← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 133

Sashe 95

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Irin kalamin da ka furta a lokacin da na ke cikin gidanka da cikin yayanka? Irin zuwan da iyayena suka yi ka wulakanta su? Yata ba zata je ko'ina ba Haruna.... Ban amince da wannan auren ba...”

Hajiya Binta ta ce.

“Adai hakuri Iyami a daina tuna baya, a bar baya ta wuce”

“Haka ne Hajiya, da dan yaran nan ba da be isa ya shigo cikin gidan nan ya zauna a nan yana magana da ni ba”

Appa ya share hawayen da suke masa zuba.

“Na cancanci tozarci da wulakanci da rashin mutunci a gurinki Iyami, ban kyauta ba na sani, kuma na karbi hakan”

Ya kalli Hurriya dake amayar da ruwan hawaye ya ce.

“Ba zaki ce komai ba Hurriya? Wata kila ban kyauta miki ba, domin ban tsaya na ji ra'ayinki ba”

Hurriya ta mika hannayenta ta kama hannayen mahaifinta ta rike.

“Hakika kai uba ne na gari Appa, ba zaka aurar da ni a inda kake tunanin zan wahala ba, ba zaka aurar da ni a inda za a musguna min ba, ko da ban gani a aikace ba na san a cikin zuciyarka haka ne, Appa ko kare ka aura min a matsayin miji, Wallahi zan karbe shi na zauna da shi, balle kuma mutumen da kake kyautatawa zato, na gode da zabin da ka yi min. Ya Allah mahaifina na ciyar da ni da halak, Allah ka ciyar da shi da abinci da ya fi ko wane abinci dadi a aljanna, mahaifina ya shayar da ni da halak, Ya Allah ka shayar da shi da ruwan alkausara, ruwan da bayan su babu sauran ƙishi bayan shansu, Mahaifina ya tufatar da ni da ni da Halak, Ya Allah ya tufatar da shi da mafi kololuwar darajar tufafi a aljanna, Mahaifina ya sama min muhalli, Ya Allah ka yi masa muhalli kusa da Annabi Muhammad S A W, Ya Allah ka shaida a yau mahaifina ya sauke nauyi na zaba min mutumen da yake ganin ya dace da ni, Ya Allah ka sauke masa nauyin zunubai, a saka a aljanna a saukake”

“Ameen, Allah ya miki albarka Hurriya”

Appa ya amsa yana kuka, sannan ya kalli Amma ya ce.

“Iyami na gode da kika haifa min ƴa mai tarbiya da sanin ya kamata a kananan shekarunta, wannan ma kadai abun alfahari ne a gurin, ku yafe min a inda na yi ba daidai ba, na barku lafiya”

Ya mike tsaye ya saka talkaminsa ya nufi kofar fita daga tsakar gidan, sai ga yaransa yan tawaye sun shigo sanye da uniform din makaranta rike da lunch box, suna ganinsa sai suka yi gurinsa suna murna kamar sun saba da shi.

“Appa...Appa.... Appa...”

Durkusawa yayi yana shafa kansu a madadin ya amsa sai ya fashe da kuka kamar ba shi ba. Yasir mai ya sauke kansa kasa yana hawaye, Gwaggo ma hawayen take ita da Hindu, Rukayya kuma ta koma kusa da Hurriya ta zauna ta rungume suna kuka. Cikin karfin hali Appa ya mike tsaye ya kama hannun yaransa ya fice daga gidan, Yasir ya share hawayensa ya kalli Amma.

“Amma...”

Sai ta daga mishi hannu tana hawaye.

“Dan Allah tashi ka bi mahaifinka”

Ya mike tsaye ya kalli kakarsa.

“Hajiya tashi mu tafi”

Hajiya ta yi murmushi.

“Zan tafi Iyami amman zan dawo idan kin huce”

Sannan ta mike tsaye suka fice tare da Yasir. Amma ta share hawayenta ta kalli Hurriya dake kuka ta ce.

“Shikenan abun da zaki fadawa mahaifinki? Kin goyi bayan auren da yayi miki? Kin san wacece Nafisa, kin kuwa san irin zabin da Alhaji yayi miki?”

Hurriya ta dago daga jikin Rukayya ta ce.

“Amma, mata da yawa iri na ba su san ubansu ba, saboda uban ya mutu a lokacin da suke ciki ko suke da kurciya, da yawa iyayensu ba su ga ranar aurensu ba saboda mutuwa ta yi katanga, suna da yawa wadanda iyayensu ba su samu damar zaba musu miji ba, wasu kuma an fasa aurensu, saboda ba a san ubansu.... Shim ni a gareni, wannan na gata ba ne?”

Amma ta kasa amsawa. Cikin kuka Hurriya ta cigaba.

“Amma..., baka sanin muhimmanci uba sai ranar da ka rasa shi, uba yana da ƙima, shi uban bango ne majingina ko wace ƴa. Idan kana son ka san darajar uba tambaye maraya, idan kana son sanin tsadar uba da halin da ƴa mace take shiga idan bata da shi, tambayi Ƴar da aka haifa ta hanyar zina...”

Ta saka hannunta tana share hawayen da suka ki tsaya mata

“Ni dai kam na sani, dukan abun da zai zo daga gurin Ubangijina mai kyau ne, dan haka zan tara hannu biyu na karba, ko da ba zai min dadi a yanzu ba, zai zama daraja ce da nasara a gaba, shi dan'adam ba ya kauce kaddara, kaddara bata wuce bawa, wannan ma daga gurin Allah ne....”

Amma ta girgiza kai tana kuka.

“Aa Hurriya ban yarda da wannan auren ba, ba zaki je ki sha wahalar da na sha a gidan ubanki ba, na yi irin wannan wautar na ki a lokacin da nake da kurciya kamar ke, amman yanzu me ya haifar min?”

“Nasara....”

Gwaggo ta amsa mata a tsawace.

“Nasara ya haifar miki Iyami, haihuwar da kika da Alhaji Haruna nasara ce..! Zaman auren da kika yi a gidansa nasara ce...! Samun soyayyarsa da ta mahaifiyarsa nasara ce....! Abun da kuma ya same ki yanzu jarabawa ce ni ma na gane...”

Amma ta runtse ido ta jingina da bangon gidan.

“Abun da ya gudana a yau din nan ma Nasara ce Gwaggo...”

Cewar Hindu tana murmushi. Gwaggo bata sake cewa komai ba ta mike tsaye ta shige falonta, Hindu kuma ta dafa kafadar Amma tana bata magana, Rukkaya ta kama Hurriya ta kwantar da ita a jikinta.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/18/2023, 2:14 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

4️⃣4️⃣

Da farinciki Appa ya shiga dakin Momy ya nufo inda take zaune fuskarsa da annuri ya zauna gefen gado. Da mamaki yake kallonsa daman kam mamakin kiran da Daddy yayi mata ya karbi sarka be gama fita mata ba.

“Alhamdulillahi”

“Allah abun godiya”

Ta amsa sannan ta kalli goro da dabinon da ya shigo da su gabanta na faduwa.

“So da yawa kanyi abu basan alherinsa ba sai a gaba, wani abun kuma Allah ya barwa kansa sani, ban tana jin farinciki da alfahari da aurenki ba sai yau, Allah ua miki albarka Nafisa sanadinki yau na fita bakinciki an shafe min duk wata damuwa da nake jinta a raina saboda faruwar abubuwan nan”

Momy ta yi murmushin rashin gamsuwa.

“Daman ai Yaya akwai karanci, wani abun yayi maka ko?”

“Ďanki Jamal kuma dansa ya nemawa auren Hurriya, kuma be bar gidan nan ba sai da aka daura auren”

Momy ta kyalkyale da dariya har da daga kafa sama da buga a kasa.

“Yau kuma ni ake yi ma zolaya, taya za'ayi daurin aure a cikin gida ba mu sani ba kuma daga kai sai yan tairarun mutane? Kila dai aurenka ne za a daura ko kake min kwano kwano”

Appa yayi murmushi mai kyau.

“Shi aure ai ba dole sai an tara mutane ba, amman amsu aikin gidan nan da yayanta Yasir sun shaidin auren Hurriya aka daura da Jamal a yau, kuma yayanki ya bada Zinari a matsayin sadaki”

Ya aje mata goro da dabino na daurin auren a gadonta.

“Kin ga goro da dabino nan!”

Ta kalli goron da dabino har lokacin dariya take domin maganar Appa ba magana ce mai kama kai ba, sai dai kume? Appa ba zai mata wasa ba, ba zai ce anyi ba alhalin ba ayi ba. A take dariyar ta bace mata bat ta daga kai ta kalli Appa.

“Da gaske Alhaji? Yayana ya zo gidan nan ya nemawa Captain auren Hurriya?”

“Har an daura, yace ba zai iya da rigimarki ba, dan haka ya wuce yace ni na sanar miki....”

Momy ta mike tsaye wayar dake cinyarta ta fadi kasa.

“Aure Alhaji? Auren Hurriya aka daura da Captain?”

“Kwarai, kowa ya ji zai yi mamaki, kuma tabbas Alhaji Turaki ya kai mutumen kirki har ya wuce, ya yaye min bakinciki kuma na yarda zai rike yata da amana”

Momy ta dafe zuciyarta.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
La'ilaha Illallahu Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam”

Appa ya bita da kallon al'ajabi ganin yadda ta yi kamar wadda aka fadawa mugun abu.

“Yanzu duk matan duniyar nan Captain ya rasa wa zai aura sai Hurriya? Yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicinta? Yarinyar da ko ido bata shi a yanzu? Anya Captain yana cikin hayyacinsa?”

“Ita Hurriya ba mace ba ce? Da kike fadar ya rasa wa zai aura sai ita? Wane irin magana kike haka ne Nafisa?”
Chapter 95 · 0% Book details