← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 57

Sashe 49

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********** "Rufaida meyasa ne Umma take so ta matsamin akan auran nan,yanzu fisabillah hakan ya dace" Rufaida jin maganar da Wahid keyi yasa ta aje wayarta gefen gado ta maida kallonta gare sa "To mene ne ya faru kuma?" Yace "Sam ta kasa fahimtata tace min nine na fadawa Abba karya amince da auran nan vayan kuma ,ba mu taba maganar da ta shafi aurena da Ruqayya ba nida Abba,amma zancen da ni ke miki yanzu ya kafe kaida fata ba zan aureta ba,ita kuma Umma ta kafe sai nayi auren nan" "To yanzu ya za'ayi" fadin Rufaida "Ina so zanje gida gobe saboda inaso Umma ta fahimceni maganar waya bazata wadatar ba"fadin wahid " amma Yaya gobe gobe banyi kusa ba" "Wanne kusa kanwata kinsan dai wacece Umma idan banje ba kinsman abinda zaije ya dawo ba karami bane" "Eh da kuma hakan,Allah ya kaimu lafiya" jin karar wayarsa yasa shi mikewa ya karasa inda yasa caji a falon ya dauko wayar ya dawo inda yake,ganin mai kiran ya sashi saurin dagawa ganin Ummansa ce "Assalamu Alaikum Umma ina yini" "Wa'alaikumus salam lafiya lau ya aiki" Bai dama tsammaci za ta ce yasu Rufaida ba hakan yasa shi saurin ce mata "Alhamdulillah ,Umma" "Yawwa dama so nake na fadama inason ganinka gobe,saboda Ina so Bukar ya amince da auran nan kana sane indai ba amincewarsa babu abinda zai yiyu" "Eh hakane,Umma dama yanzu make maganar zuwa na da Rufaida" Jin ya anbaci Rufaida yasa ta jan dogon tsaki dan ita ko sunan Rufaida bata so ma a fadama ta shigar mata cikin rayuwar danta wato ma saboda zaizo gida sai yayi maganar da matarsa kila ma har shawara ya nema,tsaki taja a karo na biyu tace "Ok" Wahid dinne yace "Yasu Wasila da karamar kanwata" "Wacce kanwartaka kuma kana da kanwa da ya wuce Wasila ne" "Eh mana Umma,akwai 'yar Aunty da Mama" Tsaki tayi tace "Naji" "Yawwa,Ummi kema yaushe zaki min kani,ko kanwa" "Kamar ya ai yanzu nabar muku kudai kuyi,yanzu idan ka auri Rukayya,ai shikenan zan fara tara jikoki,kaga ai gwara na bar muku tunda wuri" "Eh hakane gama ,Umma amma ga Yasir nan ai yafara zuwa" Hajiya Jamila jin an sako maganar Rufaida da batasan jinta sam yasa ta cewa "Kaga sai anjima"daga haka sukayi sallama ya katse wayar Ya dubi Rufaida yace " Allah Rufaida banason zuwa Zariya akaran kaina dandai akwai muhimmanci a zuwan nawa,amma inajin kar naje Umma tace min na sake ki,jikina yana bani wani abu zai iya faruwa Indai nasanar da Umma abinda Dady yace" Rufaida ta kallesa da hawaye ya taru a idonta tace "Yaya Wahid,ka daina wannan tunanin ni dakai mutu ka raba,nasan Umma ba zata ce haka ba" "Idan to batace hakan ba, idan kafin goben na mutu fa,Rufaida banaso na mutu na barku" Rufaida da ta fara hawaye tace "Yaya dan Allah ka daina maganar mutuwa,bazaka mutu ba,tare zamu mutu" Murmushi Wahid yayi yace "To zan daina amma kinsan da cewa mutuwa dole ce duk mai rai zai zama gawa,kuma na fiso na rigaki mutuwa saboda ke din yanzu kikasa kafa a cikin rayuwarki ni kuma nafara kwana biyu" "Eh,a'a Yaya ni baka tsufa a guri na ba so nake mu rayu mu mutu tare" Dariya yasa ya nuna ta "Oh kinganki dama kina sona sosai haka" Murmushi tayi tace "Yaya idan banso mijina ba wazan so" "Ra'uf mana ai ni duk a tunani na gangar jikinki na aura" Harararsa tayi tace "Kai Yaya,Wannan Ra'uf yaki fita a ranka shi yana can ya manta da shafin rayuwarmu kaiko kana tason sawo mana shi a cikin rayuwar mu,bayan ba muda alaka dashi" "Rufaida kenan ba zaki fahimci yadda nake son Ra'uf a raina ba inajinsa har a jinin jikina" "To fa saboda me" fadin Rufaida tana zaro ido "Saboda inason abinda kikeso Rufaida nasan kin soshi koda a yanzu baya ranki,kinsan mene fata na" Kai ta girgiza yace "To bazan fada ba ma nafasa" "Yaya Dan Allah ka fadamin" Yayi dariya yace" badai shagwaba zaki ba to dama abinda zance shine koda bana raye ki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki" "Oh Yaya kwanaki ma fa ka fadi haka,dan Allah kadaina fadar mutuwa duk sanda bana tare dakai zan zama banida ragowar farin ciki" "Ai hakane Rufaida zaki samu haske da zai haskaka ki a rayuwarki,Rufaida mutuwa dole ce,amma tunda bakyaso na daina fada yanzu dai ina Yasir" Rufaida da murmushinta tace "Ya kwanta a falo,bari naje nadaukosa" "Kyale kawai zanje na daukosa yau ni zan masa shirin barci ma" "Yaushe rabon duniya da ayya raye yau wacce rana m Yace " asabar" yana kokarin fita da dariyarsa *JININMU D'AYA* By Sadiya Khalil 48. DAWOWA LABARI *RUFAIDA POV* Abdul Malik ne ya dubi Rufaida da suke zaune a harabar gidan suna fira kasancewar yau an tashi da zafi garin kuma ba wuta babu inji yara kuma duk sun tafi Islamiyya Tahfiz da yau lahadi babu boko harda Yasir suka tafi Abdulmalik din ya soma magana "Rufaida yau fa naga mai kama dake" "Ni kuma yaya AbdulMalik" Rufaida tayi maganar da mamaki akan fuskarta Ya sake kallonta yace "Kwarai kuwa,da farko dana ganta tana tafiya tunani na bani yayi kece ma,harna fara tunanin maiya faru a kadunan kikazo saida ta juyo da fuskarta naga bake bace,tafiyarku ce sak daya amma a fuska bakwa kama sai dai a fisge" "Oh kodai Samiha ce,ana cewa muna kama nida ita?" Harararta yayi yace "Samihan ce bansani ba" "Aunty Amarya tasa vaki a firartasu tace " oh maiyasa baka tsaya yi mata magana ba,kaga aida ko lambarta saika samowa Rufaidan" AbdulMalik yace"wallahi kuwa Aunty kinga dana hada su kawance,amma zan rika bi ta hanyar kozan sake ganinta,kamar tayi yawa duk da babu a fuska amma akwai a siffar jikinsu" Hajiya Jamila da take jin firarsu tasa baki gurin cewa "ai babu mamaki ko a cikin yawon da akayi ana abun kunya aka sameta" Jin maganar Hajiya Jamila da Rufaida ta jita kamar dirar mikiya yasata mikewa daga gurin gaba 'daya kanta a kasa Ganin Rufaida ta mike daga gurin tayi shigewarta falon gidan kallon data tarar a kunne shi ta kashe tayi kwanciyarta da ita sai yanzu tasan andawo da nepar data san an dawo da wutar ita kam mai zai jama ta zama a can sam shiyasa batasan zama koda a fall ne indai Hajiya Jamila na gurin dan saita fadi bakar magana akanta Ganin Rufaida tabar gurin yasa AbdulMalik kallon Hajiya Jamila ya soma magana "Haba Umma hakan baida ce ba" Hajiya Jamila ta hararesa "To ubanka nace da baida dace ba a cikin maganar,don na fadi gaskiya" AbdulMalik zai sake magana Hajiya Kubra da sai yanzu tasa baki tace "Kaga AbdulMalik kyaleta karka sake yin wata magana" Hajiya Jamila ta harari Hajiya Kubra tace "Kinga nifa banason shishshigi 'dan kine ko nawa,ki barsa ya fadi abinda zai fadama na,a haka a nuna ana sonka sai an ware a fara gulmarka" AbdulMalik ya dubi Hajiya Kubra yace "Mama don Allah kar kice komai" Ya maida dubensa ga Mahaifiyarsa yace "Haba Umma daga ban hakuri" Hajiya Jamila tace "To ubana,hana ni na maida martani" Ganin ba zata fasa maganar ba yasa shi mikewa ya bar gurin don yasan indai yana nan ba zata gaji da magana ba ya nufi falo A falo ya sameta a kwancea a kujera kamar mai varci ammma da gani ba barci take ba zama yayi kujerar dake kusa da wadda take kwance yace "Rufaida kiyi hakuri don Allah,nasan Umma ba ta kyauta ba" Murmushi tayi ta bude idanunta wakeke waken da Rukayya ta fito daga kofar kitchen da Kofi a hannunta tanayi shi ya tsaida maganar da Rufaida Rukayya ta kai kallonta ga Rufaida da take kwance da hankalinta vaikai ga ganin AbdulMalik ba Rukayya ta fara magana cikin bacin rai "Malama ke wacce irin kidahuma ce ya zaki zo ki tarar na kunna kallo ki kashe min ki kuma kwanta wa mutane shame shame a kujera kamar ta gidan ubanki,sakarai kawai ana mata kora da hali kina nacewa mutane..." Ganin Rukayya ba zata yi shiru ba yasa AbdulMalik gyaran murya da zuciyarsa take tukuki jin maganganun Rukayyan Rukayya da sai yanzu ta san AbdulMalik na gurin tuni ta fara zaro ido ta soma magana "Yaya AbdulMalik wa...." cikin bacin rai AbdulMalik ya nuna nuna Ruqayya da ya tsa yace "Ke daka ta munafukar banza ke waya kai kidahumanci,inba kida humanci ba mai zai kawo mace budurwa gidansu saurayin da taso don ya mutu kuma bama zuwa gaisuwa ba a'a zuwa a zauna kamar wadda tarasa mafadi,kuma kenan gidan ubanki ne? da kikazo kikayi shame shame kina cin arziki mai kika hada danan gidan,to ita din ta fiki matsayi da komai anan gidan,donke arzikin Umma kikeci,don koni Rufaida ta fiki matsayi a zuciya ta" Cikin bacin rai da hawaye taf idon Ruqayya tace "Naji ta fini matsayi anan gidan amma ita da ba'ada tabbaci akanta shine,zaka fadamin magana akanta" "Tabbacin ubanki ne va'ada shi akanta,ke ba'ace ba'ada tabbaci akan Ku ba,saike zaki fadawa wata"fadin AbdulMalik "Wallahi mu anada tabbaci akanmu,ita da uwarta take karuwa fa niko mai uwata tayi wallahi muna da banbanci nida ita fiye da tunanin mai tunani" AbdulMalik jin maganar da Rufaida keyi yasa ran Abdulmalik ya kara baci ya mike ya nufi Rukayya zai doketa Rufaida da hawaye ya cika idanunta ganin haka yasa Rufaida mikewa tayi gurinta tace "Yaya AbdulMalik karka doketa kaya hakuri" Hannu AbdulMalik ya dagawa Rufaida ya shiga dukan Rukayya Da kyar Ruqayyan ta kwaci kanta tayi gurinsu Hajiya Jamila tana kuka wiwi Abdulmalik ya bita shima Rufaida ta biyo bayan sa tana kiransa ya dawo amma baya jin ma mai take cewa tana hango Rukayya tana maida lumfashi yayi kanta ya fara dukanta cikin zafin zuciya ba tare da ya bi ta takan mutanan dake rirriqesa ba Tsawar da Abba Bukar ita tasa AbdulMalik sakinta yana maida lumfashi Bai saurari kowa ba ya fara tafiya da niyyar barin gurin Abba Bukar yace "Dawo nan" Dawowa yayi ya sunkuyar da kansa "Rukayya me ya hadaku"cewar Hajiya Jamila Rukayya tana rusa kuka ta dago kanta ta nuna Rufaida wata hararar Rufaida Hajiya Jamila tayi Rufaida ganin haka yasa Rufaida kai kallonta kasa Ganin ta nuna Rufaida Abba
Chapter 49 · 0% Book details