← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 57

Sashe 21

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke angwayen a falon hankalin kowa naga abincin da aka kawo musu Friend rice da sinasir sai kayen soyeye soye,Ahmad Ra'uf ya duba da yake kokarin kai ruwa bakinsa yace
"AHMAD kasan yarinyar dana nunama 'dazu ta tsakiyar SAMIHA naji har magana kayi mata" yayi maganar yana aje gorar ruwan da ya bude yasha a kasan carpet
"Eh nasanta Cousin's din mata tace Rufaida sunanta lafiya maiya faru"ya karasa maganar yana kallon RA'UF kallon rashin fahimtar a inda ya santa"
"Bakomai nasanta ne"
Murmushi yayi Ahmad kana yace
"Malam kodai itace kayi gamo da ita kwanaki kafadamin gaskiya kar naki baka ita tinda kasan kanwar matatace kuma kawarta"
"Wallahi baka isa Ba idanma kace haka toni da nake matsayin kaninsa zan tsaya masa ayi komai" cewar Bello dayake kai lomar doughnut bakinsa
"Yawwa fadamasa dai ni dan Allah kiramin yarinyarma please (yi hakuri)"
Abokan ango sukayi dariya da yawanci abokan sune duka suka ce
"Kai Ra'uf ai duk saurin unguwar zoma tabari a haihu"
Ahmad yace
"Kuma kwa fadamasa dai"
"Kaga idan zaka kiramin ita kakirata hakurin kwana nawa kakeso nakuma yi,vayan wanda nayi a baya" Ra'uf ya karasa fadar haka yana daukar wayar Ahmad ya danna yasa a kunne
"Tunda bazaka kira ni bari nakira"
Abokan nasu dariya suka sa ciki harda Bello da yaji suna neman kwafsa masa ya mike yabar musu falon ya nufi kofar fita daga falon jin an 'daga yasa shi tsayawa daga kofar falon
"Assalamu Alaikum,Amarya Samiy" Yayi saurin katse maganar da Samiha keyi
A daya bangaren aka fara magana
"Wa'alaikumus salam,Yaya Ra'uf" saboda ta fahimci ba Bello bane tasan idanko vashi bane to baya wuce dayan biyu ko Ra'uf
Murmushi Ra'uf yayi jin ta gane muryasa ya katse tunaninta da cewa
"Dan Allah daya daga cikin kawayenki mukeso tazo"
"To shikenan bari naturo ma wata"
Da haka ya katse wayar sai da ya katse ya fara tunanin maiyasa ma baice Rufaida yakeso tazo ba tsaki yaja yana addu'ar Allah yasa Rufaida ce zata zo,da wannan tunanin ya koma cikin falon abokan nasu suka cigaba da zolayarsa shi kuma murmushi kawai yake abinsa

*****
Rufaida Samiha ta kalla bayan ta gama wayar da take kusa da ita gefen gado dasu biyune kawai a dakin ta soma magana da cewa
"Rufy Dan Allah kije gurinsu Ahmad,yanzu Brother dinsa (dan uwansa)ya kirani sunason ganin daya daga cikin kawayena,kinga suku ma sauran sun tafi gidansu Zainab din Momy Balki"
"Eh hakane,amma banda haka Allah Ba inda zani" ta karashe maganar tana mikewa
"Maiyayi zafi kuma haka Rufaida ko Ahmad yayi miki laifine"
"Ko daya wallahi baimin laifi Ba illah dai abokansa kallo garesu musamman wani wanda ya dan darasu haske"
Murmushi Samiha tayi tare da fadin
"Nidai ki taimaka kije karsu sakemin waya"
"Naji" da haka tasakai tavar dakin Samiha ta bita da murmushi har ranta takeson kawarta sai dai gashi sunkusa rabuwa har watarana ta yiyu ko wacce tayi wuyar gani
********
A hankali take tafiya cikin nutsuwa harta kusa isa kofar falon Ra'uf da ya hangota Kasancewarsa yana waje yana amsa waya wayar yayi saurin katsewa ya karaso yasha gabanta da murmushi a fuskarsa da gavatarmata da sallama dago idonta tayi ta dubeshi kallo daya tayi masa ta shaidashi shine mai kallon ta dazu gefe takoma ta amsa masa sallamar ta sake gaishesa karo na biyu ya 'dan murmusa kana ya soma magana
"Gimbiya Rufy ya hidindimun biki"
"Alhamdulillah"
"Kinko shaida fuskata koda yake ta yiyu in ban sace zuciyarki ba, bare harki matsawa zuciyarki gurin neman wannan barawan"
Murmushi tayi ka'dan
"Gaskiya ban shaidaka ba ,nashiga goma satar me nayi maka dan Allah ka fahimtar dani"
Shima murmushi yayi
"Kar dai na tsorata Gimbiyar matan ,kin tuna kwanakin baya a store ban riqe dai sunan store din ba, munyi karo dake a lokacin to tundaga nan kikayimin satar zuciyata"
Sai a lokacin ta tunosa ta fahimci kallon sani yake mata a dazu sai dai ita a dazu bata ganesa ba"
"Naganeka "
"Yawwa Rufee,karna cika ki da surutu bari na gabatar miki da kaina ni sunana AbdulRa'uf Jabir Danbatta cousins din Ahmad ne ma'ana dai (Abbansa kanin Abbana ne) haka momynsa kanwar momyna ne ina Delhi da zama da mahaifana kuma ina aiki acan,a takaice kenan ,naganki a tun wannan lokacin naji ina qaunar ki kasance mata a gareni insha Allah ina fatan ki amince dani kuma da yiwa kaina fatan Allah yasa bairigani ba,dukda bazanso haka ba amma dai zan baiwa zuciyata hakuri idan har haka ya kasance"
Murmushi ya subuce mata jin karashen maganar tasa tayi shiru ba tare da tace komaiba
"Kinyi shiru ko dai zuciyarki bata amince dani"
Sauya maganar tayi
"Bari na karasa cikin falon,inda ake kira na"
Zaro ido yayi
"Wato ba zaki amsamin maganarba kika canzamin da wata,to gurin wa zaki cikin bayan ga basaraken dake kiran gimbiyarsa to tunda ta gansa babu abinda yayi saura ko"
Jinjina karfin halin Ra'uf itadai Rufaida takeyi wato daga haduwar sau daya zata amince masa
"Kinyi shiru gimbiya"
"Kaya hakuri..." Bai barta ta karasa maganar ba ya zaro idanunsa duka
"Hakurin me harkinsa zuciya tayi raunin"
Ita dai murmushi tayi
"A'a cewa zanyi zan koma ciki tunda kafadamin sakon"
"To naji vani number dinki yanzu"
"Banida waya"
Bata jira cewarsa ba tabar gurin dan ta lura baida niyyar kyaleta ta tafi
Ganin tabar gurin yasa shi murmushi ya kyaleta dan yana ganin alamun nasara ko a yanzu,yana sane da balallai tayi masa doguwar magana ba kasancewar ba gida yazo ya je ya sametaba da haka ya bar gurin ya koma falon

*****
"Angon gobe gaskiya gayu bikin Ahmad mu sashi a tarihi" abokansa da suke hangosa shida Rufaida ta kofar falon da take a bude sukayi hanzari fada yana shigowa falon
Murmushi yayi
"Kai Guys haka zaku ce"
"Eh mana haka ne,ko ba haka bane gayu" inji daya daga cikinsu ya fa'di hakan
"Khalifa ka kiyayeni"
"To tuba nake ranka ya dade"
Ahmad da ya shiga firar a yanzu ya soma cewa
"Dan uwa Allah kayi sa'ar mace"
Khalifa yasa baki karo na biyu
"Gaskiya ne Ahmad babyn kyakkyawa tayi ba karya"
"To naji dai,yanzu dai ka kira mana amarya muyi hutunan ayi shirin tafiya da amarya na matsu na koma KD"
"Kadai fadi gaskiya malam Ra' uf kodai so kake muyi mu koma gobe a dawo bikinka ne"inji Bello
Tsaki yayi ya sake ficewa daga falon dan yasan zasu takurasa ne da magana indai ya cigaba da zama sukayi dariya ganin ya bar musu dakin.

*SADIYA KHALIL😊😊**JININMU DAYA*
By Sadiya Ibrahim khalil (Sadiya Khalil)

*Wannan shafin naku ne group mai albarka Sadiya khalil group Allah ya sadamu da alkhairi ya bamu ikon rubuta abinda zai anfanemu duniya da lahira Amin kuyi yadda kukeso da wannan shafin donku akayi*😊

Page 22

arfe 1 na ranar daurin auren aka taho da amarya Samiha da take kuka sosai na rabuwa ita da gida saidai da ziyara haka dai suka taho da yayyenta biyu aunty samira da aunty samina da kannen da yayyyen babanta dana mamarsu biyu da kawayenta cikin harda su Nasiba da Rufaida da bayan gama shagalin bikin da za'ayi a Kaduna yau bayan kai amarya zasu koma kano dasu Aunty Samina duk tare Ra'uf kuwa yayi sa'a motarsa su Rufaida suka hau da Mukhtar yake tuka motar Ra'uf da ya katse shirun motar da fadin
" Da alama Mukhtar kurame muka dauko a motar mu"
"Nima nafi tunanin hakan kuwa" Mukhtar ya karasa zancen yana maida hankalunsa ga tuki
"Saboda me" Nasiba da Zainab suka fa'da itako Rufaida shiru tayi da kwata kwata bata sakewa a motar "
"Yawwa to kudai naji magana ku kun fita daga jerin kurame,saura 'yar uwarku"Ra'uf ya karasa zancen yana sake kallon Rufaida ta gilashi
Nasiba da ta gano nufinsa ta soma fadin
" oh Rufee zakace mana,tana magana sai dai kasan ita sarauniya ce bata magana da kuyanginta matukar bata kama ba amma tunda Sarkin yayi magana to itama ba shakka zatayi"
"Hmm haka dai kikace banga alamun zata yi ba,mu muke kidanmu na lura muke rawarmu ni na aje sarautar a yau amma ita na lura ba haka bane anata fannin"
Wayar Nasiba da tayi kara yasata kin basa amsa ta duba wayarta ganin mai kiran AbdulRafi ne yasata saurin 'dagawa AbdulRafi yanajin Nasiba ta 'daga ya fara da
"Nasiba ina kuke ne kunsan fa yau zamu koma keda Rufaida muke jira"
"Yaya AbdulRafi muntaho kawo amarya Samiha,muna tare da Rufaida ma"
"Amma buku kyautamin ba kunsan zan jiraku"
"Wallahi Momy ce tace mutaho kai amaryar daganan saimu taho dasu Aunty Samina"
Tsaki AbdulRafi yayi ya katse Wayar dan bakaramin lokaci suka bata musu ba da tuni sun manta sun bar sokoto dan sunyi dasu tare zasu koma baisan hardasu aka tafi kai amaryarba dole yasa shida Samir suka yi haramar komawa kano
Nasiba ce ta dubi Rufaida ta soma fadin
"Kin jini da Yayanku ko"
"Eh au ke ba yayanki bane"
"Sorry sister (yar uwa)yayanane mana"
Daganan Rufaida tayi shiru har suka karaso Kaduna bata sake cewa komai ba sai dai Nasiba da Zainab da suke magana tare da Ra'uf ke sa baki a wata firar yana kuma cigaba da aikin kallon Rufaida ta madubi a haka suka karaso Kaduna Isah Kaita Road aka wuce dasu da a unguwar gidan Samiha yake gidan yayi kyau sosai an zuba kudi komai yayi sosai suna isa gidan Samihan suka firfito daga motocin zuwa cikin gidan da mortar amarya aka wuce da ita gidan sirikanta inda daganan sai akawota gidanta Ra'uf ne ya tsaida Nasiba dan ya fahimci tafi sanin Rufaida akan Zainab ita yakeso ta shigar dashi gurinta saida suka gama shiga dakunan gidan da kitchen gidan da yakasance plat saidai yayi kyau dukda babu dorin benen iyayen Samiha ma sunyi kokari sun kashe mata dukiya sosai part biyu ne a gidan nata dana Ahmad din nan suka dawo falo suka zauna suna yaba kyan gidan Ahmad yayi kokari sosai
Chapter 21 · 0% Book details