Sashe 86
Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kana aje wayar nan, ka duba list din mutanen da suka dora hotunan karka damu da yawansu ka turo min su, tare da sunanyen gidanjen jaridun, ka hado min da account number dinka”
“Okay Sir”
Ya sauke wayar.
“Za su san sun taba mai gata, na miki alkawarin farinciki Hurriya zan cika miki shi... ”
Ya fada sannan ya nufi madubin dake bandaki ya dora wayar ya cire tufafinsa ya sakarwa kansa shower. Ya bata minti arba'in a bandakin sannan ya fito yana rike da wayarsa jikinsa kuma na daure da tawul.
“Good Nafi'u”
Yayi forwarding sakon zuwa mabanbanta gurare sannan yayi waya da mutane daban daban. At the end ya kira Namra.
“Hello Captain”
“Wace asibiti aka kai Adam? Kanen Salim”
“Ban sani ba, ya jikanka?”
“Bincika min yanzu”
“Toh”
Ya aje wayar ya dauki wani tawul din ya goge jikinsa, sannan ya zauna gaban madubi yana hararo abubuwa da yawa. After like one hour yana zaune kan carpet bayan ya sallame sallah wani kiran ya shigo a wayarsa bayan na calls din dake ta shigo masa na yan'uwa da abokan aiki masu son tambayar jikinsa. Amman be amsa kiran kowa ba sai na Namra.
“Yana yana asibitin Yariman Bakura, layin ya hadurra”
“Good”
Ya yanke kiranta tun kamin ta kara cewa komai, ya shiga whatsapp dinsa ya sake sauke hotunan da Salim ya turo masa, ya yanke iya gurin da fuskar Adam take ya turawa wata number tare da address, sannan ya fito whatsapp din ya shiga contact dinsa ya nemo number the same person da ya turawa sakon ta whatsapp.
“Hello Sir”
“Uzairu na turo maka hoto da addreshin wani dan'iskan yaro yanzu a whatsapp, ni ya taba so the fight is between me and him.. Ka duba address din ka dauki mutanenka ki shiga cikin asibiti ku dauko shi ku aje min shi wani gurin da babu haske kuma babu rahma, ku masa doka irin dukan da idan na masa tambaya zai ba ni amsa a take amman ban ce ku kashe shi ba, ku aje shi a gurin for 10 hours”
“Yes Sir... ”
Ya sauke wayar, sannan ya amsa dayan kiran daya fito daga bachi.
“Yeah good so nake ku kama mai gidan jaridar ku bincike shi a ina ya samu hotunan, at the end ku sa ya rubuta cewar sheri aka yi mata kuma yana neman yafiyar Hurriya, ku saka yayi hakan tun a cikin office din ku idan be yi haka ba ku karya kafarsa”
“Amman Captain me yayi maka?”
“Yarinyar da suka batawa suna yarinya ce mai tsada she is innocent, please karku ragawa kowa a gurin”
“Subhanallahi, aiko za su ga aikin DSS”
“Thank You My friend”
Ya sauke wayar ya amsa wata wayar, haka yayi ta bata umarni a inda umarninsa suke jira a inda alfarma yake nema sai ya roki ayi masa haka.
HURRIYA POV.
“Daure ki sha tea ne kuma ba mai yawa ba”
Hajiya Binta na lalabata tana hada mata tea. Gwaggo ta ce.
“Babu yadda ban yi da ita ba amman ta ki cin komai tun safe har yanzu”
“Bana iya cin komai ne, ko na ci bana iya hadewa”
“Hurriya wannan abun duk zai wuce, wata kila an buga an buga an ga babu sa'a ne shi ne aka bullo ta nan, amman duk wanda ya sanki ya san ba zaki aikata ba, babu wanda zai yarda kawai ana son a jefaki a damuwa ne, dan haka karki bari damuwar da suke son jefaki ta tasirantu akanki karbi ki sha”
Ta mika hannu tana lalaben kofin ta karba ta kai bakinta ta kurba kadan sai ta gagara hadewa.
“Hajiya bana iya hadewa”
Hajiya ta karbi kofin ta rike tana kallon jikarta cike da damuwa sosai a fuskarta.
“Jibi zan wuce Ummara zan miki addu'a mai karfi a can, da yardar Allah wanda ya aikata miki haka ba zai sake sanin rahma a rayuwarsa ba”
“Amin Hajiya”
Gwaggo ta amsa, sannan suka daga kai gaban dayansu suka kalli kofar dakin da aka turo. Cikin wani irin yanayi kamar na kunya kamar tsoro Yasir ya shigo dakin fuskarsa a raunane.
“Yasir”
“Na'am Hajiya”
Hurriya ta sauke kanta kasa duk da kasancewar bata ganin kowa tana jin kunyar aga fuskarta saboda an yada tsiraicinta. Yasir ya tsaya daga tsaye suka gaisa da Hajiya da Gwaggo be ce da Hurriya komai ba ita ma bata iya dagowa ba balle tace masa wani ba sai hawaye take.
“Appa ya ce na zo da Hurriya”
“Ka zo da ita kuma? Be san tana asibiti ba?”
“Ya sani, yace na yi magana da likitan ya bata sallama”
“Saboda me? Be san idonta ya samu matsala ba?”
“Ya sani Namra ta fada mana komai, Hajiya idan za ayi mata aikin idon a ba nan za'ayi ba kuma abu ne da yake bukatar shiri da tantance inda ya kamata da kuma likitan da ya dace”
Hajiya zata sake magana Gwaggo ta dakatar da ita
“Je ka karbo sallamar, zamu tafi da ita mu ga iya gudun ruwansa amman ba zan bar Hurriya ta zauna a gidan nan ba har bada...!”
Yasir ya juya ya fita daga dakin ba tare da yace komai ba, Hajiya Binta kuma ta hau masifa ta daga wayarta ta kira shi kiran be shiga ba. Misalin karfe biyar da mintuna Yasir ya faka a harabar Appa, Gwaggo ta fara fita sannan ta fito da Hurriya Hajiya Binta ma ta fito tana kara shiryawa duk wani abu da ďanta zai yi. Hurriya ta kama hannun Gwaggo ta rike da karfi.
“Gwaggo tsoro yake kar Appa yace be yafe min ba”
“Ko da ya fada ba zai kama ki ba, domin ba ki aikata ba kuma Allah mai adalci ne”
Cikin karayar zuciya da duhun idanuwa Hurriya ya shiga bangaren na Appa Gwaggo tana mata jagora komai bata iya banbance komai a yanzu. Yanayin yadda ta ji numfashi na tashi ya karantar da ita falon cike da mutane da bata san su waye ba, yan gidansu ne kadai ko kuma dai duka familynsu da suke garin. Me Appa zai fada akanta shi ne abun da ya fi tsorata ta, da lalabe ta zauna a falon kusa da Gwaggo, hawaye na mata zuba, ta wani bangaren tana gode Allah da bata iya ganin komai, a yanzu da bata san da wane ido zata kalli Appanta ba.
“Hurriya...!!!”
Gabanta ta kasa amsa kiran da Appa yayi mata gabanta sai bugawa yake da karfi.
“Kina da wata hujja ta kare kanki akan abun da muka gani tsakanin jiya zuwa yau?”
Ta yi shiru, Gwaggo ta ce.
“Ka san dai ba zata aikata ba...”
“Gwaggo dan Allah ki yi hakuri ki bari ta amsa min”
Appa ya bukata cikin yanayi da ke nuna shi ma yana cikin damuwa kwatankwacin wanda Hurriya take ciki.
“Appa akai ni na yi alwala”
Tana fada ta mike tsaye tana kuka.
“Ba sai kin rantse ba abun da duk ba halinki ba ba zaki aikata shi ba”
Hurriya ta girgiza ma Hajiya Binta kai ba dan tana ganinta ba.
“Idan ban rantse ba babu wanda zai yarda da ni, ni ma kuma ba zan samu sukuni ba, dan Allah ku kai ni bandaki”
Yasir ya kalli Ruma.
“Tashi ki kaita”
Ruma ta tashi ta rika hannunta suka shiga bandakin dake cikin falon, Hurriya ta yi alwala ta fito ta bukaci a bata kur'ane.
“Bari zaka yi ta yi rantsuwar nan Tsoho?”
Appa ya kasa amsawa mahaifiyarsa, shi ma ji yake kamar Hurriya ba zai aikata hakan ba sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa. Yasir ya tashi da shiga bandakin da Hurriya ta fito yayi alwala ya shiga bedroom din Appa ya dauko mata alkur'ane ya kama hannu ya mika mata, shi kansa idan ta rantse zai fi jin natsuwa, domin ya shirya ui mata mummunan hukuncin idan har ta tabbata ta aikata. Hurriya ta rike qur'anen da dayan hannunta sai ta dora hannunta na dama a saman kur'ane ta dafa.
“Na rantse da littafin nan, abun da yake cikinsa da wanda ya aiko da shi ban aikata ba Appa”
Ta karasa cikin kuka... Gwaggo ta saka kalma shahada.
“La'ilaha Illaha Muhammad Rasulullah”
Sai gaba daya falon ya amsa suka karasa a tare.
“Sallalahu Alaihi Wassalam...”
Appa ma ya sauke kansa kasa ya fashe da kuka, babu wanda be yi hawaye ba a falon kuma babu wanda be tausaya mata ba ciki har da Momy. Yasir ya sa hannu ya karba yana hawaye da murmushi a fuskarsa, yar'uwarsa ta tsarkake kanta a gaban kowa hakan ya kwantar masa da hankali yanzu kam ya yarda hundred percent bata aikata ba.. Appa ya dago hawaye na zubowa daga idonsa ya mika mata kamar ance masa tana ganinsa.
“Zo nan gareni yata, fada min wa kika tarewa farinciki ya aikata miki haka?”
Hurriya ta fara takawa ta inda take jiyo sautin muryarsa tana kuka tana lalaben hanya, Yasir ya rika hannunta ya karasa ta ita gurin Appa, hannayensa ta fara kamawa sannan ta zube kasa a gabansa ta kwantar da kanta a kafarsa.
“Allah ya tsinewa wanda ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai gama lafiya ba, bakinciki da ya saka mana da neman bata miki da sunan gidan nan Allah ya ninka masa shi...”
Kowa ya amsa da Ameen ban da Khairy da Namra dake ta kuka kai ka rantse da Allah su aka aikatawa haka ba Hurriya ba.
“Ba zan bar maganar nan ba, sai na yi shari'a da yaron nan, ya ci mutuncina ya ci mutuncin ƴata ba zan kyale shi ba”
“Ni ma na yi wannan tunanin Appa, na kudirta a raina idan har ta tabbata Hurriya bata aikata abun nan ba, ba zan kyale maganar nan ba”
Yasir na aje aya Hajiya Binta ta ce.
“Da kun kyauta daman be kamata a kyale ba”
Momy ta tashi ta fice ba tare da tace komai ba, Ruma ta bi bayanta. Gwaggo ma ta mike tsaye fuska a daure ta ce.
“Zan tafi gida, kuma zan tafi tare da Hurriya saboda a can zata samu kulawa”