Sashe 10
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ganin Ruqayya na waigegen bayan shigowarta falon dako sallama babu dan duk adabirce take yasa Hajiya Jamila tanbayarta"ke lafiya "Ruqayya da saida ta zauna a kujera tace" Umma ai Yaya AbdulMalik ne ya kamani ina musu la'be"Hajiya Jamila tace"to saime ince dai ba dukanki yaiba ko?"Ruqayya tace"a'a bai dokina ba,Gaskiya UMMA Yaya AbdulMalik baida mutunci matarsa zatasha wuyar zama dashi kafin tasan halinsa kai kodama tasani idan ta sake ta kuskure masa zatasha bala'i da masifa kings ko yadda yayi min yanzu" labari ta bawa Hajiya Jamila"Hajiya Jamila tayi murmushi tace"to kuma dake zamu aura masa"Rukayya ta zaro ido tace wa waini Umma ko wata dai?indai dan ta nice na yafe akai kasuwa dama dai waccen da yake nuna alamun yanaso Rufaida kika barsa ya aua kodan tasha wuyar sama dan in inbama itan da yakeso ba dawa yake zama yayi magana ta da'din rai mai tsawo sai dai ko Abba dan koke indai yaji kinsa abinda bai masa ba a hirar tuni yake tashi"Hajiya Jamila da ranta ya soma 'baci da maganar Rukayya tace mata "keni rufemin baki tunda kince bazaki aure sa ba saiki bar maganar ,sai shigo da yarinyar da kuke da banbanci maiyawa tsakaninku" Rukayya ta 'dan yatsina fuska tace haka nefa"amma 'kasan ranta addu'a take Allah yasa AbdulMalik ya aureta kodan tasha wuyarsa dan ita gani take ma tafi Hajiya Jamila tsanar Rufaida da kishi da ita tunda ta auri masoyin da taso take karaso har yau wato AbdulAhad shiyasa duk wannan tsanar da take nunawa Rufaida bata shafi Yasir ba dan har wayarta basa take yayi game da take ganin Yasir din kamar AbdulAhad dan ita kanta Rukayya batayi tunanin tanasan AbdulAhad har hakaba sai bayan rasuwarsa ta fahimci haka dukda dai kiyayyar da yake nunamata a fili amma tunaninta data samu ta auresa zai daina anata ganin kenan Hajiya Jamila ta katse shirun da cewa "ni waima na tanbayeki Rukayya wa Rufaida tace ya hanata saka caji nifa shiyasa kin ganni nan banasan zaman ire-iren Aliyu da Hauwa'u a gidan nan indai neman gurin zama ne sun iyashi an musu lecture dinshi" Ruqayya da maganar Rufaida ta fara isarta dan ita duk abinda bataso batasan aita surutunsa kai ko ma dason abin take batasan a dinga damunta da maganar baki ta ta'be tace"Umma bara na 'dauko wayata"daganan tasamu damar tserewa tabar Hajiya Jamila a falon da tunda gari ya waye ko tsinke bata daukaba bare ta wanke ba dukda ranar girkintane ga bayinan tasamu Rufaida da Inna Lami,da sanda ba Rufaida bata gidan wannan bautar ta Inna Lamice sai taga dama sukeyi tare idan taga an kuskure mata ta fara fada kaikace cinye mutum zatayi 'danye
Rufaida jin shigowar Inna Lami ta kofar kitchen wadda take ta baya bata falon yasa Rufaida yi mata sannu da zuwa, Inna Lamin ta amsa da dan murmushi fuskarta tace "yawwa Rufaida kinsha wiki Rufaida yakamata kije ki huta ai tunda na dawo" Rufaida tace "haba Inna keda kikasha tafiya ai gwara kibarmin aikin tunda saura karashe shima don baki fadaminba zan tanbayo Umman Yaya AbdulMalik ya shigo kitchen din" Inna Lami tace Allah sarki amma dai kibari na karasa tunda kinga ni aiki name"murmushi jin maganar Inna Lami tayi tana tausayin Inna lami ta fara tsufa amma tana wannan wahalar ta yiyu rashi garesu shine ya janyo hakan kuma sai gashi ta ha'du da muguwar uwargijiya Hajiya Jamila tunda dai kusan aikin gidan da take kusan natane kuma Hajiya Jamilar ce ta samo ta,Rufaida da bayarda ta iya ganin yadda Inna Lamin take ta roqonta da take ji ba dadi ace babba na rokarta da haka yasa Rufaida bar rmata ragowar aikin kayan da AbdulMalik a siyomata ta dauka ta yi hanyar dakinta.
SADIYA IBRAHIM KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA*
HalimatusSadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khalii)
Page9
Dady da ransa yakai makura gurin 'baci ya soma magana cikin bacin rai yace"Ra'uf abinda kakefa ya fara isata kace bazakayi aure yanzu ba na hakura na qyaleka yanzu kiri kiri ka nuna bazakaje gurin danginka ba Nigeria so kake kayafe zuwanta gaba daya shekarunka nawa da daina zuwa haba Ra'uf yanzu kai sai wani yayi ma fadan abinda yakamata kayi yanzu"
Ra'uf yana mamakin fadan Dady akan abinda baikai yakawoba dan kawai yace bazaije Nigeria ba,toma shiko mai zaiyo a Nigeria a yanzu haka yake jin kansa kasar da aka saka masa ciwan da yake damunsa har yau da yasan duk sanda zaije wannan mikin sashen rayuwartasa zasu kara tuno masa abinda yake da tabbacin ku'di martaba duk ahalinsa suna da shi mai kuma yayi saura da har zasu rasa Samar masa farin cikinsa dan shi a yanzu ma koda zaije Nigeria ba wai don waccen rayukan zaijeba sai dai dan rayukan da duk sanda ya kwanta yake tuno su
"Ra'uf ya takaita tunanukansa yace "a'a Dady kaima kasan yanayin aiki ne yake hanani zuwa Nigeria" Dady da ya'dan sassauta murya yace "ai kai ne agogon sarkin aiki dama,Ra'uf ko ka'ki koka so bakada kamar mahaifarka ko ta iyayenka amma Yaro ace kiri kiri kaki kasarka duka duka zuwannaka Indian duka yaushe"
Ra'uf ya dan kara gyara muryarsa ya nutsu gurin fa'dar cewa"a'a Dady kaima kasan banda yanayin aiki babu abinda zaisa nace bazanjeba"tsaki Dady yaja yace"nikaga kakiyayeni da wannan dadin bakin naka kamar mace,tunda bazaka ba shikenan zanje da Safiyya kawai"shiru Ra'uf yayi yana tunanin halin da Safiyya zata shiga idan aka tafi da ita dan bawai sabawa tayi dasu ba sabodahantarar Safiyyan da suke yi shiyasa babu sabo tsakaninsu wannan shine abinda yasa ma bayasan zuwan Safiyya kwata kwata cikin zuriyar tasu",ya ce "amma Dady a kano za'a bar Safiyyan ko?" Dady da ya gane wancen tunanin nasa sai kawai ya share yace"kamar ya na barta a kano,ita bazataje cikin dangintaba a yanzu haka tanada kamarsu ne fadamin?"Ra'uf yace"a'a Dady"Ra',uf ya sauya maganar da cewa yanzu ranar yaushe zaku tafi?"Dady yace"sai zuwa wani satin nake tunani"Ra'uf yace"to Allah ya kaimu lafiya zan bada sako akaiwa Momy Hannatu"murmushi Dady yayi"yace toni tawa Momyn fa"murmushi shima Ra'uf yayi yace"ni fa tawa Momyn kawai zanyiwa kowa yayi wa momynsa"dariya Dady yayi yace"shikenan tunda abin 'yar hakane"Dady yace "yawwa Ra'uf kunyi waya da Malika kuwa ta fadamin akwai sa'kon da zaka bani na tahomata dashi" Ra'uf yace"Eh Dady ita Safiyya zanbawa sakon ta bata" yace to shikenan dadai haka suka cigaba da firar duk dai akan tafiyar har zuwa wani lokaci"
Dan Allah kuya hakuri kuyi maleji✍🏽
SADIYA KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA*
By Sadiy Khali
10
WAIWAYE