← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 57

Sashe 20

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan Ra'uf ya shige cikin daga cikin dakinsa da yake cikin falon ,bai karasa jin maganarsu ba,da baya ma kaunar jinta wato har a gabansa ma maganar mahaifansa za'ayi saboda a nuna isa da fifiko akansa shida mahaifan nasa ,dafe kansa yayi da ya ke matu'kar sara masa, Bai ko tsaya watsa ruwa ba ya fada gado yana danna wayarsa, Sai da yaga kiran momy ya katse yabi kiran suka shiga fira yana bata labarin abubuwan da suka faru bayan zuwan sa Nasiha ta dinga yi masa data sanyaya zuciyar Ra'uf sosai

Jin bu'de 'kofar tare da yin sallama yasashi saurin tashi zaune ganin mai sallamar da yake jinta tamkar Ammi da Momy a zuciyarsa,Ga ma kuma kamannin da takeyi dasu,Ba wata bace illah Yakumbo,Sakkowa yayi daga gadon fuska dauke da Fara,a yana kar'bar 'katon farantin hannunta yana cewa"Kai Yakumbo irin wannan kayan sai su ya dake ki jawomana cinya"

Dariya Yakumbo tayi tace "Su dai bello sayi badai kaiba"

Ra'uf yayi murmushi yace "To ni 'din gunma indiya zamu tafi har ki warke"

"Allah ya 'kara kiyayewa" inji YAKUMBO, Ra'uf ya amsa da "Amin dai yakumbo"

Abincin ta shiga zuba masa Inda take sanar masa ita tayi girkin Dan shi ka'dai kawai

Ra'uf ne ya dubeta bayan yagama cin abincin yace "Gaskiya yakumbo kin iya girki idan nayi aure ke zaki koyama matata irin girkinki"

"Kamar gaske auren zaiyi?, Ga dai Ahmad nan zaiyi ya barka saura kuma bello shima, kai ka tsaya ruwan ido, shekarunka yakai talatin yanzu amma ka'ki yin aure,

Murmushi yayi ganin Yakumbo so take dai dan dole sai ta cikamasa shekaru takaisa inda baije ba yace " Eh yakumbo da gaske nake nasamu matar da nakeso nima yanzu, na yarda dai Ahmad yarigani aure amma bazan yarda bello yarigani ba insha Allah, ya 'dora dacewa ba ruwan ido na tsaya ba sai dai yanzu ne nasamu wadda tayi daidai da tsarina".

Inda ya shiga bawa Yakumbou labarinta, da a koda yaushe yake jin sonta aransa ya kuma kasa daina jinsa.

Ita kanta Yakumbo taji lokaci guda ga labarin Rufaidan da ABDUL-RA'UF ya bata ta shiga ranta

Karfe Biyar su Ammi suka iso Nigeria Dan-ladi driver yaje daukosu dakai tsaye gidan Malika ya fara kaisu suka aje Safiyya da itama kanta batasan shiga cikin wannan ahalin gudun kar a batawa Safiyya rai yasa Ammi ta yanke shawarar ta zauna gidan Malika duk da anan ma bata tsira ba Safiyyan amma bakamar a gidan Hajiya ba
Sunyi murnar zuwan Ammi gaba daya ahalin kasancewarta cikakkiyar yar ahalin musamnan RA'UF kamar ya shekara baiga mahaifiyarsa ba yake jin murna da kowa sai da ya fahimci haka

Zaune suke a babban falo wajen large tara na dare da yawanci bakin wasu duk sun kwanta hakan yasa"BAFFA ALHAJI ya zauna a falon cikin 'ya'yensa da matansa da jikokinsa da MA'U ke zaune cikinsu tana bawa kowa tsarabarsa da RA'UF ke taya ta godiya suke sosai "RA'UF da tun 'dazu yake son tanbayar AMMI ina Safiyya ya dan dubi AMMI yace "AMMI ina SAFIYYA ban ganta ba kuma nasan da ita za'a taho "tana gidan Malika " Jin ko haka da Hajiya tayi "yasata bata rai ta fada" wallahi MA'U indai baku fitar da wannan yarinyar daga cikin zuriyarmu ba zan sallama miki JABIRU tunda bashi ka'dai na haifa ba,Kin zamar masa fitina a rayuwarsa kin mallakesa,har wayau bazan daina danasanin ha'da zuriya da HANSATU ba"BAFFA ALHAJI jin maganganun da HAJIYA keyi marasa da'di gaban jikokinta wadanda ma busu San halitta ba da ba'a KADUNA suke zaune ba yace"Haba HANNE irin haka baikamata ba yarinyar nan SAFIYYA itama ta muce kuma 'da na kowa ne bakasan wazai tallafeka ba,kuma komai lalacewa"MA'U ma taki ce ke kina fadar haka a kanta mai zahana ki hana wasu fara"ganin fadan da BAFFA ALHAJI ke mata gaban mutanan falon yasata tashi ta fice fu kamar iska"mutanan falon da duk jikinsu yayi sanyi nan yanayin halayyar Hajiya HANNE da har yau suka kasa sabawa BAFFA ALHAJI,ya shiga kwantar musu da hankalin da nusar dasu ita haka Hajiyar take tuni batun yau ba sai dai su cigaba da hakuri da halayyarta.

HAJIYA HANNE ce ta maida dubanta ga Ammi tana cewa "yanzu Ma'u sai an je har Sokkwato saboda d'aurin auren nan?"

Ammi ta ce "to ya za'a yi Hajiya? Yanzu haka ma Ra'uf ya fa'damin sun yi nisa, kuma Ahmad ya fad'a min ba 'yan asalin Kano bane, sai dai mu taya su da addu'ar dawowarsu lafiya, amma sun fa'damin da amaryar za'a taho".

"Oho musu dai, ace mutum ba zai yi auren zumunci ba sai yaran da ba wanda yasan asalinsu"

Ammi ce ta mi'ke wannan hirar tasu da dama gaisheta taje yi ta tareta da wannan zancen tace"Hajiya bari na shiga gurin Maman Karima naji ance acen ake aikin abincin bikin"tace"Eh hakane,ki kiramin NAFI daganan"ta amsa mata "to"da haka ta fice daga dakin tayi hanyar bangaren MAMAN KARIMA 'din*JININMU 'DAYA*
Na Sadiya Ibrahim Khalil
(Sadiya Khalil)

*WANNAN SHAFIN NAKU NE MASOYAN LITTAFIN JININMU 'DAYA SAKON GAISUWARKU YANA ZUWARMIN DA ADDU'AR FATAN ALKHAIRIN DA KUKE MIN ALLAH YA BAR KAUNA😊😊*
Page 20
Abba Aliyu da Sallama a bakinsa ya qarasa shiga cikin falonsa kallonsa Ummi Hauwa'u tayi kafin tace "sannu da zuwa Abban ABDUL-RAFI" ya amsa da "yawwa Hauwa"mikewa tayi daga zaman da tayi daga baiwa RA'IS abincin da take ta tashi ta nufi kitchen RA'IS gurin mahaifinsa kai tsaye ya nufa ya daukesa yana masa wasa mintina kalilan UMMI HAUWA'U ta daw falon da sallama da ruwa dauke a hannunta da Kofi saida ya sha ruwan kafin ta kallesa cikin nutsuwa tace
" Ya naga ka dawo gida tun yanzu ina meeting(taro)da za kuyi"
"Hmm kedai bari,ai sam director bai kyauta ba tun fitar da nayi muna can jiransa,bai zoba sai yanzu yayi mana waya ya fadama bazai samu halartar taronba?"
"Kai amma bai kyauta ba amma kila yana da uziri amma da ya fadamuku tun wuri kaga ai da muntafi bikin nan"
"Kedai bari HAUWA'U ni kaina abinda ya qara batamin rai kenan naso zuwa daurin auren SAMIHA ko dan yadda iyayenta da ita kanta suka dauke mu"
"Wallahi kuwa to ya za'ayi haka Allah yaso,amma gasu ABDUL-RAFI sun wakilcemu ai"
"Hakane kunyi ko waya da yaron ma kuwa?"
"Eh munyi waya dazu da ABDUL-RAFI yace,a lokacin shirye-shiryen 'daurin auren ake"
"Allah sarki ,dama 'daurin auren Safiya ne"
"Eh ai naji suna KADUNA za'a kai SAMIHAN kuma da 'yan daurin auren zasu tafi,na dauka kaga Invitation 'din ai,na gansa akan lokar 'dakinka jiya"
"A'a bangan shiba ina Sauri zan fita SAMIR ya kawomin , ina ga yaron ne yake aiki acan KADUNAN,amma ai shi iyayen yaron ai anan suke da zama,baban yaron ICP ne na yanzu"
Murmushi tayi kawai tace"Eh nagani a Invitation Allah ya sanya Alkhairi,ya basu zaman lafiya"
"Amin,ina sauran yaran ne"
"Suna ciki amma RUMAISA ta fita na aiketa gidan HAJIYA RABI"
"OK" daga haka suka cigaba da firarsu
********
'Karfe 11 na safe
Aka daura auren SAUDAT HASHIM SARKI da MUJAHID AHMAD TIJJANI
sai SAMIHA HASHIM SARKI da AHMAD USMAN MAHMUD 'DANBATTA

Shigowar amaren cikin falon da suke tare da 'yan uwansu da suke 'yam mata da kawayensu 'dai'daiku da suka taho tare daga kano da a kawayen SAMIHA RUFAIDA ce da NASIBA kawai sukazo bikin,cikin ankonsu suke na atamfa da yayi musu kyau gurin da su MOMY MARYAM suke zaune cikin falon itada 'yan uwa da abokan arziki yasa su karasawa suka gaggashesu amsawa sukayi da murmushi kan fuskar kowaccensu suna yi musu addu'ar fatan Alkhairi da haka suka mike don barin gurin MOMY MARYAM ta tsaida RUFAIDA da cewa"YAYA BILKI kinga 'diyar HAUWA'UN RUFAIDA da nake ce miki kawar SAMIHA"
"Masha Allah gatanan 'yar kyakkyawa har kama suke da SAMIHA,banga mamarta taba"
mikewa RUFAIDA tayi da wannan zancen ba tare da taji mai MOMY MARYAM da sauran matan dakin zasu fada ba
***
Amaren ne suke karasowa jikin motar da angwayen su AHMAD da abokansa ciki yarda RA'UF da suka fito don gaisawa da yi musu iso cikin gidan su SAMIHA suci abinci ayi photuna daganan kasancewar gidansu SAMIHA babban gida ne kuma gidan sarauta mai 'bangare 'bangare
*AHMAD RA'UF yake tabawa yana nuna masa amaryar da kawayenta da suke tahowa da ya kasa cire idanunsa ga RUFAIDA da take tsakiyarsu da kallo daya yayi ganeta itace suka taba haduwa waccen ranar a store dan kullum saiya tuno fuskartabanda addu'ar da kullum yake Allah ya qara hadasu ,AHMAD ne kallesa ya katse masa tunanin da take da fadin
"YAYA RA'UF ya ya dai meya faru"
"Kalli waccen yarinya ta tsakiya da suke tahowa da amaryarka"
AHMAD fuskarsa ya 'daga ya kallesu da RUFAIDA ya gani ita ce a tsakiya a layin da suka yi,da kafin yace wani abu suka karaso wajen da sallamarsu,amsa musu sukayi gaba 'dayansu abokan angon gaisawa suka yi da RA'UF ya kafe RUFAIDA da kallo ko 'kiftawa ba yayi tunda suka iso gurin da suke
"Amarya bata laifi kota kashe 'dan masu gida"abokan AHMAD suka fa'da cikin tsokana da fara'arsu sukai maganar"
Kawayen SAMIHA sukayi saurin cewa
"Bata kashe ba dai da har gida za'a korota karewar laifi ma"
"Haka dai kuka ce" inji BELLO da yake cikinsu RUFAIDA data 'dago kai taga mai son karyata maganarsu anan suka hada ido da RA'UF taga iron kallon da yake mata tayi saurin dauke kanta zuwa 'kasa"
NASIBA da itace tasa baki a maganar yanzu tace
"Ai haka ne, yanzu dai mu dai mu shiga daga ciki,kuci abinci da lemo kun shawo tafiya"
Murmushi su AHMAD da abokansa sukayi kawai,su RUFAIDA ne da amarya SAMIHA suka yi gaba ,angwayen suka take musu baya da RA'UF a cikinsu gani yake hatta AHMAD bai kai sa murna ba shida yake ango danshi yau muradin zuciyarsa ya gama a nasa tunanin.*JININMU 'DAYA*

*SADIYA IBAHIM KHALIL*
*(SADIYA KHALIL)*

*WANNAN SHAFIN NAKI NE AYISH HUMAIRA MUHAMMAD MY SISI INA MIKI BARKA DA DAWOWA ONLINE KIYI YADDA KIKESO DA WANNAN SHAHIN DONKE AKAI KAWAI*

PAGE 21
Chapter 20 · 0% Book details