← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 57

Sashe 41

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin bugun kofar falon nata yasa ta mikewa daga kwanciyar da ta tayi a kujera da barci ya fara daukarta jin an cigaba da bugawa yasa ta mikewa ganin waye cikin tsakar ranar nan yazo gidanta sai da ta leka kofar ganin mijinta tsaye jikin kofar ya sata kokarin bude kofar da murmushi akan fuskarta,ido biyu tayi dasu Hajiya Jamila da suke bayansa da hanzari tayi kokarin basu guri tana cewa
" Sannunku da zuwa Umma"
Wani banzan kallo suka jefeta da shi,suka karasa shigowa falon wanda da ido suke bin ko ina na kusurwar falon da suke kokarin ganin makusar falon nata
Da wani murmushin ta sake cewa
"Sannunku da zuwa Umma ku zauna mana kunsha hanya bari na kawo muku ruwa" daga nan ta shige ciki
Basu ce da ita komai ba ganin ta wuce yasa suka bita da wani banzan kallo daganan suka zauna a kujerun falon suna ya mutsa baki dukda kayatuwar falon kuwa
AbdulWahid katon akwatunsu ya shigo musu da shi da shima ya najin sannu da zuwan da ta musu basu amsa ba,har karo biyu sharewa yayi ya shige da akwatun nasu ciki dan yana ganin akwatun ya fahimci bada tafiya suka zoba da zama suka zo kofar wani corridor na gefen wani daki ya aje kayan ya shige cikin kitchen din da yake tsammanin Rufaidan na ciki jikin kofar kitchen din yayi tsaye yaki karasa shiga ciki da murmushi kan fuskarsa yake kallonta tana kokarin jera lemuka da ruwa akan faranti mai girma ta juyo zata fito idanunta ya sauka cikin nasa murmushi tayi masa inda take ya karaso ya mika mata hannu ganin haka yasa ta gane manufarsa mika masa plat din tayi ya amsa ya rike dubensa tayi kana ta soma magana
"Haba Yaya yanzu su Umma zasu zo koka sanarmin gashi sunsha hanya,kuma nasan suna jin yunwa yanzu fa sai sun jira na dora"
Murmushi yayi jin kalamanta gaba daya baza kace bata murna da zuwansu ba dukda kuwa yasan hakan ne don koshi da Umma take mahaifiyarsa Rukayya kuma take matsayin kanwarsa baya murna da zuwansu bare kuma ita dan yasan babu alkhairi a zuwan nasu tunanin da yake ya aje gefe kafin yace
"Kanwata sai yanzu suka sanarmin da zuwan nasu tuba nake" ya karasa maganar da murmushi
"Hm" kawai tace tana kara mika hannu ta amsa tray din
"A'a ki kyale zan kai musu ki dauke musu kayan nasu ki kai musu inda kikaga ya kamata su sauka suna corridor" daga nan suka fito daga kitchen din tare

Da sallama ya dawo falon da sallamar ta katse musu firar da suke ganinsa dauke da tray da yake kokarin aje musu akan centre table yasa Hajiya Jamila saurin kallonsa tare da kokarin cewa
"Wahid me zan gani haka,kaine dan aikin gidan kardai daga auren harka zama mijin tace"
Kai ya sosa da kokarin cewa
"A'a Umma wanne irin mijin tace taimaka mata nayi fa"
"Taimako a haka ake taimakon,dalilin gujema auren nan da nayi kenan,haka kurum kaje ka kwaso irin karuwai,ba dole su mallake ka ba,gashi harsun rabani da kai,ko waya yaushe rabon da ka kira ni" cewar Hajiya Jamila
Rukayya tayi saurin cewa
"Wallahi kuwa Umma"
Hararar Rukayya yayi yace
"Ke kuma dake ake magana ya kalli mahaifiyartasa yace mata,
"amma ni Umma wannan va mallakewa bace,kowa yasan akwai taimako tsakanin mata da miji sannan,vatun kalmar karuwanci da kike jifansu dashi ,ina jin tsoron mahaifiyata ranar lahira ta tsaya gaban ubangiji ace tazo da wannan shaidar,biki gani ba ba ayi a gabanki ba,to me zaki cewa ubangiji a wannan,sannan ni Umma wallahi ba ruwan Rufaida da kin wayata dake dangataka da ita daban da taki ma haka,ba ruwanta da mahaifiyata,idan ba itama biyayya zata yi miki ba"
Hajiya Jamila cikin fusata ta dubesa tare da cewa
"To ubana jeramin magana,don ance matarka tana kokarin mallekeka zaka rika jeramin magana" ganin yadda mahaifiyata sa ta fusa ta daga 'yar maganar sa yasa shi sassauta murya gurin cewa
"Umma kiyi hakuri" sai a sannan ya gaishe da Umman tasa,kamar ba zata amsa ba tadai daure ta amsa,Rukayya da dakyar ta iya gaishesa don bakara min haushin abinda yayi mata lokacin ta ji ba amsa mata yayi ya mike yabar falon yana kokarin shiga ciki kiran Rufaida jin har lokacin bata fito ba wanda ta tsaya sake gyara dakin da su Umman zasu sauka ne a hanya yaci karo da Rufaidan zata fito falon bayan gamawarta murmushi ya sakar mata don baya so ta fahimci wani abun ita ma murmushin itama tayi don bata so ya fahimci taji duk maganar da sukeyi a kokarin ta na dawowa falon da tayi jin suna magana ya sata kasa karasawa kuma takasa barin gurin kuma maganarma duk dai akanta maganarsa ta katse tunaninta
"Dama nazo na sanar miki zan koma vakin aiki,ki fito kuyi fira karki varsu su kadai,sai ma naganki zaki fito din"
Ba tare da tace komai ba suka rankayo falon tare
Rufaida da suna isowa ta durqusa har kasa tana gaishesu da sake musu sannu da zuwa harda Rukayya ta gaisar da Rufaida bata tunanin Ruqayyan zata iya gaida ita kamar ba zasu amsa ba Hajiya Jamila ta daure tace mata
"Lafiya"
Daganan ta mike ta nufi Centre table din ta tsiyaya kowacce ruwa da lemo tace musu
"Ga ruwa kafin a dora abinci" babu wadda tace mata koda to a cikinsu ita ma batayi tunanin hakan ba daganan ta mike ta basu guri,AbdulWahid dake tsaye jikin TV yana kokarin canza tasha yana jin duk abinda yake faruwa bai sake saurararsu ba yayi hanyar barin falon
Yana kallonsu dukansu har Rufaida da ta yiwa kanta matsugunni a wata daga cikin kujerun falon yace musu
"Zan koma bakin aiki saina dawo"
"Adawo lafiya"
Hajiya Jamila ta iya furtawa,Ruqayya ko kallonsa bata yi ba bare tayi masa addu'a
Rufaida ta biyo bayansa yi masa rakiya da su Hajiya Jamila suka biyota da wata muguwar harara,musamman Ruqayya dan gani take da tuni ita ce a cikin daularnan fa wannan yarinyar tayi mata shigar sauri a zuciyar AbdulWahid dalilin da yasa take jin wani matsanancin kishi akan Rufaida, har jikin motarsa ta rakasa
Wahid da yake kokarin shiga motarsa ya juyo yana Kallonta cikin nuna tausayawa zamansu da mahaifiyar tasa tun kafin aje ko ina yace
"My wife kiyi hakuri nasan kemai hakuri ce anma ki cigava dayi karki gaji nasan kinsan halin UMMA bana tunanin zaki sha wuyar zama da ita,dama kafin sanin halin mutum shine wahalar kafin nan dai da Abba ya sauko ta koma dakinta"
Murmushi tayi masa ta kallesa
"Haba Yaya ai mamarka kamar Ammi ce koda ba muda alaka ni dakai"
Ya tari zancenta da cewa
"Eh dukda hakan,kinsan zama da uwar wani sai hakuri musamman Umma"
"Haba Yaya karka ce haka uwa uwa ce mu cigava da yi mata addu'a Allah ya ganar da ita Rufaida take fadin haka
" Hakane my wife,bari na koma aikin,sai na dawo"yayi maganar yana yi mata kallo mai cike da soyayya
Kai ta sunkuyar kasa ganin kallon da yake mata
Murmushi yayi yace
"Badai kunya na baki ba dan na kalli mata ta kallon soyayya,wallahi Rufaida ina sanki kinada halayya mai kyau,da yake karamin sanki koda yaushe,gaki kyakkyawa" yayi maganar yana dariya ya shige mota yana kokarin tayarwa yace
"Ya ba kice komai ba"
Ta kallesa race
" to Yaya mai zance?"
Yace mata
"kice wani abu nake so"
Tace
"To ka kulamin da kanka banda kula 'yammata"
Ya dan harareta yace
"Idan na kifa"
"Hmm"kawai tace
Yace
" kinga uwar kishi ni bani da lokacin kula mace,amma ga babbar wadda zaki kishi da ita nan tazo har gidanki Ruqayya,kibi a hankali dama inason fada miki"
"To Yaya insha Allah,ka koma naga lokaci na kurewa"tace masa
" to My Special na tafi
Yana kokarin tada motarsa tayi kokarin yi masa addu'a
"Adawo lafiya Allah ya tsare minkai"
Amin ya fadi hakan da murmushi yayi kokarin barin harabar part din nasu.
Saida taga wucewarsa tabar wajen ta koma ciki tana murmushi tana san mijinta saboda halayyarsa abar so ce ya iya nuna kulawarsa ga mace,dukda tasan tanasan Ra'uf amma yanzu ta manta dashi,dama addu'arta a kullum Zabin Allah sai gashi yayi mata zabi da Wahid ta kuma rungumi mijinta don dama uwarsa ta jiwa tsoro ba auransa ba amma tunda tanasan zama dashi dole tayi hakuri da mahaifiyarsa domin ance maso uwa taso danta haka ma maso da sai take ga taso uwarsa zaifi,dan da uwar bata haifesa ba ita da bata auresa ba
Da sallama ta shiga falon da babu wacce ta amsa mata bata damu da hakan ba ta dubi centre table din yadda ta tsiyaya musu lemukan haka ta tarar dasu
Murmushi tayi tace
"Umma naga buku sha komai ba anan"
"Haka karuwar uwarki ta koya miki bawa baki abinci kenan,amma ta ko yamiki mallake miji ko,to ni bazan jure haka ba saboda akwai banbanci tsakaninmu mu daku,gadon tsiya kawai"
Hajiya Jamila tayi maganganun tana sake gyara zamanta
Ruqayya shewa ta buga ta ya mutsa fuska tace
"Kinga zo ki mikomin ruwan nina sha"
Bata ko tankawa Ruqayyan ba ta shige ciki ta barsu,dan Ruqayya bata kai matsayin da zata sata aiki ba ta yi mata saitayi niyyar dukda durqusawa wada ba gajiya bane saboda a girme ta girmi Ruqayyan amma ita Rukayya da izgilanci tayi mata maganar kuma ita bataga laifin taba takawo musu ruwa ta tsiyaya musu,daukarce zata gagaresu,to ko ita 'yar aikice aikinta iya nan zai kare
Chapter 41 · 0% Book details