← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 133

Sashe 1

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*HURIYYA*

*BOOK 2 PAGE 1*

𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣

Kamin direban ya isa gida duk wanda ke cikin motar ya dauka Hurriya shudewa zata yi, saboda kukan da take yana yin sama da nufashinta kamar nunfashin zai fice daga jikinta gaba daya. Namra ce take rike da ita tana kuka tana bata hakuri.

“Yi Hakuri Hurriya In Sha Allah zai dawo lafiya Allah zai tsare su”

Hurriya bata iya furta komai, gashin idon nata ya rufe gaba daya saboda kukan hawayen ya hanata ganin dishe-dishe ma da take gani idan babu gilashi a idonta. Direban na fakawa Salma da Khairi suka fita suna kuka suka nufi bangaren Hajiya Kaltume suna kuka, Namra kuma ta tsaya ta riko Hurriya suka fito.

“Bana ganin komai Yaya Namra idon ya rufe gaba daya... Karki bar ni nan dan Allah tsoro nake ji... Kira min Yaya Yasir ko ki kaini gurin Amma ko ki kira min Appa na dan Allah”

Tana maganar muryarta na rawa saboda numfashim da ya sarke ta. Ta san a gurin dayan su ne kadai zata yi kukanta ta more kuma ta fada musu abun da ya faruwa. Kowane ďa ko ƴa idan abun farinciki ko kishiyarsa ya same shi guduwa yake gurin uwarsa, sai dai ita a yau bata da wannan gatan, ba dan mahaifiyarta bata raye ba sai dan bata tare da ubanta, bata taba sanin zafin rashin Amma a gidan ba sai yau, ko wane ďa yana bukatar uwa a kusa da shi balle kuma ita da take da lalaurar ido. Dukawa ta yi a gurin ta dora duka hannayenta biyu a kai ta kwalla ihu da kukam muryarta tana kuka har sai da duk wanda ke harabar gidan hankalinsa ya dawo kanta.

“Wayyo Amma ma, Amma..... Amma... Amma... Ke..... Amma na”

Namra ta yi saurin rika hannunta tana kuka.

“Hurriya ba gani nan ba, ta zo muje ciki Momy tana nan ai”

Ta fisge hannunta, sanin kanta ne daga Momy har Hajiya Kaltume babu wanda ta isa ta jingina a cikinsa ta yi kuka, domin ba su dauke ta kamar sauran ƴaƴansu ba.

“Kira min Yayana kira Yayana”

Namra na cira kafa da zimmar tafiya kiran Yasir sai ta hangoshi ya fito da saurinsa ya nufo inda yake.

“Hurriya”

Hurriya na jin muryarsa ta mike tsaye da sauri ta fara lalaben inda zata ganshi.

“Yayana Yayana Yayana”

Kusan duk wanda ke tsaye yana kallonta sai da ya tausaya mata, domin lalurar rashin gani babbar matsala ce. (Alhamdulillah da kyautar Allah, if you can read this ku gode Allah, ba zabinku ba ne, kyautar Allah ce, and don't forget littafin na kudi ne idan kika karanta baki biya ba, ko kika min sharing na barki da Allah)

Yasir na isowa ya rika hannunta dake ta rawa take da fatar bakinta.

“Yayana dan Allah ka kai ni gurin Amma... Dan Allah..”

Without second thought yaja hannunta ya karbi key hannun dayan direban da ya aje Hajiya Kaltume few minutes before the incident happen. Ya bude motar Namra bata kara jin tausayinta ba sai da ta ga yadda take lalaben motar zata shiga, Yaisr ya taimaka mata ya saka ta a back seat sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya murza key ya juya motar cikin tashin hankali, ba dan yana namiji ba da tuni shi ma ya fashe da kukan kamar yadda kanensa da mahaifiyarsa suke kukan. Shiru Hurriya ta yi a cikin motar domin bata ganin komai sai duhu zucuyarta kuma ta cika fa tsoron abun da ya faru. A harabar gate din gidan Yasir ya faka motar sannan ya budr ya fito da Hurriya. Sai da ya daga gate din gidan sai kuma ya ji ba zai iya shiga ciki ba domin ba zai iya zama mutum ya farko da ya labartawa Amma labarin an sace danta ba, ya san idan ya shiga gidan ta ga yarta a wannan halin sai ta tambaye shi shi kuma ba zai iya mata karya ba. Haka kuma ba zai iya barin Hurriya ta shiga cikin gidan ita kadai ba a wannan yanayin.

“Hurriya ko dai ki hakura mu koma? Ba zan iya shiga cikin gidan nan ba, bana son na daga hankalin Amma a yanzu”

Tana jin haka sai ta saka dayan hannunta ta kwance hannunsa dake rike da nata.

“Tafi zan.... Iya... Shiga... Daga... Nan”

Be san bata gani gaba daya ba, a zatonsa tana gani dishe-dishe kamar da, dan haka be musa mata ba ya bude mata gate ta lalaba ta shiga, ya maida kofar ya rufe sannan ya koma cikin motar ya fice daga unguwar. Hannu Hurriya ta mika tana lalaba hanya, tare da amfani da zuciyarta tana ayyana yadda hanyar take a lokacin da take gani.

“Ke Hurriya...”

Ta ji muryar Rukayya sai wani sanyi ya ziyarceta. Ta karaso kusa da ita ta rika hannunta.

“Waya kawo ki? Mun ji an bude kofar gate ba mu ga an shigo ba shiyasa na fito na duba”

“Yaya Yasir ne ya kawo ni, ya tafi Mama Rukayya kai ni gurin Amma na”

“Me ya same ki Hurriya?”

“Kai ni gurin Amma please, bana gani yanzu bana iya ganin komai sai hudu, gaba daya idon ya rufe, na daina gani dishe-dishen ma”

“Innalillahi”

Rukayya ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki, Amman dake zaune dakin Gwaggo tana kwadon zogale ta aje kwanon zogalen ta yunkura da cikinta wata tara ta mike tsaye da sauri ganin Hurriya da hawaye a fuska kacha-kacha har ya bata gaban hijabinta, gata sanye da uniform din makaranta da bata cire ba kuma babu gilashi a idonta.

“Hurriya me ya same ki?”

Kunne da jikin da yayi kewar uwa ne kadai zai iya fahimtar yadda ruhu yake ji idan ya ji ko yayi arba da uwa.

“Amma ina kike?”

Ta saki hannun Rukayya ta fara lalaben inda take jin muryar Amma. Amma ta mika hannu ta rikota sai Hurriya ta rumgume ta ta kwanta jikinta tana wani irin kuka da ya saka Amma ta kasa rike kanta ita ta fashe da kuka.

“Me ya faru Hurtiya? Me ya same ki? Waya kawo ki? Me ya samu idon naki ina gilashinki”

Har Hurriya ta bude baki ta yi magana, zancen da Yasir yayi a waje ya fado mata a rai. Shi ma kenan ya ce ba zai iya sanar da Amma ba balle kuma ita da take yarta. Kamar an saka allura da zare an dinki bakin Hurriya haka ta zama, ta kasa furta komai kuma ma sai ya koma mata cikin zuciya hawaye kawai take ita yi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Amma ta furta gabanta na bugawa da karfi. Ta san ba lafiya zata kawo yarta a irin wannan yanayin ba, kuma gashi ta kasa fadar komai sai rumgume ta take kamar zata shige jikinta.

“Hurriya yi a hankali mana, kin san akwai kanenki a jikinta, ko kuma ki zo ni na rumgume ki idan rumgumar kike so”

Gwaggo ta fada, sai Hurriya ta girgiza kai tana kara kankame Amma.

“Hurriya dukanki aka yi?”

Ta girgiza kai.

“Wani abu aka watsa miki a ido?”

Ta girgiza kai.

“Fada kika yi da wani?”

Ta girgiza kai.

“Dan Allah ki bude baki ki yi magana mana minene? Ko dai fada kika yi da Hamad? Na san zai iya cewa yayi miki mugun duka saboda bana gidan?”

Maganar da Amma ta yi ta Hamad ta saka Hurriya fashewa da sabon kuka.

“Yasir ya kawo ta, ta fa yi magana dazun yanzu ne dai ta kasa cewa komai”

“Wata kila fadan ta yi da Hamad shiyasa ta kasa fada tana tsoron kar na yi masa fada ya kara mata”

Zuciyar Amma ta fi aminta da fada suka yi da Hamad shi yasa har ta furta hakan, ganin Hurriya ta fashe fa kuka a lokacin da ta ambace shi.

“Kai Hamad yana da matsala Wallahi sai ace baka iya zaman lafiya fa yan'uwarka, ko tausayinta baya ji”

Rukayya ta fada. Sai Gwaggo ta ce.

“Kusan duk mabiyi da mabiyi haka ake, ba kowa ke shiri da juna ba”

“Amman dai shi nashi yayi yawa”

Amma dai ta yi shiru tana ta saurare numfashin Hurriyya dake fita da karfi..

FAMILY HOUSE...

A rikice Appa ya fito motar tun kamin direban sa ya gama fakin, ya nufi hanyar Falon Hajiya Kaltume cikin tashin hankali, hausawa suka ce ba a saka masa rana. Gaba daya kuka suke cikin falon har Namra da ta shigo. Hajiya Kaltume na ganin Appa ta kara mulmulawa a kasa tana dafa kai ta tashi zaune ta koma ta kwanta kamar wata bayarba...

“Eyyyy Eyyyy Eyyyy ni Kaltume yau na shiga uku yata, wayyo Umm Ruman, Alhaji ina cikin matsala da bala'i sun sace min yar auta, wai ni mi na yi ma mutane ne ne? Wayyo Allah na”

“Haba Hajiya ki yi hakuri mana, idan ke kina haka su kuma yara waye zai rarrashensu? Dan Allah ki tashi”

“Alhaji wasu sun tare mota sun tafi da Ruma”

“Hamad ma yana can hannunsu ai, ba ita kadai ba, kuma In Shaa Allahu zaku dawo lafiya”

“Mutanen nan ba su da imani shi Hamad ai namiji ne, ita kuma mace ce yarinyar yar shawalwala”

Appa ya zauna a kujera ya cire hular kansa duk sanyin ac falon gumi ne ke keto masa ta ko'ina. Salma da Khairi suka fara fada masa abun da ya faru suna kuka ba tare da ya tambaya ba, Kamin ya dago ya bi kowa da kallo.

“Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba, ku yi ta addu'a, idan ma wani abun suke so ai dole za su kira. Ina Hurriya?”

Appa na rufe baki Yasir da shigowar falon kenan ya amsa masa.

“Yanzu na kaita gida?”

Appa ya masa wani kallo.

“Gida ina?”

“Gurin Amma tana ta kuka ta ce a kaita can, shiyasa na kaita amman ban shiga gidan ba”

Appa ya dafe kai cike da takaici kamin ya dago ya kalli Yasir yana jin kamar ya mareshi.
Chapter 1 · 0% Book details