← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 57

Sashe 57

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shekara guda da auren Amina ta haifi yaronta namiji mai suna Ahmad.

Amina da tasowarta tafi Aliya kyau da farin jini samari suka fara tururuwar son auranta,cikinsu duk Habibu tafi so da yake abokin Tijjani mijin Aliya da Habibun shima magani ne kamar Tijjani

Malam Basiru a kullum cewarsa Amina matar manya ce,shiyasa duk yaki bawa manemanta damar turo magabatansa, Allah ya amsa Addu'ar mahaifinta taje sayayya Central Market Allah ya hada ta da Mamuda da taje siyayya shagon nasa

Shiko Mamuda yana ganin Amina a shagon nasa da taje siyayyya ganin nutsuwar yarinyar ta kwanta masa a ransa har yaji yana son ya kara aure da ita
Abokinsa da suke tare a shagon sanda taje siyayya ya tanbayesa koya santa ganin sunyi magana yace masa
"Eh yasanta a unguwarsu take mahaifinta ma a nan kasuwar yake sana"ar dukanci"
Sosai abin da abokin nasa ya fadama sa yayi masa dadi ganin yasan ma mahaifin Aminar Malam Basiru mutumin sane ma sai dai bai taba zuwa gidansa ko wani abu ba a iya kasuwar suke hurdarsu anan ya yanke shawarar zai fadawa Malam Basiru yaga yarsa yana son aurenta

Malam Basiru da Mamuda yayi masa wannan maganar ba karamin dadi yaji ba,ganin koba komai Amina zata auri babban mutum Kamar Mamuda da yana sane da cewar Mamudan yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha daya amma shi koda Mamuda ya fadama sa yawan 'ya'yan nasa da matansa har su biyu bai damu ba,kudi sun rufe idonsa,koda yajewa da Amina da mahaifiyarta batun auren Saude kin amincewa tayi ya za'ayi akai Amina gidan mai mata bama mace daya ba a'a har biyu ga yaran sa 11 da take da tabbacin a 'ya'yan nasa akwai sa'ar Aminar

Haka dai Malam Basiru ya shafa wa idanunsa toka yace arziki yana kiran 'yarsu suna gujewa waccen shekarar yaji labari yakai matansa makkah,shine ita Saude zata yiwa 'yarta bakin ciki Saude da har garinsu taje akan maganar auren da yakeso ya yiwa Amina bataso ita Aminar akan a hanasa aurawa Amina Mamuda amma da suka masa magana bai saurare su ba,sam ya ki hangen gaban da su suke masa hange

Haka yasa Mamuda ya kawo kudin aure shida makwabtansa suka ansa ba tare da wani dan uwansa ya sani ba,saboda yasan basu son auran

Amina da ita ma a bangarenta tunda aka kawo kudin hankalinta ba a kwance yake ba sam ba son Mamuda take ba zuciyarta tana gurin Habibu,

Mamuda ko yakan zo zance gurin Amina dukda Aminar bata wani sakin jiki tayi fira da shi saboda yadda zuciyarta bata garesa amma sam shi bai kawo bata san sa ganin yana da duk abinda za'aso shi danshi,kuma ma bai taba ji koda da wasa ba wani yace masa Aminar bata sonsa ba saboda shi soyayyar Aminar ta gama mamaye cikin zuciyarsa jinsa yake a lokacin indai bai aureta ba akwai matsala a rayuwarsa don shi Amina ce daga kallo daya da yayi mata a rayuwarsa yaji yana tsananin sonta fiye da kowacce mace,banda Hajara diyar Alhaji Audu ubangidansa da ya fara so 'yan uwansa suka yi masa auren gida da Hanne dukda bawai sonta yake ba haka ma Suwaiba matarsa ta biyu auren hadi aka musu da ita itama bawai sansu duk yake ba ya auresu

Sanda labarin auran da Mamuda ya zowa Hanne gaba daya kiyayyar duniya ta dorawa Amina tun kafin ma taganta haka ta tashi hankalinta ta kuma tashi namijinta, haka ta shiga bin bokaye da malamai akan maganar auren

Itako Suwaiba ko a jikinta dan ita dama tasan namiji mijin mace hudu ne,saidai dan kishin da taji dan kadan da baza'a rasa ba

*****
Anyi bikin Amina da Mamuda lafiya an gama lafiya Amina ta kasance mai hakuri da zabin mahaifin nata da Allah dama ya riga da ya kaddara auren basu,amma bawai da son ran Saude mahaifiyarta ba dama 'yan uwansu baki daya,haka bada son ran Hanne ba

*****
Amina shigarta gidan duk soyayyar duniya Mamuda ya dauketa ya dora mata,bangare guda ya gina mata a matsayinta na Amarya

"Wannan ya kara bata ran Hanne ganin duk shige da ficen da take da asarar dukiyarta da take duk a banza suke tafiya,Mamuda yanzu bama ta tasu yake,wannan ya kara hura wutar kiyayyar da Hanne take yiwa Aminar

Amma itako Amina tana ganin girman kishiyoyinta da 'ya'yansu sam batada mummunan manufa a ranta game da su

Shekara guda da ta zago da auren Amina da Mamuda ta haifi diyarta mace kyakkyawa mai kama da mahaifiyarta sak,tare da kishiyarta Amina ta haihu wato Suwaiba da ta haifi diyarta Malika
Safiyyya nada wata shida abubuwa suka fara sauyawa game da zaman Amina da mijin nata babu kwanciyar hankali, dama abokan zama duk ba shiri suke ba dan hatta Suwaiba Hanne ta fara zugeta akan Aminar,saidai ita Suwaiba tunanin da take baza ta ki Hanne da take 'yar uwarta ba tace zatayi shiri da bare da basu da alaka a tsakaninsu,gama halayyar Hannen da ta sani tuni inda ta fahimci shishshigin da take wa Aminar zata iya cewa akwai kullin da suke,ita ko Suwaiba macace mai gudun magana,wannan shine dalilan Suwaiba

Malam Basiru tun kafin aje ko ina ya fara dana Sanin aura wa Mamuda 'yarsa Amina don shi tunaninsa yana aurawa Mamuda 'yarsa shikenan sun samu hanyar samu gurin Mamudan,dukda a farko mamudan ya gwada hakan bayan bikinshi da Aminar abinci ake saukewa iyayen Aminar amma yanzu ko ko buhun gishiri basa samu

A yanzu haka Malam Basiru gani yake gwara Tijjani mijin Aliya akan Mamuda mijin Amina,saima da Aminar tazo gida bayan komawarta gidan mijinta bayan haihuwar ta da taje gida goyon ciki harta haihu yarinyar tayi wayau ,nan yana ganin Aminar yadda dukta rame daga komarwata gidan daga goyon cikin da tunda Aminar tazo Mamuda ke faman zarya gidan da naman kaji da lemuka amma daga komawarta duk ta rame nan iyayenta suka shiga tanbayar maike faruwa ba ta boye musu komaiba ta fada musu,tunda boyewar mai zatayi bayan ita dama Mamuda ba zabin ta bane,haka Malam Basiru da yasan shine silar auren 'yar tasa, nan ya fara rokon Aminar da mahaifiyarta yafiya
Saude tace"ai karshen kwadayinka ne dama yakai ka ya baroka gashinan tun kafin aje ko ina ga yadda ta dawo,kaje ka kai 'yarka cikin kishiyoyi kuma kowacce da 'ya'yanta bayan bata rasa ma rasa matar ba saboda son abin duniya ka manta ubangiji ke azurta bayinsa,amma idonka ya rufe tunaninka ai mijin Aminar shi zai a azurta mu ko ya azurta 'yarta mu,in banda zama babu kwanciyar hankali mai take yi"

Wannan abun da Mamuda yake yiwa 'yarsa ya yiwa Malam Basiru ciwo nan ya shiga neman Mamuda a kasuwa akan ya sakar masa 'yarsa amma Mamuda yace shi yana son matarsa ko ina zasu je bazai sake taba haka malam Basiru ya hakura
Aliya ma ta sake haihuwar diyarta mace Bilkisu sunan kakarsu Aliyar da ranar da Aliyar ta haihu aka saka
wa yarinyarta ta Bilkisu da aikowa da su Aliyar a lokacin da Aliyar ta haihu da kwana daya da rasuwar Bilki kakarsu Aliyar ta wajen uba wannan yasa Tijjani sakawa 'yarsa sunan kakar matar tasa Aliya
Wanda bayan haihuwar Aliyar Tijjani ganin sun fara tara 'ya'ya daga daya har suna biyu yanzu ga yanayin yanzu babu wani samun da suke a harkar ginin yasa ya yanke barin anan ya yanke shawarar zai dauki Aliya su koma Sokoto haka yadauketa zuwa sokoton da niyyar Tijjani da duk shekara zai kawo Aliya gida ta ga gida ba dan san ran mahaifan Aliyar da 'yan uwanta ba tabi mijin nata kuma gashi yace zai rika kawota gida wannan yasa shi jin dadi
Safiyya na da shekara biyar da haihuwa Amina ta sake haihuwar 'ya mace aka saka mata suna Hauwa'u wato ni da har nafi Safiya kama da mahaifiyarta mu Amina,a lokacin Saude mahaifiyar Amina ta haifi diyarta mace da ita Saude ta fidda rai da haihuwar ma a lokacin dan Haladu yayi shekara goma sha biyar sannan aka yi masa kanwar da taci suna Bilkisu aka sake maida sunan Kakarsu Aminar ga kanwarsu

Duk shekara sai su Malam Basiru sun zuba ido ko Aliya zata zo amma babu labarinta bana mijinta har tsawan shekara shida, duk wanda suka tanbaya a abokan Tijjani 'yan Sokoto idan sunje gida maiyasamu Tijjani har aka dauki wannan lokacin bai kawon Aliyar Kaduna ba amsarsu itace aisu Tijjani basu koma Kaduna ba wanda a wannan lokacin ne kuma Allah ya karbi ran Malam Basiru 'yan uwa da abokan arziki sunji mutuwarsa Amina da Mahaifiyar Saude da Haladu har sunfi kowa jin mutuwar Malam Basiru Bilkisu kuwa tana goye a lokacin batasan mahaifin nata ya rasu ba

Naji korafin page din danake muku nasan nima yana gajere amma kunsan yanayin rayuwa saboda karna rika barinku shiru yasa nake kokarin turo muku kullum ammah zan rika tsallaken rana indai kunaso sau uku a sati zan rika yi muku amma pages da yawa indai kun amince shikenan.
Nagode da yadda kuke nuna soyayyar littafin nan
Chapter 57 · 0% Book details