← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 57

Sashe 55

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dady Jabir da ya samarwa kansa gurin zama a daya daga cikin kujerun falon yace
"Husna kaita dakinku tayi sallah,muci abincin saimu kaita gidansu"
Husna tace
"To Abba" daganan ta mike ta saki murmushi ta kalli Rufaida tace
"Muje ko?"
Rufaida ta mike tabi bayan Husna har zuwa ciki"
***********
Abida ce da wata mai aiki suka jera abinci kasan carpet din falon Momy hannatu ta mike ta tsiyaya wa Dady Jabir ruwa a kofi ta mika masa
"Yaya Jabir ga ruwa"dady Jabir da shigowarsa falon kenan ya shiga masallaci sallar la'asar sunyi azahar a hanya,ya amsa ya fara sha
Momy Hannatu takoma ta zauna
"Yaya Jabir ina yini,ya hanya,ya kuma gajiya"
"Lafiya kalau gajiya tabi lafiya"
"Nifa daukata Yaya driver ne zai kawoku,saina ganka da kanka ka tuko motar"
"Eh wallahi Hannatu kinsan drivernsu daya ne,kuma ni nafison na rika tuki da kaina ma"
"Eh hakane,ya kuka baro su Yaya Asma'u,da Ra'uf
"Lafiyarsu kalau,ina Usman din ban ci karo da shiba"
"Bai dade da fita ba Safiyya ta yomin waya kun iso fitarma ta dole ce yayi an kirasa a gurin aikinsu ne,bai tsammaci zuwanku yanzu ba,yanzu Dady haka zamu bar yaron nan Ra'uf kiri kiri yaki yin aure"
Dady Jabir yayi murmushi yace
"Ai halin yaron nan sai shi,Amminsa tace har yau ya kasa mantawa da wannan yarinyar kuma kema kinsan ko giyar wake muka sha ba zamu aura masa yarinyar ba da silar danginta muka rasa farin cikinmu"
"Hakane Dady to mai zai hana a hadasa da Safiyyan da Yaya Ma'u tace kun yanke shawarar hakakwanakin baya tunda shi ya tsaya shirme kamar karamin yaro"
"Eh to Hannatu kinsan dai matsalar Hajiya ba lallai ta yarda ba"
"Ina tunanin zata amince tunda ita ma ta matsa yayi auren yanzu,kuma yanzu Safiyya tana tare damu"
"To zan jarraba na gani,ko Allah zaisa a dace"
"To Amin"
Sallamar su Rufaida ita ta katse hirar dasu Dady keyi suka amsa musu
Momy Hannatu ta dubi Rufaida tace
"Dama yanzu nake shirin kiranku,kuzo aci abinci"
Safiyya tace
"Momy ita tafiya zatayi anzo daukarsu"
Momy Hannatu tace
"Ba Yaya Jabir yace har gida za'a kaiku ba" tayi maganar tana kalon Rufaida
"Wallahi Aunty dazu Yayanmu ya kirani waya na masa kwatance unguwar da muke yanzu,shine naba Safiyya waya ta masa kwantance yace yanzu yana kusa da hanyar zai biyo ya tafi damu"
Dady Jabir da baiji dadi ba yace
"To shikenan amma dai,banso ba naso na kaisu har gidan"
Daga haka suka fito rakata
Har jikin motar Abdul suka kaita da ya shigo da motarsa ciki Abdul ya fita suka gaggaisa ya kwaso kayan su Rufaida a motar Dady Jabir zuwa motarsu bayan suna kokarin shiga motar Abdul ya dubi Dady Jabir yace
"Yalla'bai mungode sosai Allah ya kara girma"
Dady Jabir ya dubi Abdul yace
Amin,amma kun mana laifi daya fa"
Abdul yace
"Yallabai laifin me mukayi"
" zaku tafi da abokina"
"Abdul yayi murmushi
" au Yasir,ai yalla'bai zamu zo nan mukawo ma shi"
Yace
"Nida ba'anan nake ba,saida in zaku barmana shi mu tafi tare,kayima Babansa magana ko zai yarda na tafi da shi,ya shiga ranmu sosai"
Abdul yayi murmushi yace
"To shikenan yalla'bai"
"Ai nasan ba zaku iya ba fade kawai kukayi, nan gidan kanina ina fata zaku cigaba da zumunci tunda garinku daya
"
"Insha Allah yalla'bai"
Husna da take sauraransu tace
"Ai Abba ko busu zo ba,mu zamu je kodan Yasir yaron ya shiga ranmu lokaci daya"
Abdul yayi murmushi
"Haba mai zai hana mu muzo ma"
"To Allah yasa" fadin Safiyya
Daganan suka shiga motar Rufaida a gaba Yasir ya na baya shikadai yana wasa da motar da Da Dady Jabir ya basa su Rufaida suna ta godiya har Abdul zai tada motar Safiyya tasa kanta cikin glass din motar ta dubi Rufaida tace
"Rufee bamu lambarki,saimu rika gaisawa"
"Rufaida ta fado mata tasa daganan Abdul ya tada motar suka fara kokarin barin gidan su Husnan suna dagawa Yasir hannu har saida suka ga barinsu gurin

Abdul da ya soma tukinsa ya dubi Rufaida da take gaban motar yace
" oh Rufaida ban taba tunanin a zamanin nan za'a samu mutane irin wadannan ba,mutanan arziki kiga nifa kamar sun sanmu"
"Rufaida tace
" wallahi kuwa yaya suna da kirki sosai,Yaya yana ga har kayi kumatu bayan rabuwar mu"
Yayi dariya
"kai Rufaida banda sharri"
"Wallahi Yaya da gaske nake"
To nidama kinsan ina da kiba dan duk nafi ku,karatu ne dama ya tsotseni yanzu kuma tunda nagama karatu kuma ina dibar albashi mai tsoka dole na canza"
"Eh lallai hakane"
"Muje gida kiga abun bazata"
"Menene Yaya kodai budurwa kayi ne,tazo tarbata "
"Oh budurwa kuma Rufaida"
"Eh mana Yaya"
"Tab aini ba yanzu zanyi aure ba"
"To Allah ya kaimu lokacin ya hadaka da ta gari"
Ya amsa da Amim
Ya dora da cewa
"Oh Rufaida ya zaman naku,keda su Umma, naga ma duk kin rame"
"Hmm kaidai bari Yaya ba dadi"
"Ai nasan dama bazai dadi ba,Allah dai ya raba ki da auren na kaddara,dan wallahi yanzu ko mai za'ace a kaina bazan yarda karo na biyu ayi wa kanwata wannan auren ba dan saidai muyi fito na fito dasu Abba"
Ido ta zaro
"Kai Yaya su Abban"
"Ko su waye kuwa,kin manta waye Abdul ne ni bana goyon bayan zalinci a rayuwata,dubi fa yadda a kari ka gasa ki kamar biredi,basu a dubi yadda aka rika gasa mu a baya kafin mu samu wannan canjin rayuwar,kina gani yadda har yau ba musan dadin dangi ba,dukda kasancewarsu dangi Ummi da Abba duk daya amma basa nuna kulawarsu gare mu"
"Babu komai Allah yaya komai yana gaf da zama tarihi"
"Rufaida kenan anya kuwa,kina sane fa ko Abba Bukar ba wani sonmu yake ba,ni tsorona kar abinda ake fada akan Ummi ya zama gaskiya"
"Haba Yaya karkai fatan hakan,nina san komai zai wuce"
"To Allah yasa Rufaida"
Daganan suka cigaba da firarsu har suka isa kofar gate din gidan nasu
Horn yayi maigadi ya bude musu gate din suka shiga yana kokarin yi musu sannu da zuwa

******
Gaba 'daya gidan ya rude da murnar dawowar Rufaida kannan nata suka rasa inda zasu sa Rufaida don murna ga Yasir da kowacce kenan nan da shi su Rumaisa an zama 'yan mata tana shirin Candy a lokacin Abdul-Rashid ya tafi gaba da sakandire yana karatunsa a Northwest sai da suka gama murnar suka fara kokarin shigo da kayan Rufaida cikin gidan wannan kenan.[10/3, 10:25 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU D'AYA*

Sadiya Khalil

53
Book 2 page 3

Wannan book 2 ne page 3 yakama 53 kenan

Safiyar litinin

Misalin karfe 11 na safiyar ranar Rufaida tana zaune a falon gidan ita kadai tana kallon wani Film na Sanam teri kasam a Bollywood wayarta ce ta dauki kara ta daga da sallamarta fuskarta da alamun farin cikin ganin mai kiran ta maida wayar a hands free ta cigaba da kallonta
"Kanwata kin buya ko flashing bakya yimin"
"Kai Yaya Malik haka ma zaka ce"
"To ai haka ne ko kina yimin ne,abokina yasa kin mata da 'dan uwanki"
"Kai Yaya duka fa jiya muka fara waya da Zahraddin din fa"
"Koma yaushe ne nasan dai,zuwa yanzu kinyi na'am da abokina"
"Hmm Yaya kenan"
"Meye kuma hmm ko baki sonshi ne,karfa ki yaudararmin abokina,wani yazo yayi wuf dake"
"Kai Yaya fatan da zaka min kenan"
"Ba fata bane Rufaida,nasan irin ku kyawawan mata aurenku rabo ne"
"Kai.Yaya Malik ina wani kyau"
"Hmm Rufaida kenan,nidai yanzu mu koma batun abokina,please karki kishi Rufaida yace wa Mamarsa inbake ba sai rijiya,sannan kuma ma Zahraddin mutumin kirki ne,haka ma iyayensa nasan zasu rikeki amana"
"Insha Allah"
"Yawwa kanwata,yawwa na turawa Safiyya photonki yarinyar da nace miki kuna kama kwanaki"
"Eh nagane"
"Ina turamata photon tace min ta sanki"
"Niko a ina tasanni" ta yi maganar tana zaro ido
"Ashe kwanaki a motarsu kuka zo Kano"
"Dan Allah Yaya Malik,wallahi nima nayi wannan tunanin da naji sunanta,kuma naga yanayinta yayi kama da wadda ka bani labari"
"Eh wallahi itace"
"Suna da kirki sosai,amma nifa banga kamar mu ba"
"Itama tace bata gani ba,amma ni kuma na ganta kune dai kuka kasa gani banda yanayin tafiyarku kuna da siga a fuska ta fannin kalar hancinku"
Dariya abin ya bata tace
"Yaya Malik kenan kanada zakulo kama wato harta hanci zaka ga kama"
"Au dariya na baki ma ko?"
"Eh mana ai abin dariyar kayi,don wannan safiyyan ta fini kyau"
"Ita din ko kafarki bata kama ba"
"Zanfada mata kuwa"
"Yi maza kar kuda ya rigaki,kinga ni ina Yasir ne"
"Yana can suna wasa da Rahima"
"To idan sun shigo falon ki kira ni ki hadamu"
Daganan suka yi sallama Rufaida ta maida hankalinta ga kallon da take yi
******
Sallamar Ummi Hauwa'u ya katse tunanin Rufaida da take zaune a dakinsu saman gado
Rufaida murmushi ta kakalo ta amsawa Ummin sallamar Ummi Hauwa'u ta karasa shigowa dakin ta zauna gefen gado kusa da inda Rufaida ke zauna

"Ummi ina yini" fadin Rufaida tana sinne kai
"Da ban wuni ba zaki ganni ne yini ba zaki ganni ne,ace yinin yau baki leqo ko da falo ba,haba Rufaida me ke damunki ne?"
"Babu komai Ummi"
"Ban yarda ba,nice mahaifiyarki nafi kowa sanin halinki,nasan hakanan bazaki ki fitowa waje ba,Rufaida a yanzu haka baki da wanda ya fini a rayuwarki karki kokarin boyemin damuwarki"
Chapter 55 · 0% Book details