← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 57

Sashe 24

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
"Rufaida gaskiya kinyi sa'ar masoyin gaskiya samun masoyi kamar Ra'uf a wannan lokacin abu ne mai matukar wahala Dan inada yakinin da gaskiya yazo aurenki zaiyi dan Allah ki riqesa hannu bibbiyu dan yanada kyakkyawan hali,Ahmad yasha fadamin kyawawan hali irinna Ra'uf kuma yafadamin da gaske yake sonki har sun kira Abbanmu sun shaidamasa zasu je tanbaya kuma yanaso kafin yakoma Delhi ya tura magabatansa asaka rana ayi komai""
Rufaida da take kokarin gyara kayan jakarta takalli Samiha
"Gaskiya ne Samiha insha Allah zan riqesa da hannu bibbiyu ina godiya kawata"
"Babu komai kawata nidake tamkar abu daya ne,ina tunanin nama fiki jindadin hadin nan"
Ido ta zaro
"Eh mana dan yaya Ra'uf yace min bakya wani sansa kike nuna masa"
"Kijimin da mutumi idan ba goyasa ya keso na riqa yi ba bansan maiyakeso nayi ba"
"A to kidai gyara dan gaba kadan mijinki zai zama dan nama rage miki zance ban fadamiki Abba dazu ya kira Ahmad a waya yake shaidamasa Abbanku ya masa izinin zuwa gurinki zance yamace basai sunzo Kanon ba,kinga nanda wata shida zamusha biki ni tuwona maina abu namu"
Ni kinga ki kyaleni haka da wannan maganar tayi maganar tana mikewa
"Au zamu rabunma shine zaki mike kibani guri"
Hannun Rufaidan ta riko
"Yi hakuri kawata dawo ki zauna,tunda abin na laifi ne dan na miki maganar rabin ranki kuma gaskiya na fadamiki"
"Wani gaskiya indai irin wannan maganarce banaso"
"Zaki sone malama ki kyaleta samiy ina tunanin tafara jin kunyar mune shiyasa bata san mu riqa mata maganar Ra'uf din"
Nasiba tayi maganar tana karasa zama a bakin gado dan duk tanajin mai suke cewa dan ta shiga bandakine sanda suka fara maganar"
"Allah ya kyauta min jin kunyarku ai indai naji kunyarku gaskiya na fado"
"Eh lallai fa munyarda,kuma indai ba kunyar bace mai zaisa kice abar maganarsa"
Inji Nasiba
"Saboda kuna sawa zuciyata da kunnuwana da idanuna son ganinsa dan jin muryarsa da sauraron sakon da zai isar ga zuciyata"
Rufaida tayi maganar kamar ba ita tayiba Dan tagaji da maganar Ra'uf da suke mata dukda yadda xuciyarta ta aminta dashi lokaci guda da har mamakin kanta take dukda cewa kuwa tun ranar data taba sasa a idanunta take yabon halayar saurayin a ranta dan ko alamun fushi bata gani ba a fuskarsa ba tadai kawar da mamakin son da take masa da ya shige ta farat daya Dan babu mamaki da ikon Allah,dariyarsu ce ta maidota daga tunanin da take"
Dariya maganar tata da tayi ta basu kuma sunga tayi shiru kamar ba ita ta yi maganar ba,nan suka hada baki gurin cewa
"Allah ko yayi masoya"
"Nasiba ta furta
" ni kunga bari nayi sallar walhar nan nayi alwala na zauna fira"
",dadai yafi miki da kin zauna in kunji kunji"
Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin dakin
*"**"**********
Abba Aliyu yayi murmushi bayan ya cire wayarsa daga kunnensa ya maida kallonsa ga Ummi Hauwa'u da Abdul-Rafi da suke saurarensa suji mai zaice musu dan sunsan dai da ganin murmushin fuskarsa akwai magana mai dadi a bakinsa
"Hauwa'u kinsan dawa na gama waya,Alhaji Hashim ne yanzu ya kirani ne akan cewa wani abokin Mijin Samiha ya ga Rufaida wajen bikin yace yana sonta to yanzu dai Abba Hashim din yace ya ari bakina ya cumin albasa gurin amincewa yaron fara zuwa zance,su dan fara fahimtar juna kafin ya turo magana
Abdul-Rafi ne ya soma magana dalilin da ya sa Ummi Hauwa'u ta maida maganar da take kokarin yi sai dai murmushin farin cikin dake kan fuskarta sai kuma taji Abdul-Rafi 'din yayi wata magana
"Allah yasa nagari ne" fadin Abdul-Rafi da tunda aka fara maganar yaji ransa yafara baci da baisan dalilin fadin hakan ba"
"Wacce irin magana kake ne wai Abdul" Ummi Hauwa'u tayi maganar tana kallonsa
"Ummi addu'a nayi mata fa"
Injishi yana kokarin mikewa danko maganar ma saiyaji duk ta gundiresa
Abba Aliyu yasa baki a lokacin yana fadin
"Saboda haka ake addu'ar dama ko,kai wai maiyasa bakada wani tunani kafin kafurta abu kamar wani karamin yaro,duk fadan da akema bakaji"
"Abba kaya hakuri bada wata manufa nayi maganar ba"yana maganar yana karasawa wajen dining
" ai dama haka zakace sakarai kawai"
Ummi tayi maganar cikin bacin rai
"Abdul yana kokarin zama a kujera yaji furucin Ummi Hauwa'u yaji le'ben kasa matukar haushi kalmar Sakaran da ummin nasu takirashi dashi yaji
" Haba Hauwa me ye haka ya zaki ce masa sakarai yanzu da a gaban kannensa kika fadamasa ai rainasa zasu yi"
Abba Aliyu ya fadi haka.
"Allah Abban Abdul yaron ne baida tunani wani lokacin ko daya sai shegiyar wauta ya iya"
"To naji dukda haka kidaina cewa yaran nan haka mu riqa musu addu'a"
Da haka suka canza babin firarsu ko maganar Rufaidan busu sake bi takan taba

11AM
Ra'uf ya fito falo cikin shigarsa ta shaida Ash ruwan toka Hajiya ta dubesa da take zaune a falon itada Yakumbo da Mama da sauran yan biki da busu gama tafiya ba
"Kai mai kake nufi ne wai,badai tafiyar zakaiba,wa zaka tarar a gidan idan kaje ca nake ita kanta Hannatun sai zuwa gobe zasu koma"
"Mama tasa baki a maganar
"Keko Hajiya Hanne banda abinki saurayi kamar Ra'uf kya tanbayesa ina zashi,gida bakowa idan yaje,kika sani ko amarya muka samu a kano zashi gurinta"
Murmushi yayi yace
"Kamar ko kin sani Mama,na samo muku amarya tunda ku kun tsufa"
"Hajiya Hanne ta ha'de rai ta kallesu gami da furta
" wanne irin amarya bayan ga Karima nan ban fadama maganar ta ba tun kwanaki"
"Eh kin fadamin amma nasamu Karima da maganar tace tanada wanda takeso"
"Kodai kai ka fadamata kanada wadda kakeso ba"
"Haba Hajiya ku daina gardamar nan kibar kowa da zabinsa mana, mudaiyi musu addu'a Allah yasa Alkhairi a zabin nasu"wata saga ciki tayi maganar mai suna Habi
Shikenan Habi wallahi donke kikai maganar nan ne amma kinsan cewa Karimah bazata furta wa Ra'uf tanada wanda takeso ba,sai dai idan shi ya fadamata yanada wanda yakeso dan dama shiba dan mutunci bane uwarsa tagama lalatasa shi kuma ubansa an mallakesa,bare ya tabuka wani abun"
Ra'uf ganin bazai iya jure kalaman kakartasa ba yasashi barin falon dan indai ya cigaba da sauraron kalamanta to zai iya fadamata duk maganar da tazo bakinsa,Yakumbo da Mama suma baya suka rufowa jikan nasu da sunaji Hajiya Hanne nace musu munafukai jika dai natane ko mace tace natane to tafi iko dashi bare ma kuma harda su karere wato Mama Suwaiba murmushi sukayi da fitowarsu harabar gidan har Ra'uf ya karasa wajen da motarsu take ajiye dan da saurinsa ya fito falon Mama Suwaiba ce ta kirasa da sunan da ita dince kadai take kiransa da sunan wato Babban mutum,dan sunan babban danta garesa danko da wasu sun fadamasa to gurinta sukaji tana fadamasa suka kwakkwaya ,gurin da suke tsaye ya koma hakuri suka shiga basa akan halin Hajiya Hanne shima hakuri ya basu dan yasan sums suna matukar hakuri da ita fiye dashi namiji tunda shi koda yana kadunan ba zama yake ba a gidan idan sunzo shida Amminsa bare kuma yanzu da basa ma kasar dan Hajiya Hanne wata macace mai wuyar sha'ani halinta kwata kwata babu wani wanda za'a yaba gata da zafin kishi da son zuciya da sonkai da take gaskiya da haka sukayi sallama suka rabu cikin tunanukan rayuwa kala kala haka Mukhtar yaja motar suka bar gidan zuwa Bayajidda street gidan Ahmad suna zuwa daga kofar gidan yacewa Mukhtar ya tsaya anan,wayar Nasiba ya kira yace su fito ba jimawa suka fito harda Samiha da Ahmad inda Ahmad ke masa tsiyar yaki shigowa ciki,ko kulasa baiba shima jin hakan yasan ran mazane ya baci,da haka suka shiga motar Mukhtar ya fito yasa musu kayansu a boot ya hau yana kokarin tada motar Ra'uf yace sai sunyi waya shima a lokacin Ahmad kai ya 'daga Ra'uf ya murmusa dan ya fahimci Ahmad haushi yaji addu'a Samiha take musu da idonta ya cicciko da kwalla da Rufaida gudun kar a banbareta jikin Samiha suna kuka yasata riga kowa shiga motar tanajin sheshshekar Samiha itama ta fashe da kuka a motar a haka suka bar kofar gidan da Ra'uf ya juyo ya kalleta kallo daya ya maida kansa da kukannata baya sansa ko alamu saidai a gaban su Aunty Samira baya tunanin ya iya lallashinta saboda yanada yakinin suma zasu bata hakuri haka ko akayi su Aunty Samina ke kokarin bata hakuri da suma sunsan shaquwar Samiha da Rufaida ranar da daya zai rabu da daya Dole suyi kuka.

*LIMATU KHALILULLAH*❤️💞*JININMU 'DAYA*
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad:Sadiya Ibrahim Khalil

*PAGE 25*

DAN ALLAH KUYI HAKURI KUYI MANAGE BA YAWA MORE COMMENT'S MORE TYPING

3pm suka sauka a Kano kai tsaye gidan Aunty Samina suka ajesu da take a Sharada phase 1 da sai sun huta kowacce zata tafi gida Ra'uf yace wa Rufaida su jira zaizo ya kaisu gida badan taso ba ta amince Ba jimawa da shigarsu gidan Ra'uf ya turo Mukhtar gidan Aunty Samina da lemuka da yoghurt dasu Ice cream Nasiba ce ta fito ta amsa tayi godiya ta koma ciki.

Aunty Samina ta dubi himin kayan
"Kai wannan hidima haka baya gajiya shidai kiduba Alkhairin da yayiwa su Yaya balki kuma da siyayyar da yayiwa su Khalil (wato tana nufin 'ya'yansu Khalil,Kalim)"
"Wallahi kuwa Allah yasa dai yasa ya dore har aurensu ya kuma sa ya kasance mijin nata indan shine mafi alkhairi a gareta amma gaskiya naga alamun yanada kirki"
Cewar Aunty Samira
Aunty Samina ta amshe da "Amin dai"
Itako Nasiba harta bude tafara shan ice cream dan yunwa take ji gashi taga Aunty Saminan batada niyyar cewa su dora girki itako Rufaida Kitchen ta Shiga ta dora girki don gidan Aunty Samina Ba bakonta bane Iran suka zo da Samiha bata musu iyaka da komai dan sun maida Rufaida kamar Samiha su,kuma aranta bata tunanin zata iya cin kayan dan gaskiya yunwa takeji bazasu kosar da ita ba tadaifi gane ko zata cisu sai dai da marmari
Chapter 24 · 0% Book details