← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 57

Sashe 13

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sallamar Samir shi ya dawo dasu Rufaida daga cin abincin ranar da suke tare suka amsa gaba 'dayansu Samir ya gaisheda dasu Ummi Hauwa'u da Abba ALIYU sauran yaran suka gaishesa ya amsa yana murmushi Rufaida da bayan gaisuwar tace "lah yaya Samir yau Kaine a tafe a gidanmu hala makuwa kayi" AbdurRashid yace"Nima "yaya Rufaida na dauka makuwa yayi" Samir ya harari AbdurRashid yacewa Rufaida "ke dai bari Rufaida wannan yarinyar ce tasa saurayinta yazo gidanmu kuma tasan ba'anan take weekend" Abba Aliyu da Ummi Hauwa'u suka ce ai dama munsan ba'a aikin banza a kano banda haka yaushe rabon duniya da ayyaraye"Samir yace "wallahi bahaka bane Abba bahaka bane mutumin nawane AbdurRafi shima baya zuwa inda nake tunda aka samu hutu"AbdurRafi yace" kai Samir kaji tsoron Allah zuwa na nawa nayi gidanku"Ummi Hauwa'u tace kanku dai akeji"ta dora da cewa"AbdurRashid jama yayan naka kujera mana ya zauna yaci abinci shima Samir ya zauna yana cewa" Yawwa AbdurRashid"ya dora da cewa Ummi kamar kinsan banci abinci ba Ahmad yazo Momy tace nataso na rakosa gurin Samiha kinganni ma Ummi bako waya bare key din mota a hannu na sai dai idan mutumin nawa zai kaini gida ya fada yana kallon AbdurRafi da yagama yiwa karya"ganin baice komaiba yafara lomar abincinsa da Ummi ta zuba masa,Abba Aliyu yace "Hauwa'u baki tanbayesa ya budema bakon falon baki"Samir yace "Eh Abba na budemasa" Abba Aliyu yace "yawwa Samir ,Hauwa'u azuba ruwa da lemo akaimasa" Ummi Hauwa'u tace to, da haka Abba Aliyu ya cigaba dacin abincinsa"Samiha da take zaune tana ji duk abinda suke fada bata sa baki ba da tunda aka ce mata Ahmad yazo take cin abinci hankalinta raba da rabi ta qagara Abba ya mike taje taga sahibin ran nata,Jin maganar Ummi yasata tsaida tunanin nata da Ummin ke cewa
"Ya haka Samiha ko bakyacine kin koshi kiyi maza ki gama kinga yaron ke yake jira"AbdurRashid yace" Ummi ai dole ma ta koshi ta ci fa 'dazu bandana Yaya Samiha ci gare ta"Ummi tace"AbdurRashid bafa nasan raini kaike kawo abincinne" ya girgiza kai AbdrRafi jin haka yasa sh tuno abinda tayi masa dazu yasa shi cewa"wallahi Ummi Ba Karya AbdurRashid yake ba kifadawa Abba ya karo buhun shinkafa"Ummi ta gallawa AbdurRafi harara,Samiha jin hakan yasata hade rai ta mike ta fara barin falon ta haye sama"Yara ne sukayi dariya Rufaida tace"wa yaran dama kofar guduwa take nema Abba Aliyu da ya gama cin abincinsa ya mike ya bar falon a ransa yana kara jin san iyalensa,da kuma matarsa Hauwa'u ha'ki'ka yayi dacen samun mace tagari, Ummi ta shige kitchen ta shirya kayan da za'a kaiwa Ahmad falon baki ta kira AbdurRashid ya mikamasa Rufaida upstairs saman bene tabi Samiha dakinsu ta tura ta shiga da sallamarta inda ta sami Samiha tanata cacca'ba kwalliya kai kace gidan biki zata"Rufaida tace "Samiha wannan kwalliyar fa harkinyi wankane kinsan dazu fa baki yi ba"
Hararar Rufaida tayi tace"waike Rufaida ni kwado ce kamarki zantayin wanka ina laifi nayi daya tunda nayi da zan tafi makaranta ai ya isa"
Murmushi Rufaida tayi daga bisani tace mata"ai wanka jindadin jiki ne,kuma ai kinsan fa munshawo rana a makaranta,kyaeje gabansa kita warin rana"
Tace"ke ni banshawo wata rana ba,inma nasha haka zan fita,tunda turare yana magani ai"
Rufaida tace "nufinki turare na zan baki ki fesa kin da'de wallahi"
Samiha tace"kwantar da hankalinki nima inada turaren ai"jakar makarantarta dake kan lokar gado Samiha ta zage ta de'bi turare ta feshe jikinta dashi ta bude Sib ta samo mayafi mai girma kalar kayan jikinta ta yafa"
Rufaida da take tsaye tana kallonta Samiha ta kalleta tana bu'de kofa ta kashe mata ido tace"aini ba'ayimin gatse"Rufaida tace" naji kimaza ki tafi kinsan ajan aji ake barin arha,kuma wannan kashe idon ai Yaya Ahmad zaki yiwa"Samiha tace "kuma fa hakane,bari na wuce na tafi said kinzo gaisheshi ko?" Rufaida tace"bafa zanzo ba kigama fa'damin magana"Samiha ta dawo ta dafa Rufaida tace"haba kawata Yar uwata ki taimaka kizo"ganin Samiha zata cigaba da 'batawa kanta lokaci tace"zata zo su gaisa"da haka Samiha ta fice ganin Abba a cikin falon suna hira dasu Samir yasata dan jin kunya ta koma da baya ta tabi ta kitchen zata fita tanan ta wuce Abba Aliyu da idonsa na gun Samihan yayi dariya inda ya tuno halayyar matarsa Hauwa'u tana kama data Samihan amma azamanin baya tunkafin aurensu can yake tunowa sai gashi Rufaida gudan jininta bata biyo cakwakkwayyar Hauwa'unba sai Samiha da babu dangataka ta kusa kota nesa tsakaninsu,Dariyar da Samir keyi ita tadawo da Abba Aliyu daga wancen tunanin nasa"Abba Aliyu ya dubi Samir yace "lafiyarka kuwa Samir" yace "Abba lafiya ta kalau,Samiha ce data ganmu a falo taki wucewa tabi ta kitchen zata wuce tayi arangama da Ummi " murmushi Abba Aliyu yayi yace"kasan yaran suna da kunya duk cakwaikwaiwar Samiha tana da kunya diyartawa"Samir da baice komaiba Dan ya fahimci Abba baisan rashin kunyar da Samiha keyi a gidansu ba akan Ahmad"Abba Aliyu ya tsaida shirun nasa da cewa"Muna magana da Abbanku da muka hadu shekaran jiya yace min yaron ya turo magabantasa to bamu gama maganar ba aka kirani a waya....."Samir yace"Eh wallahi Abba yazo tsaida rana za'ayi Abba yayi bincike akansa baida Matsala babansa shine sabon Commissioner of police a Zariya Road suke da zama"Abba Aliyu da yaji dadin Labarin kamar akan 'diyarsa ya faru ,danshi dama yadda yakeson Rufaida haka yakejin Samiha har aransa baiji bakin ciki ko kyashin wannan labarinba,yace cikin murmushi mai yalwa a fuskarsa"To Masha Allah,ai kaga idan AbdurRafi zai ya tashi tafiya police (Dan sanda)ai bazamusha wuya ba muna da hanya"AbdurRafi da sai yanzu yasa baki yace"Abba yanzu kaima har dakai a tonan nawa" Samir ya kunshe dariyarsa"Abba Aliyu yace"ai kaine Rafi abu ka'dan kace bakaso har kannenka sun ganoka tsokanarka suke da abunda bakaso,kana girma kana kara rashiin wayau"AbdurRafi yace "ni dai Abba Dan Allah a bar maganar ,kai kuma da kake kunshe dariya ka tafi mana kai ga hanya nan" yacewa Samir,Samir,yace"Allah ya huci zuciyar manya musu tsoron training din 'yan sanda"daganan Samir ya gudu ya bar falon yana dariya dan yasan halin abokinsa sarai indai kan ace ya tafi police ne zaku iya yin baran baran,can majalissar unguwa Samir ya shige kasancewar yasan 'yan unguwar wasu saboda akwai abokan karatunsu acan nan ya zauna suna taba fira"AbdurRafi shima binsa yayi yana tunano rashin mutunci da zaiwa Samir saboda yadda ya rainasa dan kawai yace bayason dan sanda saboda training dinsu yanada wuya shiko riqe wannan bindigar aka barshi da shi ai anbarsa da aiki,Abba Aliyu yayi murmushi AbdurRafi da Samir fadansu sai su ba'a shiga koma ka shiga sabaka kunya ya cigaba da kallon da yake a TV
Rufaida ko Samiha bata jima da fita ba tasa hijabi mai girma tabi Samiha su gaisa da Ahmad a falon ba'ki ta samesu ta gabatar da sallama suka amsa mata ta shiga" ta zauna kusa da 'kawartata Samiha da take a kujera mai biyu shikuma yana zaune a kujera mai 'daya an ajemasa lemuka a plat da ruwa datasan duk aikin Umminsu ne inda Samiha ta tsiyaya ruwa a kofi Rufaida tace"Yaya Ahmad ina yini"ya 'danyi murmushi yace"lafiya kalau Hussaina,ya juma'ar?"
Tace masa" Alhamdulillah Yaya,wato bazaka daina cemin Hussaina ba"wanda tun farkon gaisawarsu da Rufaida da taje gidansu Samiha yace ita Hussainar Samiha ce saboda yadda take basa Labarin Rufaida kona Yaya Saudat bata basa haka,dan shi 'daukarsa suna da ala'ka ma,danshi har kama yaga sunayi,"yace mata "Eh mana ai Ku 'yan biyu ne idan akaga wata za'aga Zahra gashima kuna kama ma inda za'a kara tabbatarwama" ya fadi hakan da sigar zolaya"Rufaida tayi murmushi tace"Samiha kinji fa yaya Ahmad da wani zance"Samiha tace"kema dai kya fa'da nibanga wata kamarmu ba ko 'daya"Ahmad da har yanzu bai fahimci alakarsu ba yace"dama haka zakuce"Rufaida tayi murmushi tace" Ai hakane ma"da haka suka sake ta'ba hira ka'dan sannan Rufaida ta fice daga falon ta basu guri suyi firarsu.*JININMU DA'YA♦️*

Sadiya Khaliy💞

Page 13
Samiha ta shigo 'dakin ko sallama babu ta fada gado tareda cire mayafin kanta Rufaida tace" ke lafiya kuwa"Samiha tace"bansaniba wallahi Rufaida Ahmad ya cuceni"Rufaida ta jinjina kai tace mai kuma yayi miki bawan Allah"Samiha ta ta'be baki tace"kinsan tun kwanaki da yacemin zai turo a tsaida magana asa rana"nace masa ya bari keda Yaya Saudat kuma Ku samu miji tukun"ita da Rufaida abinda dariya ya bata ma,Samiha tace"au dariya ma kike ko"Rufaida tace"Ai abin nakine abin dariya banda abinki mainene dan ankawo kudinki muba'a kawo mana ba,kinsan komaifa lokaci ne,kafin ayi naki bikin sai kiga munsamu namu mazajenmu,"da haka dai Samiha tasamu kan Samiha dan ita Samiha dagaske bata yarda ba sai sun samu nasamu mazajen Ahmad ya jira saboda ayi bikin nasu tare
Chapter 13 · 0% Book details