← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 57

Sashe 14

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da Weekend ya kare Monday litinin su Rufaida suka shirya Abbansu da zai shiga Makaranta suna wani taro a BUK din ya tsaya ya saukesu a Al'AZHAR har bakin gate din makarantar ya kaisu inda hankalin Samiha ya tafi a motar da aka sauke Sir AbdurRahman motace maikyau da tsada drivernsa ya tsaya ya fito Samiha tace"Abba kalli malaminmu maikama da yaya AbdurRafi"Abba Aliyu da ya 'karasa parking ya dubi AbdurRahman kasancewar ya 'dan juyar da fuska bai ganshi sosai ba ya daiga bayansa saida ya sake kallonsa yaga fuskarsa shidai baiga wata kamarsu ba sai dai a fisge"Samiha tace "yawwa Abba ka ganshi ko?yace mata " Eh a ina yaron yake kunsan shine"Samiha ta cemasa"Khalid Bashar way yake kusa da gidanmu wasu ma cewa suke 'dan sane,TP yazo makarantarmu inda kake lecturing yace yake karatu BUK" Abba Aliyu yace"ok,Allah sarki ba lallai nasan yaron ba akwai daliba da yawa kinsan kuma department department ne "tace " eh hakane"da haka suka fice daga motar sauran yaran suna cewa sumafa basu ga kama ba,Abba Aliyu da shima baiga kamaba yaja motarsa ya bar harabar makarantar,a kofar Gate 'din suka ci karo da Sir Samir suka gaishesa suka shige tare da ya shaida fuskokinsu yaran ne ma baigane ba,saboda baya daukar 'yan ajujuwansu,yace"Health prefect da Labour ne ashe"Rufaida tayi murmushi"
Samiha tace"Sir yanzu Abbanmu ya saukemu a mota da har zan kwala ma kira ku gaisa"Rufaida da take zungurar Samiha tayi shiru taki banda shiga ukun Samiha meye na fa'dar hakan bandama koyarwa daganin wannan matashin AbdurRahman zaiyi ji dakai,kuma ga iron motar da aka saukesa da gani dan masu dashine sosai,amma Samiha sai zaqalewa take,tana nema ta wuce gona da iri"AbdurRahman yace"Aiya wani lokacin zamu gaisane"Samiha tace "hakane " tabar maganar daga haka kar dalibai su hangosu a yimata wata fassarar,dan tasan halin 'yan makaranta"
Ana gama a assembly malamin biology AbdurRahman ya shigo yafara koyarwa nan aka aiko wata daliba ta kira Rufaida da sallama 'dalibar ta shigo ajin inda AbdurRahman ya tsaya da koyarwar ya amsa 'dalibar tace"Sir ,Sir Nura yace Rufaida Aliyu Bukar tazo"AbdurRahman yace"to kice tana zuwa"ya dawo ya kalli 'daliban yace"wacece Rufaida Aliyu Bukar"Rufaida ta mike tace"Sir gani"AbdurRahman yace "au Health prefect dama kece Rufaida?" Tace masa" Eh"yace "ok,kije Sir Nura ke kiranki kiyi maza kidawo kinga lesson muke"da haka Rufaida ta fito daga bencin tana cewa"to"shi ko AbdurRahman zama yayi akan kujera ya huta kafin Rufaida ta dawo ya cigaba shi sai yanzuma ya tuno Rufaida itace su Nasiba sukace yana kama da wani yayanta,shi kasancewarma baidamu da sabgar ba yama manta gaba 'daya tundaga ranar baisake tunowa ba ,saida ya dawo ya cigaba da lesson 'din harya gama ya fita ya kira Nasiba"ya bata wani class work daya basu ta rubuta a allo period ta gaba da malamin period din baizo makarantarba zaizo ya duba"daliban da sai zagin Sir AbdurRahman suke don ya fiye takura daga fita abada wani aikin aji suna mita suka rubuta suka fara duba test Book 'din biology ita Rufaida key point kawai ta duba tayi taba Samiha tayi ita kanta Nasiba zagin AbdurRahman tafarayi duk shirin da suke da AbdurRahman din don kusan a ajin sunanta yafi riqewa
Periof nashiga yana shigowa ajin ya fara da duba litattafan daliban benci benci matanma sunfi mazan kokartawa bencin su Rufaida ya karasa da shine ya bari na karshe duk sunfi sauran kokartawa dan da marking zaiyi sune suka cinye duka tundagan suke 'dan shiri dan shi AbdurRahman yanaso yara masu kwazo Samiha har number dinshi gareta da Ahmad ya kawo mata wayarta mai tsada ba laifi infinix ce da a yanzu haka ansa rana da sunyi candy za'ayi bikin dukda yadda Samiha taso a hada bikin koda na Yaya Saudat ne da yanzu haka tasamu saurayinta mai sonta cousin dinsu a sokoto Mujahid dan tuni ta hakura da wancen da suka hadu a biki dan akarshema wayoyinsa daina shiga sukayi,hakanan Yaya Saudat ta hakura da jiran gawon shanun da take ta amince da Mujaheed Abba Hashim mahaifi ga su Samihan shima kansa ya amince da hadin auren kuma abin yayi masa dadi sosai itako Momy Maryam mahaifiyarsu Samihan da Mujahid din yakasance 'dan yayanta tamafi kowa murna da wannan hadin
AbdurRahman ranar da zai gama TP dinsa haka 'yan ajin duk suka ji ba da'di kasancewar sunsan ba lallai su sake cinkaro da Shiba koda a hanya ne don su dai sunsan haduwa da iyalan Khalid Bashar da kamar wuya dan Nasiba Shehu da Hauwa Umar sunada ya kinin gaskiya suka fada musu dukda yawanci yan makarantar 'ya'yan masu da shine amma wasu sunfika kaima kafi wasu sunfika haka rayuwar ke tafiya.
AbdurRahman ya kalli su Nasiba gaba 'daya su shida group 'dinsu harda su Rufaida da yake ji a ransa duk ba dadi saboda yadda ya fara sabawa da yaran da yake jinsu har a ransa gasu masu kwazon karatu donshi ko 'yan ajin basu taba masa rashin kunya ba ko zaginsa sai dai ko a bayan idansa shiyasa yake ji babu dadi bayan ya fito daga ajin nasu inda yake tsaye birandar ajin nasu sukuma sun tsugunna a gefe yace"Nasiba Shehu ya maganar karatun naki ne"tace masa"Sir Jamb zamuyi nidasu Zainab Farouk,da Hauwa"AbdurRahman yace"banji kince su Rufaida da Samiha ba"Nasiba tace "lah sir dama banfa'dama su Samiha aure zasuyi ba" ita da Rufaida"Samiha tace"Sir karya fa suke"AbdurRahman yace"to inma shine aiba wani abu bane"Hauwa'u tace"wallahi Sir bama karya muke ba itafa Samiha bayan candynmu da sati biyu za'ayi bikinta,itace dai Rufaida bamu sani ba"AbdurRahman yace "hala wannan yayan Rufaidan da kuke cewa muna kama zasuyi auren zumunci dashi da Samihan,gashima har zan tafi bamu haduba" ya fada da murmushi kan fuskarsa Dan shi ma tunaninsa sunada dangantaka"Aisha Mudassir tace "Eh Sir laifi su Samiha ne basu hadaku kun gaisa ba amma yarone fa koni nakusa girmarsa"Rufaida ta harari Aisha"tace kinma girmesa kawai zakice"AbdurRahman yace"To masu 'dan uwa,don tace ta kusa girmarsa shine harda bakar magana" Rufaida tace"Sir koni fa shekara kusan biyar ya bani inji Umminmu shine zatace ta kusa girmarsa "murmushi AbdurRahman yayi kawai yacanza maganar da cewa"saura kuma kumanta dani lokacin bikin kuki fadamin"duka suka amsa da Insha Allah zasu fadamasa tunda suna da number dinsa da haka ya musu bankwana ya tafi suna kewar juna*JININMU 'DAYA*

Sadiya Khaliy💞
Page14

Zaune suke gaba 'daya yaran Abba Aliyu a babban falo da yau yake shirin tafiya zariya da yara hutu Abba Aliyu ya dubi kowa na falon yace"kufa nake jira kowa ya tsaida gidan da zaije hutu kar sai munje Ku batamin lokaci naji Rumaisa tace Kaduna gidan Zainab zatayi hutu shima AbdurRashid yace can zashi"Rufaida jin ba'a anbaceta a tafiyarba dan tagama sakankancewa har da ita tace"Abba yanzu ni banda ni"Ummi Hauwa'u ta harareta tace"bikin Samihan zaki bari ki tafi ko kuwa"Rufaida da ta tuno yanzu dan da tunima anyi bikin bangaren su Ahmad sukace a bari ayi hutun Makaranta sai ayi tace" a'a Ummi"Abba Aliyu da shima ya tuno da bikin yace"ni banda zuwa porthacourt din nan kamar dolece ni aka za'ba naje Hauwa'u bazan 'ketare bikin nanba bikin 'yata sukutun da guda"Ummi Hauwa'u tace"hakane Abban AbdurRafi aiga AbdurRafi zai wakilceka"Abba Aliyu yace "Eh hakane,saura kwana nawa bikin ne Ummi Hauwa'u tace saura sati biyu" Abba Aliyu yace haba harma dawoma"Rufaida tace"Abba kona ha'da kayana naje nima"Ummi Hauwa'u tace "wai Rufaida meke damunki raban IV da zaku fara fa a wannan satinfa,kuma kinsan ranar asabar din nan amarya zatayi yininta a Kano,tunda a sokoto za'ayi bikin akaita daga can"Abba Aliyu da yaga matartasa ta hakikance Rufaida bazata hutu ba kamar ba garinsu zata hutun ba shi abinma dariya ya basa dan yasan badan komai take wannan hanya hanyarba don kartaje ne suma su AbdurRashid dan bayarda zatayi tace bazasu bane shi yarasa maiyasa Hauwa'u takasa manta baya dukda yasan abubuwan da suka faru da aurensu dama bayan aurensu,haryau tsoro take kar nata suje gidan da tasha wahalar rayuwa a ciki,suko yaran da basu fahimci dalilin fa'da Umminsu ba dan cikin fada take maganar abinda basu saba jiba gurin umminsu saifa ta tutance dukda suma suna fuskantar tsangwama amma a gidan Abba Bukar da matarsa ke musu shiyasama ko zuwa zariya zasuyi gidan Gwaggo kakarsu suke zuwa da Malam da Gwaggo suke lalla'basu kamar kwai sai duk jikin yaran yayi sanyi jiki ko harda AbdurRafi da yake tuno wasu abubuwa da suka dinga faruwa a zamansu gidan Abba Bukar kafin Abbansu ya samu aiki yadawo Kano,AbdurRashid ya katse shirun da cewa " Abba na shirya kayana tun jiya kuma mungaisa a waya da Aunty Zainab tun kwanaki a gidanta zanyi hutuna",Abba murmushi kawai yayi don ya fahimci AbdurRashid gudun yin hutunsa yake gidan Abba Bukar,tunda yaron yasan acan zasuyi hutun Abba Bukar nema ya bukaci aje ayi hutu a gidansa danshi Abba Bukar mutum ne mai son danginsa banda Allah ya hadasa da mace mara kirki da kusan Hajiya Jamila ke juya gidan Abba Aliyu yace"shikenan"ke Rumaisa sai kiyi a gidan Abba bukar"Rumaisa ta amsa da"to"badan taso ba ita don itama kanta batasan hutu gidan Abba bukar da tasan can za'a kaita tunda Abba Bukar ta fiso tayi a gidan kanwar babanta Aunty Zainab ko gidan Gwaggo saboda tsangwamar da suke sha indai sukaje hutu gidan Abba bukar gurin Hajiya Jamila saukinsu suje gidan kakarsu Gwaggo "Ummi Hauwa'u bataji da'di ba jin Rumaisa ce zatayi hutu gidan Abba bukar dan bata manta rayuwar da tayi a gidan saidai sam bata nuna koda a fuska ba da haka suka shirya tafiya har bakin mota suka rakasu Abba Aliyu ya bawa Ummi Hauwa'u kudin kashewa ko yaransa ragowar zasu bukata sai kuma kudin cefanan kayan miya abun abinci basuda matsala akwai komai ya sake jaddadamata ta kula masa da yaransa sosai dukda yasan baida matsala ta wannan fannin da Hauwa'u haka ma babban dan nasa AbdurRafi yana kokarin kula da yaran indai Abba Aliyu bayanan kobaya kusa fiyema da shi danshi Aliyu sanyi garesa abunda ko zai batawa Aliyu rai to babbane
Chapter 14 · 0% Book details