Sashe 17
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AAhmad dake dannawa wayarsa da yake gefen gado zaune ya maida dubensa ga AbdurRa'uf daya kwanta a makeken gado yana lumshe ido yace"yanzu brother bazaka fito koda fall bane muyi fira ba wato dai har yau bazaka canza ba daga wannan tafiyar nasan cewa zakayi ka gaji ne fa"AbdurRa'uf ya bude idanunsa duka ya kalli Ahmad yace"Gaskiya yaron nan ka rainani da yawa yanzu duk a wannin da nayi a jirgi shine zakazo kana takuramin na fito ayi fira ni kaga Malam tashi ka bani guri na huta"Ahmad ya yi murmushi saboda yadda yasan AbdurRa'uf da akwaishi da son girma kamar wasu shekaru ya basa duka duka baifi shekara daya AbdurRa'uf ya bashi ba sassauta murya yayi yayi yace"haba Yaya AbdurRa'uf ayimin afuwa"AbdurRa'uf baki ya yatsina yace"shikenan,in Kasan me kuwa"Ahmad yayi saurin cewa"A'a"AbdurRa'uf yace"Kano ta birgeni sosai babu cikowa daga zuwana na fahimci haka,anya bako a Kano zan nemi mata ba na aura,idan mundawo Nigeria nayi gidana na zauna anan"shi Ahmad ma dariya abin yaba shi amma sai yayi murmushi yace"Mutumina tanbayar da zanma kenan ya kaga garin Kanon,matsalar tsohuwar can ta hanani gini anan wallahi"dariya AvdurRa'uf yayi yace"gaskiya takwareka ka samu mace 'yar Kano amma tahanaka zaman Kano"Ahmad yace "a'a wai Samiha kake nufi ai ba 'yar Kano bace 'yan sokoto ce"to amma ai rainon kano ce ai Malam angama magana,nifa yadda naji kano farar daya garin yayi min hakama matan cikinsa inada yaqini akansu zakaji dadin zama dasu da yardar Allah" Ahmad yace"gaskiya kuwa"amma kasan matar nan dakyar ta amince na aureta ,ai indai matarnan na raye bazata bari muyi abin kanmu ba,wai haka tayiwa su Abba ne"AbdurRa'uf yace" da alama dai hakan tayi musu ai fitinanniyar tsohuwa su Abba Allah ya hadasu da ita"Ahmad yace sosaima kuwa kaima kasan Karimar Baffa Sule takeson hadaka da ita,itama naji ance Karimar tana sonka jira Hajiyar take kazo ayi magana"ido AbdurRa'uf ya zaro yace "to wallahi ba Wanda ya isa yayimin auren dole tun wurima ta canza sheqarta,shiyasa naga tunda Hajiya ta samu labarin zuwana indai na kirata mugaisa saita hadani da Karima mugaisa" Ahmad yasa dariya Abdurra'uf yace"au dariya ma na haka cikin bacin rai" Ahmad ya sassauta murya yace "haba Babban mutum kaima kasan yadda akeji dakai a gidannan Baffa Sule bazai amince ba bare kuma kasan Baffa Alhaji bazai amince ba Indai bakaso"AbdurRa'uf ya dawo da nutsuwarsa da taso gushewa da yace" Eh hakane Ahmad"Ahmad da wayarsa tayi kara yasa shi fasa maganar da yayi niyyar yi ya duba mai kiran ganin sunan da yasawa Samiha yasa shi murmushi ya kara daga ya kara a kunne dan yasan ganin bata kiransa ba hardare yasata kiranshi tunda sukayi magana a WhatsApp tace masa zasu tafi rabon IV ya sauka ba tare ma da yabata amsa ba yafara cikiniyar tarbar Dan uwan nasa AbdurRa'uf Sallamarta ita ta katse masa tunaninsa ya amsa mata ta gaishesa cikin girmamawa ya amsa kana yace Madam ansha yawo yau to ya gajiyar hanya Samiha da take zaune tana duba dinkinsu ita da Rufaida da Rufaidan ke 'dagawa tace masa "aini fushi nake dakai yau gaba 'daya ko Flashing ko text dinka babu a wayata naka" murmushi yayi yace"tuba nake amaryata"itadai Samiha kunyar maganar taji da Ahmad yayi cigaba yayi dacewa,kinsan Yaya AbdurRa'uf yau ya sauka a Nigeria shine dalili"Samiha tace" wallahi na manta shaf kace masa ina masa sannu da zuwa"da murmushi kan fuskar Ahmad yace"zaiji da kyau,gashinan a gefe na"da haka suka cigaba da firarsu "AbdurRa'uf da yaji firar ba mai karewa bace mikewa yayi yana cewa"na lura bazaka daina cikamin kunne ba" Falo ya nufa "da nan 'dinma kayan auren Ahmad da AbdurRa'uf shine ya ha'da komai ya vayar tun wancen satin a kawo su Nigeria sai a jiya suka iso da yanzu shirin mikasu ake gidansu Samihan,haka ya zauna inda kowa yaba kayan yake yasan dama Safiyya da Amminsa ba bayaba gurin iya zaben kaya shidai murmushi yake kawai muryar yakumbonsu yaji tana cewa
" Masha Allah Babban Mutum anyi zumunci kaya sunyi Allah ya bar zumunci ya nunamin naka nadau danka"murmushi yayi kawai yace kindaina auren nawa kenan"Dariya tayi tace"kadubeni kaga aina tsufa gwara na barka ka auro budurwa son kowa kin wanda ya rasa,dukda na rasa irin matar dama kaika keso tunda indai India ne akwai kyawawa " murmushi yayi yace "Yakumbo kenan,nifa nafison mai kyakkyawan hali" Momynsu Ahmad sai yanzu tasa baki tace"aiko zaka dade baka samu ba tunda baka nema,kullum mukai waya da Yaya Asma'u saita yimin kukan hakan"Dariya abin yaso basa ma yace"Ai Momy komai lokaci ne,kuma wani jinkirin Alkhairi ne"Yakumbo tace"Hakane amma sai a dage da nema har Allah yasa a dace,amma idan baka nema ai ba lallai ace kasamu kanada ga zaune ba"yace hakane Yakumbo,zan riqa dubawa insha Allah"tace masa yawwa kag shekarun sunfara ja a kalla kayi talatin da doriya"ido ya zaro yace"haba yakumbo har yau ko talatin bankai ba"tace "kaidai kawai yaron zamani da basa san shekaru" Momy tayi dariya tace"A'a Yakumbo ba'kin shekaru suke ba shekarunsa kenan wancen AbdurRa'uf 'din dai kike tuna shekarunsa",Yace yawwa Momyna fadamata gaskiya dai tsohuwar nan ta rikice"
"Duban Yakumbo Momy tayi ta suka kalli juna itada AbdurRauf dan sunsan Yakumbo halinta sarai bataso ace ta fara rikicewa Harararsa tayi tace" tsohuwartawa kake ciwa fuska ko harda ta rikice ma ko?"
Yace"tuba nake Momy"
Yakumbo ta hararesu gaba 'daya tayi ta wasan nan tace"Hannatu harda kallona kafin kiyi magana ja'irar yarinya nasan da bani hardake za'ayi maganar gwara na tattara na koma dan-bat.....
Husna data shigo falon ta katse maganar ta zauna kusa da Yakumbo tana dafa ta tana cewa"keda waye haka Yakumbo kike sababi haka harda maganar komawa Dan-batta"
"Nida wa'dannan ne ta nuna su Momy da AbdurRa'uf harda kallon juna kafin Hannatu tayi magana,gwara na tattara nakoma inda nafi wayau ai" dariyar abin yaba Husna da itama Yakumbon dan ayi tayi dariyar take wannan maganar"Husna ta juya ga AbdurRa'uf tace"Yaya kaji fa,ina Yaya Ahmad din ne"
"Ina jinku,Yana ciki yana amsa waya"
"Hala da Samiyy suke wayar ko?
"jeki tanbayesa kiji"
Tasan bakar magana ya fadamata hakan yasa tayi shiru ta mike ta kunna TV shi ko da Momy suka cigaba da firar zuwansu Ammi cikin wannan satin,dawowa Husna tayi ta zauna tana cewa"amma Yaya harda Safiyya za'azo ko?"
Yace "Bansaniba kin kagara tazo kenan ko,a fara Isar mutane gida kamar gidan kallan Kwallo don hayaniya" Dariya tayi tace"ai haka yafi ni ni kadaice gidan bayamin da'di"
"Shiyasa kike damin mutane ba" Ahmad da yashigo falon shima ya nemi guri ya zauna suka cigaba da firarsu.
LIMAT SADIY 🖊️*🔗JININMU 'DAYA🔗*
By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️
Hikima writers asso......
17
"Yakumbo gaskiya kamata yayi kiya hakuri da tafiya mu tafi tare daganan gurin bikin murmushi" Kallon Husna Yakumbo tayi da ita ke maganar kana tace" kyayi kya gama yarinya sauranma sunyi sun gama"Husna ta mike tana 'bata rai" daya daga cikin matasan falon yacewa Husna "Haba Amminmu dawo ki zauna,meye abin fushi,
Tace "amma Yaya Bello daga fadar gaskiy.." Yace "kinga kyaleta"
Yakumbo data mike tayi hanyar barin falon,dan ta fahimci bata mata lokacin yaran sukesan yi
Su AbdurRa'uf da Dady da Momy har bakin mota suka raka Yakumbo Husna ta biyosu da jakar Yakumbo tasa a gidan baya addu'a sukayi musu Allah ya saukesu lafiya suna zolayar Yakumbo"cewa ta kagara taje taga Baffa shiyasa ta damesu da saita koma 'Danbatta yau" Murmushi tayi tace"to meye a ciki tunda Ahmad yafara nuna baya auren dani tun kafin ku juyan baya harda Babban mutum da Bellotu gwara naje nima na rike mai gidana kar matanku su yimin kwace nan gaba "AbdurRa'uf yace" wato Yakumbo hardani duk yadda nake auren nan dake"Bello dake kokarin tada mota yace" Yakumbo cefa ai duk ciki indai akan Baffa ne zata iya dena aure da kowa su Dady murmushi sukeyi su dai da haka motar su tabar gidan ran kowannensu babu dadi
ABDURRA'UF JABIR MAHMUD DANBATTA
Haifaffen garin Kaduna inda aiki yakai mahaifinsa AMBASSADOR JABIR MAHMUD DANBATTA a matsayin jakadan Nigeria a India da Matarsa daya Asma'u da akayi musu auren zumunci,inda a yanzu suke da zama a New Delhi babban birnin India AbdurRa'uf yayi karatunsa a fannin likitanci ya karanci Medicine a UNIVERSITY OF MEDICAL SCIENCE NEW DELHI yanzu ya zama kwararren likita a asibitin CHAUDHARY BRAHM PRAKASH AYURVED HOSPITAL,asibiti ne babba da yake zaman kansa,AbdurRa'uf shine 'da 'daya tilo gurin Asma'u ta haifi na farko ya rasu daganan ta haifesa ta yi masa kanne wajen hudu duk duk suna rasuwa a karshe haihuwar ta tsaya mata,Safiyya a garesu kuma 'yar riko ce"Shureim Khan Salim Abokin Ra'uf ne a India tare suke a makaranta hakama a gurin aiki Shureim haifaffen dan India ne shi
AHMAD USMAN DANBATTA daya kasance Aboki kuma 'dan uwa na jini ga AbdurRa'uf tundaga yarinta har zuwa girma kasancewar halayyarsu da ta zamo daya itace takara assasa abotar dukda da tazarar shekaru daya tsakaninsu bai hana su abota ba tundaga primary har zuwa secondary da suna shekarar karshe a makaranta Jabir yasamu Ambassador
USMAN MAHMUD DANBATTA mahaifin Ahmad Kani ne ga Jabir mahaifin AbdurRa'uf uwa daya uba daya yana zaune a cikin garin Kano da aiki ya maidosa Commissioner of Police ICP yana zaune a Zaria Road da Matarsa daya Hannatu da aka musu auren gida na zumunci kanwar Asma'u ce ita Mahaifiyar AbdurRa'uf Ahmad kannensa uku shine babba sai Husna da Ammar,da Abida
Ahmad a UK yayi degree dinsa ya samu koyarwa yanzu a haka a Jami'ar Northwest