← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 133

Sashe 74

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Toh ni ma dai abun ya daure min kai, amman kin san Captain yana da son yara fa”

“Maganar ba ta son yara ba ce kawai, ko last time da ya aike ni siyo masa a Mall na je office dinsa na samu glass din Hurriya and he was telling me wai ya bata wani gilashin ne, kin tuna ko ranar da ya saka ta girki, and dazu da safe karki ga yadda ya damu saboda ya same ta tana kuka”

“Kuka me?”

“Na munafurci da neman jan hankali mana, ni ma ban san dalilin kukan ba kuma kin ga ko lokacin da ya tarar ina fada da yarinyar ita ya goyawa baya, saboda ita har marina yayi fa”

Momy ta dan yi dariya kamin ta yi murmushi sai kuma ta sake yin murmushi abun kamar zai kama kanta sai kuma ta ji be kama kanta ba.

“Amman Captain yafi karfin wannan yarinyar ai, beside idan ma zai so wata a gidan nan ai ke ce kuma ina jiyo kamshin hakan”

“Babu macen da tafi karfin namiji Momy, yarinyar ta san yadda take ta sace zuciyar maza, haka ta yi min a Salim har yanzu idan na tuna sai na ji wani iri, and now Captain”

“Idan ma haka ne ke kike yin saka, kuma idan har ta dauki hankalin Salim ba zata sami Captain ba”

“Na yi sake? Momy ni fa mace ce i don't run after a men, idan su ba su nuna suna ra'ayi ba, ni ba zan iya zubar da ajina na yi kasuwanci kamar yadda take ba”

Namra na rufe baki Hurriya ta turo kofar falon ta shigo cikin yanayi na damuwa sallamarta ma can ciki ta yi, Momy da Namra kuma babu wanda ya amsa mata, ta iso kusa da Momy ta risina.

“Momy sannu da gida”

Ta mike tsaye sai Momy ta bita da kallo kamin ta ce.

“Ke...”

Hurriya ta kalleta tare da amsawa a hankali

“Na'am”

“Tafi ki dauko min ruwa a kitchen”

“Toh”

Ta juya sai Momy ta ce.

“Cire hijab din ki aje a nan”

Ba musu ta cire hijab din ta aje ta nufi hanyar Kitchen, Momy ta bita da kallo da ta fito ma Momy kare mata kallo take tsab sannan ta karbi ruwa.

“Toh tafi dakinki”

Hurriya ta dauki Hijab dinta ta nufi hanyar stairs, sai da ta haye sama gaba daya sannan Momy ta kalli Namra ta ce.

“Na ga dai idan farin nan ne ke ma kina da shi, kuma ko mazaunai kin fita ban san wani abun ja mata hankali a jikinta ba”

“Tana da kyau Momy kuma munafuka ce ta iya kisisina kala kala”

“Ko dai minene ki cire wannan a ranki, ni da Hajiya Turai babu wanda muke so Captain ya aura sai ke, idan ma be aureki ba ai ba zan bari ya auri yarinyar da ba ajinsa ba irin Hurriya”

Namra ta mike tsaye tana rike da wayarta.

“That's mean idan Hurriya tana gidan nan wani ba zai taba cewa yana so na ba”

“Ki bude idonki Namra yanzu lokaci ya wuce da zaki ce sai anyi yaki a same ki, idan kina son Captain to ki takawa yarinyar nan birki, ko da ma baki son shi ya kamata ki hana alakarsu ko dan abun da ta yi miki amman idan kika kyale kin bata dama kenan, sannan ni da ke mun san Captain ya fi karfin yarinyar nan waya sani ma nan gaba kadan zata iya makancewa gaba daya, kuma yadda uwarta ta zo ta yi mana milki a gida yarta ma tace zata auri Captain ta yi yadda take so, abu ne da ba zan dauka ba, idan Khairy ce ko wata a cikin yayan Kaltume kina ganin zata kyale Hurriya ne?”

Fada sosai Momy take ta wani bangaren tana ganin kamar har fa laifin Namra na saken da take yi har Hurriya take son damar yi mata. Namra ta sauke ajiyar zuciya ya nufi stairs ta sani tana son Captain fiye da yadda ta ji tana son Salim da farko, har tana murna tana ganin kamar sauyi ne Allah yayi mata saboda ta rasa Salim yanzu kuma Hurriya na son sake jefata a cikin wata damuwar, idan har bata auri Captain ba to be kamata ace ya auri kowa daga familynsu ba sai dai daga wajen familynsu balle kuma ace cikin gidansu kuma kanwarta da suka hada jini daya. Ko da soyayya ce kadai be kamata Hurriya ta yi da Captain ba balle aure, sai dai yadda ta san halin Captain wata kila ko da wata alakarce ba zata dade ba saboda yanayin fushinsa da saurin daukar zafi kamar kofin tasa, sai dai duk da haka Momy tana da gaskiya be kamata ta zuba ido Captain yayi soyayya da Hurriya ba ko da be aure ta ba, hakan zai lalata alakarsa da gidan idan suka samu tsabani kuma zai juya mata baya ba zai yi tunanin ya aureta ba. Jingina ta yi da kofar dakinta bayan ta rufe, abu ne mai zafi da ba zata iya rike hawayenta ba, ko da tafiya kuke a hanya wani yace yana son kawarta ba ita ba zata ji babu dadi balle kuma ace cikin gidansu. Bayan kuma duka mazajen nan biyu sun nuna ita suke so amman gashi yanzu Hurriya tana dauke hankalinsu, ta saka hannunta a baki tana ciza kumbarta, gaba daya ta ma rasa me zata yi, ta wank bangaren tana ganin kamar yunkurin yin wani abu zubar da kimarta da martabarta ne ne mace.

“Amman Ina son Captain, Hurriya me yasa kike min haka? Why?”

Ta fadawa kanta kamin tambayar karshe ta biyo baya. Ajiyar zuciya ta sauke ta share hawayenta ta nufi gadonta ta zauna tana busar da iskar bakinta, zuciyarta na mugun zafi wani fitinannen kishi take ji marar misaltuwa, kamar an fisgeta haka ta tashi ta fice daga dakin.

A kasale Hurriyya ta shiga dakinta bata lura da ledar dake kan gadonta ba saboda hankalinta gaba daya ba a gurin yake ba, ya tafi gurin tunanin rayuwarta ta baya, alamar da Amma ta bar mata na cewar ba zata dawo gidan ba ya saka ta kewar lokacin da take gidan, tana ayyana yadda zata cigaba da fuskantar wahala da kalubale na rashin Amma a gidan. Daf da zata zauna ta yi arba da bakar ledar daman hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba. Hannu ta saka ta lalaba ta juya ta kalli kofar dakin dake rufe tana mamakin waya kawo ledar a dakin. Zaunawa ta yi sannan ta saka hannu biyu ta bude ledar wani dan karamin kati ne a sama dauke da wasu takaitattu kalmomin.

_Tafiya ta kama ni yau din nan, kuma zan yi sati a KD, na san kuma ba ki samu abinci in time na siya miki wannan i hope zai taimaka, karki ci da yawa so that yayi miki sati lol_

_Yaya_

Tana gama karanta sai ta ji kamar an cire mata damuwanta gaba daya, sai murmushi take tana sake karantawa, and the part da yace kar ta ci da yawa ya saka ta nishadi. Ta aje takardar a gefe ta shiga ciro kayan, kwalin dabino ne uku sai chocolate da kilishi da aka busar tare da biscuits kala kala da kuma karamin kwalin cornflakes da madara cube sugar and different varieties of sweet Candy. Chocolate daya ta dauka ta bude ta fara ci tana tuna abun da ya faru a dazun tsakaninsu murmushinta ne ya fadada zuciyarta kuma ta shiga bugawa da mugun karfi kamar zata fasa kirjinta ta fito, numfashinta yana yin sama kamar yadda ta samu kanta a lokacin da ya matso daf da ita yana mata magana.

“Hurriya?”

Ta kalli kofar dakin a zarane tana amsawa Namra dake tsaye rike da kofar.

“Na'am”

“Ina fatan dai ba rokon Captain kika yi ya siya miki wani abu ba?”

Ta girgiza mata kai.

“Good saboda wannan iskancin da karuwanci da kika rika yi ma Salim be kamata ki koma gurin abokinsa ba bayan kuma kin nuna masa baki sonshi, sannan Captain ba sa'arki ba ne zaren ba kalar yadin ba ne, yana da kyau ki yi hankali tun wuri, bana son kina shige masa, karki sake yi masa magana daga yau, saboda ni yake zuwa gidan nan so daga yau bana son na sake ganinki idan yana nan, ban ma rashin hankali irin na ki me Captain zai yi da makauniya”

A nan sai Hurriya ta kasa hade maganar da Namra ta jefe ta da ita.

“Zan kiyaye, ni daman ba ni nake mishi magana ba ni babu wata alaka a tsakanina da shi, wata kila ba ki fahimta ba ne, zancen makanta kuma wannan ba da ni kike ba, da mahallice ma kike ke ma kuma ba ki wuce ya dora miki ba”

“Idan be dora min ba, ke ai zai ki zo ki dora min shashasha kawai”

Taja tsaki sannan ta ja kofar dakin ta rufe da karfi. Hurriya ta ja dogon numfashi ta sauke.

“A haka Amma kike cewa ba zaki dawo ba? Haka zan yi ta zama a gidan nan ina ganin wulakanci kala kala? Idan wannan ya wuce wani zai zo? Tun da kika bar gidan nan ban sake farinciki ba, na koma kamar wata bare kowa taka ni yake yadda ya so”

Ta share hawayenta, ta sake daukar takardar ta karanta, this time around sai ta ji karatun be mata dadi ba kamar dazun ya manta da ita damuwarta ya sauya shafin bakincikin zuwa fari ba, mikewa ta yi tsaye ta nufi gurin da wadacan takardun da ya bata suke ta saka wannan a ciki. Sannan ta dawo ta sauke kayan daga kan gadon ta jerasu a closet dinta ta dawo ta kwanta saman gadon feeling so boring ba tare da dalili ba.

A WEEK LATER.....

Khairy ta cije baki tana jin kamar ta buga wayar a kasa kuma babu dama.

“Haba Adam wani irin careless ne wannan? Na fada maka yau aka sallamo Hajiyata daga asibiti fa, kuma yar'uwata ta rasu ko sati biyu ba ayi ba amman ka kasa daga min kafa wani irin abu ne wannan?”
Chapter 74 · 0% Book details