← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 57

Sashe 4

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_A ranar ukun ne yan uwa da abokan arziki suka zowa Hajiya Jamila gaisuwa daga mahaifarta Nasarawa Lafiya ciki ko harda Ruqayya da a ganinta tafi kowa jin mutuwar AbdulAhad sunzo da niyyar suyi kwana daya su juya dalili mai 'karfi da yakarasa su Kaltume da Haulatu jin haushin tafiyar tasu su da sukaso suyi fira da 'yan uwansu yau amma ga yadda Abba yace banda suna ganin girman Abba da bazasu tafi ba,sai dai matsayin da yake a gurinsu na mahaifi da tunda iyayensu suka rasu suka dawo hannunsa harya aurar dasu bazasu iya ja da maganarsa saboda koba wannan Abba Bukar ba kalar wanda za'ayiwa wargi bane da haka kowacce ta hada kayanta tabi mijinta nata_

_*Abangaren Rufaida*_

_Nasihar da Abbanta Aliyu yake mata sosai take shigarta hawaye take zubarwa daga idanunta dake cikin hijabi,inda shi bai lura ba,dukda shi a karan kansa nasihar yake amma tausayin 'yarsa yana mamaye a zuciyarsa haka ya mike daga 'daya daga cikin kujerun falon 'dakin dasu Rufaidan suke ciki tundaga mutuwar yana yi mata sallama da kyar batare da ta dago kaiba ta iya ma Abbannata addu'a wadda nasihar Abbannata jinta kawai take bata fahimtar komai dan yau mutuwar sabuwa tadawo mata fil gashi yanzu haka kowa watsewa zaiyi a barta cikin tsangwamar da tasan zata riska gurin surikarta akan abinda ba tada masaniya,Da haka Umminta Hauwa'u da Momynta Hajiya Maryam suka fito daga Bedroom din falon da jakunkunasu a hannu kowaccensu fuska babu walwala dasu ma tafiyar zasuyi nan Hajiya Maryam ta kama hannun Rufaida ta 'dago fuskarta ta fara kokarin share mata hawaye kafin tayi mata nasihar itama da haka suka fice suna yi mata Sallama saboda shi kansa Aliyu su yake jira su kama hanyar Kano kodan su isa koda da la'asar ne da haka su Luba da Gwaggo suka fito yi musu rakiya da itama Luba anjima zasu tafi itada Kabir bandama yaje gurin wani abokinsa inda ya tafi da Yasir da Yusuf toda tuni ma sunkusa Abuja Gwaggo kuwa da take a gari sai magriba Abdulmalik zai maida ita gida dukda yadda Abba Bukar yaso Gwaggo ta zauna har Rufaida tafita takaba amma kiri kiri taki amincewa sai dai ta rika zuwa akai akai duba ta_

_Karfe tara na dare gaba daya dakin yayi shiru daga ita Rufaida sai Yasir da yagama rigima yayi barci saiko karar sunnah TV da take sauraron wa'azi saiko wayarta dake gefe da sai yau Luba ta bata da ta kira su Umminta da Momynta Hajiya Maryam sun sauka lafiya nan ummin nata Hauwa'u ta dora da yimata nasiha Luba ma ta kira ta sunje gida lafiya sai kuma kiran kawaye da abokan arziki da 'yan uwa da sukaji mutuwar basu sami damar zuwa ba da take amsawa ganin Number 'din Samiha a screen 'din wayar da take ta gwada number 'din Rufaida tun bayan gaisuwar da tamata a wayar momynsu Maryam da bawani damar yi mata ta'aziyya tasamu ba,sai yau da number din ta kira ta samu ta shiga, ita kanta Samiha taji mutuwar kamar itace mijinta ya rasu dan yadda ta dauki Rufaida a zuciyarta ba abin akwatanta bane badan busu jima da komawaba da saita zo yi mata gaisuwa,da haka Rufaida ta 'daga wayar da muryarta me cike da rauni tayi sallama da kadan ya rage tayi kuka Samiharce ta amsa ta kuma kara yi mata ta'aziyya da cewa "Rufaida Wanda duk ya mutu baya dawowa yanzu Yaya Ahad addu'arki tafi bu'kata damuwa bata maye gurbin komai sai sawa zuciya ciwo domin duk abinda ka rasa bazai dawo ba addu'a itace mafita akan komai" da haka ta cigaba da bata hakuri sosai Rufaida taji da'din wayar tasu tana cewa"nagode Samiha kuma insha Allah zai dauki shawararki yasu Little din da Rufaida karama" cikin farin ciki Samiha tace"duk suna lafiya Ahmad yace yana miki gaisuwa da mundawo gida zamu zo gaisuwa shima yaji mutuwar yace gaisuwar waya ba zata wadatar ba sai anzo har gida"Rufaida ta har ranta taji dadi tace"koma ta hakane tayi ai ina Yaya Ahmad 'din"Samiha tace aiko ba tayi ba ,Yana gurin aikinsu yanacan yauma yana cuku cuku samun takaddar da za'a bashi yadawo gida"Rufaida tace"yanzu bazai hakura ba ai duk dayane nanda shekara biyun da suka cemasa"Samiha tace "wanne duk 'dayane bayan bama ganinku a kusa damu ai bawani cikakken farin ciki ba ahalinka a tare dakai anyi nisan daya wuce na ahau mota sai dai jirgi mai saukar ungulu" da haka suka cigaba da ta'ba hira wadda yasa Rufaida jin da'di dan har ranta matsayin data dau Samiha ya wuce tunanin mai tunani haka sukayi sallama kowannensu a cikin farin ciki_

_koda ta sauke wayar tunani ta cigaba dayi irin yadda rayuwarta takasance kalubalen data riska har kawo yanzu da wannan tunanin barci ya dauke ta_

_'Bangaren Hajiya Jamila_
_Aunty Shema'u da take yaya ga Hajiya Jamila ta dubi Hajiya Jamilar da sauran mutanan 'dakin tana cewa"Wai ita yarinyar nan Rufaida bazata zo gaishemu bane har takwas ta gota komu take nufi zamu je gaisheta yarinya tasamu guru said wulakanci"Hajiya Jamila tace " naga alamar hakan take nufi" nan sauran 'yan uwan Hajiya Jamila suka samu kofar cigaba da magana Mara dadi akan Rufaida dukdai akan dalilinsu nacewa batazo gaishesu da safe ba Aunty Maimuna kanwar Hajiya Jamila ita tasa baki cikin maganar tace" Aunty ai kamata ayi mata uzuri amatsayinta name takaba bakuma asan dalilin nata nakin zuwa ba tunda tasaba zuwa koda banwai Sani ba"wa'danda da suka fara korafin cewa bata zo dinba sai duk suka fara cewa hakane yakamata suje dubata Idan sungama shirin tafiya da sukeyi Aunty Shema'u ta 'dan ta'be baki suka canza fira_

_Hajiya Kubra ta dubi Aunty Amina amaryar Abba Bukar da suke kitchen suna kacaniyar girki su da wata mai tayasu aikace aikace tace" Amarya niko yau banji motsin yarinyar nan Rufaida ba"tace " nifa kinsan bana shiga harkar da baruwana saboda ina tsoron najawa kaina rigima gurin Hajiya Jamila gwara ke manyan 'ya'ya gareki nifa"Murmushi Hajiya Kubra tayi tace"Amarya rufamin asiri yanzu Hassan ya sake Kodan yatsa ya 'daga wa Hajiya Jamila basai ankoremu nidashi a gidanba kinsan Abba bazai 'dau irin wannan ba,Kawai dai gani nayi 'dana kowa ne kuma mahaifiyar yarinyar nan tana ganin girmanmu kuma nidai tunda nike bazance ga abinda sukayi mana ba yakamata muma mukula da ita tunda yanzu ita abar tausayice"Aunty Amina tace " toda wannan amma dai ina tsoron wannan yare yaren" murmushi Hajiya Kubra tayi tace" ashe dama tsoro kawai kikeji ni kinga bari naje dubota" "to sai kindawo" kawai Amarya ta fa'da ta cigaba da aikinta"_

Shiga Hajiya Kubra tayi dakin tana sallama sai dai bataji motsin mutum a falon ba yasata karasa shiga bedroom din a takure jikin gado ta iske Rufaida tana rawar sanyi gefe kuma Yasir ne dayaketa barcinsa babu abinda ke damunsa"Hajiya Kubra tace Subhanallah Rufaida meke damunki"cikin rawar murya tace"Mama zazza'bi nakeji da ciwan kai"Hajiya Kubra tace" amma baki fada ba" tace" yanzu nafara jin zazzabin" Hajiya Kubra tace "hala bakicin abinci haba Rufaida mutuwa fa dole ce Wanda mutu bazai dawoba kuma ke bakaramar yarinya bace da za'atasa ki kici abinci ko aduramiki,bari nakira Hassan idan mota tana hannunsa akaiki asibiti" waya ta 'daga da take hannunta ta lalubo Number Hassan ringing biyu ya 'daga tanbayarsa tayi kana inane yanzu nan yake shaidamata yana bangarensu ko abinci aka gama su fito ci tace a'a Rufaidah ce balafiya ta dauka mota tana hannunsa yace tana hannun Yaya Abdulmalik Abba ya aikesa nan yace Allah ya kara sauki Hajiya Kubra tace Amin ta katse wayar shima Hassan wayar ya aje yana kara tausayin 'yar uwarsa dama haka mace take komawa idan mijinta yarasu lokaci guda Rufaida ta rasa duk walwalarta shi dama za'a bashi ita ba abinda zai hanasa aurenta Koran su rike yaran nan cikin kulawa bazai fahimci yayi rashi ba"
Hajiya Kubra AbdulMalik ta kira ganin bai dagaba yasa ta fahimci tuki yake Abba Bukar takira tasanarmasa nan yace bari yashigo dakin ya gaisheta gefen Gado Hajiya Kubra ta zauna ba jimawa ya shigo ya dubata yace idan Abdulmalik yadawo zasu tafi asibiti Yakuma umarci Hajiya Kubra tadauki yasir ayi masa wanka da haka suka bar dakin suna karamata Allah ya kara sauki bayan mikawa yara Yasir ta nufi bangaren Abba Bukar da sallama Hajiya Kubra ta shiga Abba Bukar yadubeta bayan amsa sallama inda tanemi guru gefen gado ta zauna shida yake tsaye jikin Sib yana duba wata takadda da yake nema duk ma'adanar litattafansa yaduba batanan ya dubi Hajiya Kubra da mamaki ganin cewa sun gaisa kuma yanzu suka rabu baidai cemata komaiba yanaso yaji ta bakinta takunna shirun sakanni sukayi kafin Hajiya Kubra tace"Abba dama shawara nakeso na baka amma karkace na Shiga abinda baruwana koya batama rai"murrmushi Abba Bukar yayi yace"Haba Kubra kifadi koma menene bazai batamin rai ba kuma indai dayuyuwa zan dauki shawarar taki" nisawa tayi kafin tace" gani nake gwara yarinyar nan Rufaida takoma gidan Gwaggo zatafi kula da ita amma nan kasan akwai damuwa azamannata saboda kowannenmu bazai kula da ita kamar Gwaggo"Abba bukar ya nisa yace"hakane saidai zaman nata anan zaifi saboda nanne yakamata ta zauna bayan gidan mijinta tunda idan Abujar ne babu wanda tasani kuma nanma koba ta auri danmu ba ai gidansu ne,Kubra daga gareki bana tunanin wata baraka zata taso Dan Allah kirike ta amana har Allah yasa tagama takabar nan takoma gaban iyayenta tunda yar nan kema yar kice kuma da na kowane bakasan wazai taimakeka ba a gaba"Hakane cewar Hajiya Kubra da haka dai suka cigaba da fira Abba Bukar nakarajin kaunar matarsa saboda yadda tafita daban acikinsu badan wata alaqa tasu ba yasa yake kaunartasu ba a'a halayyarta itace dalilinsa babu Wanda cikin nasa zaice ga laifin ta bawai don tasu bace yasa hakanba kawaidai ita bamai son kai bace yana alfahari da matarsa.*JININMU 'DAYA*

By Sadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khali)

4
Chapter 4 · 0% Book details