Sashe 102
Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Indai kai aminin Malam ne tabbas ka san gaskiya sai idan cinye dukiyar zaku yi, zan tafi amman ba zamu kyale wannan maganar ba”
Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fice a gidan cikin bacin rai tsabanin shigowar da ta yi da zullumi. A mota ta tararda Hajiya Fatee ta fito da kafafuwanta waje tana zaune daga ciki ta jingina da motar.
“Malam ya mutu, kuma ta tafi da dukiyarmu amman na ke kin yi wauta Hajiya Fatee kuma kin yi sakarci irin haka ake gudu daman, Malam be bar wata wasiya akan kudinki ko gonakin da yake cewa ya siya miki ba, kuma babu wata shaida ke ma kuma baki nemi ya baki shaidar komai ba lokacin da yake raye, yanzu ga irin ta nan nan ke baki ga duniyarki ni kuma ba ni ga aiki ba kudin rakumi....!”
“Ni ai idai wannan abun ba zai tashi ba, kudin mai sauki ne indai wannan abin kunyar ba zai bayyanar min ba to zan iya hakura da komai”
Direban ya kai dubansa garesu.
“Subhanallahi wai Malamin da kuka zo gurinsa ne ya rasu?”
“Ba a sani ba, ina ruwanka? Ka kama bakinka ka yi abun da ya kawo ka, ba gulma da sa'ido ba”
“Ah Hajiya daga tambaya Allah ya baku hakuri, ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni”
Ya bude da yake jingine ya shiga ya rufe.
“Shiga mota mu tafi Hajiya Kaltume, zancen gida da gona zamu yi tunanin abun da ya kamata mu yi daga baya”
Hajiya Kaltume ta juya ta dayan bangaren ta shiga motar, tana kuka.
“Abubuwa duk sun lalace min, idan na taba nan wani gurin ne zai kwance, idan na dawo ta nan wani gurin kuma sai ya balle, ina saka ran za'ayi min aiki na samu sauki wannan rayuwa da nake ciki sai kuma mu zo mu tararda bakin labari wannan abu da me yayi kama... ”
“Ke naki ai duk mai sauki ne, ni cw a ruwa tsundun kuma babu tudun dafawa”
Haka suka yi ta juya zancen suna bakinciki da kukan da ya mantar da su akwau bandits a hanya, direban yana sauke su a gidan Hajiya Fatee yayi tafiyarsa. A bakin kofar dakin Hajiya Kaltume ta zube zaune ta cire mayafi ta je jaka a gefe tana kuka.
NAMRA POV.
Gaba daya ta jika screen din wayarta da hawayen dake zuba a idonta, hoton Captain take kallona gurin da yake sanye da kayan sojoji yana daga tsaye aka dauke shi hoto. Ta san ta yi rashi na har bada domin abu ne mai wahala a yanzu Captain yace zai dawo ya aureta ko da kuwa ya rabu da Hurriya, ta san ba haramun ba ne amman ai da kunya, ace miji ya saki kanwa ya auri yaya, kuma yadda ta san halin dan'uwanta ba zai aminta ya aikata haka ba.
“Tun farkon zuwanki bangaren nan, ban miki komai ba sai alheri, ke kika saka na canja ashe ma kara da na canja domin kin nuna min cewar ke ba halak ba ce mai tausayi, kin raba ni da Salim na hakura ina murna Allah zai musanya min da ďan'uwan sai kuma ki zo ki karbe min shi? Baki ji kunya ba? Kin raba yayarki da samari har biyu?”
Ta runtse ido tana kuka.
“Ina sonka Captain ina sonka me yasa baka gane ba, duk zuwan da kake gidan nan baka fahimci hakan ba? Ko kuma dai Hurriya ta dauke maka hankali ne saboda ta fi ni kyau? Me ya rude ka ka auri yarinyar da ba ajinka ba, yarinyar da bata dace da kai ba, irin wannan jihadin da ka yi a finafinai nake ganin yana faruwa, ko kuma a wasu kasashen turawa amman ba gidab Malam Bahaushe ba, waya ce maka hakan zai baka kwanciyar hankali? Me yasa zuciyarka bata shawarce karka aikata ba?”
A firgice ta bude ido ta kalli wayar da ke ringing, zuciyarta ta shiga shawarar ta daga kiran na Salim ko kuma ta kyale shi. Bata gama yanke hukunci ba ta samu kanta da amasa kiran.
“Hello”
“Namra... Ai da kin fada min dan'uwanki Captain zaku bawa auren Hurriya da ban wahalar da kaina ina neman ta so ni ba”
Namra ta yi shiru hawaye na sauko mata.
“Na ji an daura aure a yau, ina taya ku murna, amman ki sani amana ba zata bar dan'uwanki ba, ya ci amanata ya aikata abun kunya, ya aure budurwar abokinsa abokin ma na kusa da shi, yanzu na gane dalilin da ya sa baya son ma na yi masa zancen Hurriya ashe kansa yake yi ma campaign, kuma bukata ta biya tun da yayi nasara sai dai ina son ku sani KARMA is real kuma kowa ya aikata mai kyau zai sani”
“Salim bana da masaniya akan komai, laifin ba na Captain ba ne na Hurriya ne, daga mahaifiyarsa har mu ba musa san da zancen daura auren a yau ba, sai sanar mana aka yi, wata kila ta yi magana da shi ne ta roki yayi mata haka, amman Captain ba zai yarda a aikata hakan da son ransa ba, waye zai so ya auri Hurriya bayan duk abun da ya faru a yanzu, kuma idonta ya rufe bata ganin komai a yanzu...”
“To me yasa ya aureta?”
“Shi ne abun da nake kokarin ganewa, ni kaina a rikice nake Salim...”
Be sake ce mata komai ba ya katse kiran, sai ya jefar da wayar a kasa ta fada a gadonta tana kuka mai karfi, bata taba jin kaunar Captain ba irin yau bata taba sanin tana sonsa so mai tsanani ba sai yau.
CAPTAIN JAMAL POV.
Babbar rigarsa ya cire ya juyo ya dauki wayarsa ya amsa kiran dake shigowa.
“Ranka ya dade barka da yamma”
“Barka dai Allah yasa akwai labari mai dadi”
“Akwai ranka ya dade, duk mutanen da ka aiko mana da sakon sunayensu mun kama wasu mun bincike su wasu kuma mun musu barazana a waya sun goge posting din sun bada hakuri, sai dai dukansu sun ga horunan ne a wani gurin ne suka kwafa suka yada abun, su ma kuma duk mun bisu mun saka sun goge kuma sun bada hakuri, mutum daya ne ya ce mana wani ya turo masa hotunan da bayani shi da aka turowa da kuma mu da ya fadawa mun bincika account din sai muka samu an goge account din.
“Na gode sosai already a nan mun riga mun gane wanda ya aikata abun, daman dai bukatar mu a batar da hotunan daga internet, thank you so much, zan tuntube anjima”
“Thank You Sir”
Ya sauke wayar Adaidaita lokacin da mahaifiyarsa ta biyo bayansa ta daga bangaren Daddy. Kallonta yake yana rike da wayarsa har ta karaso inda yake tsaye tana murmushin takaici.
“Congratulations ka yi aure Jamal, ka auri yarinyar da haukan ka yake nuna maka kana sonta, alhalin kanka ka wulakanta, makiyi zasu mana dariya su maka, ka zama abun kwatance a cikin sa'ainka da friends dinka, saboda ka auri makauniya kuma yarinyar da a yau idan na bude data na zan iya ganin siraicinta, wani ya rigaka taba jikinta, yarinyar da mahaifiyar da kuma kaf danginka ba a maraba sa zuwanta amman a haka farinciki kake kana jindadin ka samu mata, a daura aurenka a cikin gida, daga mahaifinka sai masu aikin gida sai uban yarinya, kai da ya kamata duniya ta san ka yi aure labarin aurenka ya cika kafafen sada zumunta sai gashi ya kare a karamin gida kamar wanda ya aikata sheri”
Ya rage tsawonsa ya zauna akan gado.
“Ammy na san baki son yarinyar nan, ba zan iya sakawa ki so ta ba, amman dai ina son ki sani ni dai ina kaunar yarinyar nan irin kaunar da ban taba jin ina yi ma wata mace ba, kuma jifanta da kike da kalamai marasa dadi ni kike gogawa bakinciki domin ita din matata ce a yanzu”
Ta kara yin murmushi tana daga gira.
“Haka ne Romeo uban soyayya, matar ka ce tabbas babu wanda ya isa ya goge wannan, ni kuma uwarka ce na fi matarka karfin ikonka a kanka, kuma har abada ba zan taba karbar Hurriya a matsayin suruka ba, ba zan taba sonta ba”
Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi ta nuna shi da yatsa.
“Jamal ni na haifeka ka nuna min karfin soyayya, mahaifinka kuma ya nuna min karfin iko, ni kuma a yau zan nuna maka karfin hakki...”
Da kakkausar murya ta fada masa haka ta juya ta fice daga dakin. Captain ya soke kai kasa damuwa na baibaiye shi.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/21/2023, 11:29 AM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
4️⃣7️⃣
Bayan kwana biyu....