← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 133

Sashe 12

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa masa da kai sannan ta nufi gadon ta kwanta shi kuma ta tashi ya fice, kai tsaye bangaren mahaifinsa ya nufa sai dai yayi rashin sa'a be tararda shi ba, domin tuni ya fita after ya kai Hurriya bangaren Momy daman ita kawai yake jiran a dawo da ita gidan ya fita, saboda Hajiya Kaltume ta fada masa idan be yi da gaske ba Amma ba zata ba shi Hurriya ba.
Hurriya bata tabbatar da mahaifinta ya daina yayinta ba sai da ya canja mata makaranta ya saka ta makarantar government, yayinda sauran yan'uwanta da suke ajin karshen a private school suke can suna karatu. Ita kuma aka bata direba daya da zai rika kaita makaranta yana daukota ita kadai, ba karama ta kaddama aka yi ba kamin Appa ya saka ta government school, domin malaman dake karantar da ita a private school suna sonta sosai saboda kokarin da take da shi, ga kuma gasar da suke ta shirye shiryen turata. Har komiti suka hada na manyan makarantar suka zo har gida suka tarardar Appa suka tattauna da shi tare da nuna masa illar cire Hurriya a makarantar amman ya ki saurarensu saboda Hajiya Kaltume ta ba shi shawarar kaita makarantar Government, daga karshe ma sai suka rabu cikin rashin dadin rai domin Appa rufe su yayi da fada ya nuna musu Hurriya yarsa ce shi ke da iko da ita babu wanda ya isa ya fada masa me zai yi akan yarsa hukuncin da ya yanke ke nan kuma babu fashi.
Ta bangaren Hurriya ma hakan ya taba ta sosai domin yin sabin abokai da kuma canja wasu abubuwa na karantu domin malaman ba daya ba be ya zama abu ne marar sauki a gareta, hakan sai ya saka ta zama weak ta yadda bata iya maida hankali ta yi karatun yadda ya dace, gaba daya ta koma kamar ba ita ba, karatun da take ganewa a can bata ganewa yanzu, sai ayi darasi a gama bata fahimci komai ba, tunani da damuwa suka taru suka yi mata yawa, gashi kullum ita ce cikin kebe kanta bata son shiga cikin yan makarantar da bata saba da su ba.

**** **** ****

Hindu ta mika mata jaririn dake kuka.

“Iyami ina ta fada miki banza bata fitar da ke gidan Alhaji, amman kika sa kafa kika yi biris da maganata, yanzu gashin bayan fitar da ke ta dauke hankalinsa daga kan Yayansa, bayan an a kashe miki daya, kuma han karbe dan abun da yake hannunki, ina dadi ka haihu gari daya da miji amma yaki ya tako ya duba yara, ke da da ns yadda Alhaji yake sonki ai kin Allah kadai ya san yadda zai rika dauki yana hauka kin haifa masa yaya biyu kuma maza”

Amma ta Hamid dinta dake shan nono ta ce.

“Hindu ban saba irin abubuwa nan ba, ni Wallahi ban san kowa mai irin wannan aikin ba, kuma ni ina tsoron kauce hanya”

“Babu zancen kauce hanya, ai ba shirka zamu yi ba, kuma ba cewa zamu yi ayi mana na Sherri ba, aa mu dai kawai a karya sihirin da ta yi miki da na yayanki hankalin mijinki ya dawo ki koma gidansa ki rike yayanki, domin nan gaba kadan ma zai iya cewa su ma wadannan karbe su zai yi, tun kina cikin idda na so a nemi taimakon nan kika ki gashi yanzu har sai an sake daura aure”

“Hindu da dai mun hakura, komai fa yana da iyaka wata rana zai karye ko da ba ayi komai ba indai asiri ne.”

“Toh shi ke nan zauna a gurin, kina sakawa zuciyarki bakinciki ki lalace a banza ki zama bar tausayi daman haka suke so, yar ki kuma ta koma yar aikin gidan, idan ma ta yi sa'a kenan ita ma ba su kashe ta ba, nan gaba kadan idan ta girma ki rasa wa zai aureta, domin Wallahi ba zata yarda Hurriya ta yi aure ba ga nata yayan ko da kuwa sun yi aure, yanzu kina kallon yadda aka cireta ko ran mahaifinta, makaranta ma sai ya sakata a jnda karatunta zai lalace ba dan kuma ba shi da hali ba, sai dan an shiga tsakani”

Amma ta kalleta tana nazarin kalamanta ita kanta a yanzu ta yarda ba a banza Appa ya canjawa Hurriya makaranta ba, yarinyar da yake alfahari da basirarta har yana ikirarin fitar da ita waje ta yi karatu amman a yanzu ya cireta daga makarantar kudi ya maida ita makarantar government.

“Tun ina Amarya lokacin da aka hade mu, ta taba ce komai ta dade sai na bar mata mijinta, kuma sai ta saka ni na yi nadamar auren Alhaji, har abada kuma ba zata taba son ko ta so yayana ba, domin kallon da take min na yar aiki be canja ba a idonta, sai ta kakkabe ni kamar yadda ake kabe tabarma a gidan da yardar Allah, tun da na ci amanar ta sai na gani”

Hawaye ya sauko mata.

“Gashi kuma na fara gani, Wallahi da na san zuciyar Hajiya Kaltume ta kai haka da ba zan yarda na auri Alhaji ba duk kuwa da irin magiyar da zai min”

“Oh Allah mai iko, toh wai haka zaku zuba mata ido shikenan ta kashe Hamad ta ci bulus”

“Ba mu da tabbacin ita ta kasheshi, ba Hamad din muka gani ba balle ya fada mana ita ce ko ba ita ba, ko da ma ance yana raye ba lallai ne ya gane ita ta aikata ba, kuma ba jami'an tsaro suka kamata ba, ba mu da wata hujja ta cewar ita ce kawai dai zato muke yi”

Hindu ta sauke ajiyar zuciya ta yi tagumi.

“Toh ni Kam Alhamdulillah ina da kishiya amman Wallahi ba kamar ta ki ba, ba a aure aka aurota miye laifinki wani yace kar ta iya kula da mijinta, ba mai aiki ba namjji ko uwarki aka hallata masa aure Wallahi wani sai ya aureta balle kuma mai aiki, har yaushe zaka dauki hakki ka dorawa kanka”

“Wallahi ni kadai na san abun da yake damuna, wata rana ji nake kamar na yi ta ihu wani lokacin kuma na ji kamar na bi hanya na yi ta tafiya, wani sa'in na ji kamar zan yi hauka, gaba daya ni ma neman fita hayyacina nake”

“Au kuma shi ne kike zaune? Kuma Gwaggo ta saka miki ido? Wallahi zama be gan mu ba, idan ma ke ba zaki iya ba ni zan nema idan na kawo miki karki sha”

Hindu ta mike tsaye a fusace ta figi mayafinta tare da jaka ta nufi dakin Gwaggo, domin fahimtar da ita abun da Iyami ta gagara ganewa. Amma ta share hawayeta da ya zuba a fuskar Hamid.

“Wallahi na yi damar auren mahaifinku, na janwa kaina bala'i na kai kaina cikin manyan mata da ba su da imani babu tausayi, gashi na jefa yarana a cikin matsala, ban san kuma gaba ba me zan gani ba”

Ta fashe da kuka sosai tana jin zafin mutuwar Hamad, ga zafin rabata da Hurriya da Appa yayi ga kuma zafin mutuwar aurenta a lokacin da bata yi tsammani ba, ga kuma zafin ta haihu ya kasa zuwa ya duba abun da ta haifa balle ya saka musu albarka.

______________

Wai ni kam Tsakanin Hurriya da Amma waya fi kowa ban tausayi?

A Next page zamu dunguma a labarin Hurriya, karku manta sunan littafin Hurriya, a yanzu ne zai amsa cikaken sunansa.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻[11/3, 5:25 AM] AMINA KABIR CAPS: *HURIYYA*

*7*

𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 6️⃣

Two days later...

Hindu ta ciro gorar ruwa dake cike da rubutu ta aje a gaban Amma.

“Yace wannan ki sha shi a tsaye kuma ki shafa zaki yi haka har kwana 7, na karya sihiri ne da tsari sosai”

Amma ta kai hannu ta dauka tana juya rubutun.

“Rabawa zan yi har bakwai kenan”

“Eh wannan kuma na hayaki ne, wato matar nan ba karamin asiri ta yi miki ba na shiga tsakaninki da Alhaji, kuma yanzu haka tana nan tana shirin yin wani akan Hurriya”

“Shi ma dai tsafin yake kenan?”
Chapter 12 · 0% Book details