Rufaida ta kalli himmin fulawar da Gwaggo take so ta kwaba tayin doughnut da cin-cin,da ta tasata saita kwaba zata bar gidan zuwa gidan Gwaggo Hajiya mahaifiyar Hajiya Kubra
" Gwaggo Allah na gaji ace aikin nan duk tare za muyi,maimakon ki bari su Aunty Samina su zo tunda yau zasu zo"
Rufaida ta karasa maganar tana kunbura baki
Gwaggo ta 'dago dakanta daga kwabin alkakin da take ta dubeta taga ta kunboro baki ta ta tabe baki tare da cewa
"Yarinya koda ma kuka zaki ba ba kunboro baki ba saidai kiyi,dan sai kin kwaba zaki bar gidan nan"
Rufaida ta dan lankwasa murya
"To Gwaggona naji zanyi yadda kikace amma dan Allah kiyarda na kira Harira ta tayani,muyi mugama da wuri"
Gwaggo ta zaro ido
"Wacce Harirar yarinyar da ko uwarta bata mora mata bare ke ta mora miki daga kawancen unguwa kinajin artabun da suke da Mamarsu ta katanga akan aiki,idan Mamarta tace tayi mata"
Kasancewar su Harirar makoftansu ne da suke shiri da Harirar a Unguwa itada Rufaida
"Eh dukda haka Gwaggo nasan ni zata tayani kinsan muna shiri sosai"
Rufaida tayi hanzarin cewa Gwaggo hakan dan karta kuma fadar wani abun
"To inanan dai zan jiyo ku ta katanga,dan indai Harira ce kinsan ba shiri ba kome kuke idan vatasa kanta ba saita iya watsa miki kasa a ido"
Da haka Rufaida ta mike daga tabarmar da suka shimfida a tsakar gidan ta zura takalmi ta janyo hijabinta jikin igiya tasa tana cewa
"Gwaggo saina dawo"
"To adawo lafiya'"Gwaggo tayi maganar tana maida kai ga abinda take,a ranta tana tunanin halin Rufaida batasan auren yaron kowa ya sani badan komaiba saidan halin mahaifiyarsa amma ko a fuska vazaka gane ba