← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 133

Sashe 115

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wallahi Wallahi Wallahi Ammy ban san dalilin da ya saka nake kaunar yarinyar nan ba, ni dai kawai Allah ya saka min kaunarta, ina jin farinciki a tare da farincikinta ina jin damuwa a tare da damuwarta, idan wani ya tsane ta ina jin kamar ya tsani cigaba ne, ita kadai ce yarinyar da nake jin zan iya jure duk wani abu da ya shafe ta, zan iya daukar duk wani zagi da suka a duniyar nan, ban sani ba ko a nan gaba zan gane kuskuren hakan, amman a yanzu bana jin son kowa sai ita, shiyasa na kan kasa auna abun idan an tuna duk kaunar da kike min matsayinki na uwa kin tsani wandda nake so, to ina zan kama Ammy? Wani lokacin ina jin tsoron kar yarinyar nan ta dawo a gidana matsayin matata ki musguna mata ko ki wulankatata, kamar ni kika yi ma, na san ba zaki yi fatan danki ya wulakanta yar mutane ne balle ke kanki ki wulakanta matata Ammy ban taba tunani ba, ko da ace Hurriya tana aibu na yi tunanin zaki boye saboda kar na ji raina ya bace, amman ke da kanki Ammy kike yakar yarinyar nan? Kina fadar yadda zaki yi idan aurena ya zo yau duk kin kawar da wannan saboda Hurriya ce, a gabanki abokina yake zagin matata saboda ya samu fuska a gurinki Ammy, kina fada min irin kaunar da kike min kina gudun bacin raina amman yau babu wannan... ”

Tuni hawayen Ammy suka kafe a idonta ganin ďanta yana kuka, bakinsa na furta kalaman dake kama kwakwalwarta.

“Kuka kake yi Jamal...? Hawaye kake zubarwa?”

Ya kawar da fuskarsa gefe.

“Ammy ya yadda kika san zuciyata, tun da kika ga na shanye duk abun da aka yi ma Hurriya na kaunace ya kamata ki fahimci yadda tasirin sonta yake da karfi a zuciya, Ammy a yau zan miki rantsuwa da Allah na tabbatar miki da abun da kike da muradi... Wallahi Wallahi Wallahi Ammy idan fasa auren nan ne farincikinki, zan hakura da Hurriya Wallahi ba zata tare a gidana ba a matsayin matata zan hakura da ita! Amman tabbas zan roko Allah ya dauki rayuwata, na fi sha'awar mutuwa fiye da rayuwa babu Hurriyya a matsayin Matata...! Ko da na mutu zan tafi da tunanin wannan abun... ”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Ammy ta furta tashin hankali na kwance a idonta ta rika fuskar Captain da duka hannayenta sannan kamin ta tashi ta rumgume danta tilo daya tana hawaye.

“Abun be kai can ba, be kai can ba...”

Ta dago ta kalli fuskarsa ta sake rumgume danta.

“Wannan irin so da kake yi ma yarinyar Allah yasa ta zame mata ƴa, wannan son ya ba ni tsoro”

Tsoro ba a furucinta kadai yake ba har a cikin zuciyarta yake, domin Captain be taba zaunawa da ita gaba da gaba ya karabta mata soyayyar wata mace da karfi kamar yadda ya yi mata a yau ba, a yadda zuciyarsa take idan ya rasa zai iya jefa kansa a cikin wani hali wata kila fushinsa da zuciyarsa su karu har aikata abun daba shi ke nan ba, wata kila kuma idan yayi addu'ar ya amsa masa ya tafi ya barta da bakincikin rasa ďa ďaya tilo da Allah ya bata, da bakincikin kin abun da yake so, idan kuma hakan ta faru ta san ba zata yafewa kanta ba, Daddy ma ba zai daina ganin bakinta ba.

“Ni ban yi mata tsanar da zaka roki mutuwa akan rayuwarka ba, ni mai kaunar abun da kake so ce kawai dai ina ganin rashin dacewa ne akwai, ni mahaifiyarka ce Jamal ba makiyiyarka ba”

Captain yayi murmushi yana jin dadi a zuciyarsa, daman ya san Ammy ba zata iya zabar mutuwarsa da rayuwarsa.

“Ina son ki Ammy ina sonki sosai, shiyasa yanzu da kika ji yarinyar nan farinciki ya rage, saboda baki goyon bayana kuma babu wani annashuwa da murna da kike na auren, wata kila ma jira kawai ake na yi auren a karbi rayuwata maybe shi ne last abu da zan yi a rayuwata, wata kila zan tafi ne kawai na bar muku yarinyar nan, ko yanayin aikin da nake ma rayuwata kullum a cikin hatsari take komai zai iya faruwa....”

“Wane irin magana ne wannan?”

Ta daka mishi tsawa.

“Wane zance kake haka? Me yake damunka? Ina ce komai ya wuce ai, me kuma ya sake dawo da zancen mutuwa?, bana son wannan maganar karka sake”

Ya amsa mata kai yana murmushi.

“Ba zan sake ba Ammy”

Ya kwanta a jikinta kamar yadda yake mata a lokacin da suke cikin Kaduna idan yana gida tare da ita, babu ruwansa da girman da yayi kwantawa yake a jikinta yayi ta zuba shagwaba, kamar wani yaro. Kansa ya shafa yana kallonsa ita kam ba zata iya jurar rasa danta ba, zata haka for now domin ta san gaba ba zai dade ba, yadda yake da fushi ma wata kila da kansa zai zo ya fada mata ya saki Hurriya wata rana, domin zuciyarsa ba ko wace mace zata iya zama da shi ba, shi ma ba zai jure wani abun ba. Dan haka zata aje makamanta a gefe ta saka musu ido, gudun kar ta rasa ďanta kuma ya dauke ta a matsayin makiyiyarsa. Wannan ne abun da ta ayyana a ranta.

HAJIYA KALTUME POV.

“Daga min mana Ruma kafar nan ciwo fa take min amman sai ki rika dora min kanki nan kamar baki tausayina, gashi idan ina tafiya kamar zan yi dingishi haka nake yi, ina tunanin Egypt zan tafi a duba min ita, tun da nan sun gagara gane komai”

Ruma ta tashi daga kwancen da take a jikin Hajiya Kaltume ta kalli Khairy dake zaune tana gyara akafaitar.

“Yau ke da kanki kike gyara kafarki?”

“To ya zan yi? Ni tsoron fita nake yanzu, mutane za su fara kallonka saboda video nan da ya fita wata kila ma har a nuna ka ace ita ce”

Khairy ta fada kamar zata yi kuka. Hajiya Kaltume ta ce.

“Ke daina damar da kanki, abun ne dai kin riga min yi da kin yi shawara da ni da ba zaki aikata ba, ku yara ne ba ku san bandar kasa ba, sai ku rika gaggawa kuna son aikata abun da zai kaiku ya baro, gashi nan duk kin bi kin rame, kin tsallawa a madadin ita aka yi ma ta shiga damuwa gashi nan ma shirye shiyen aurenta kawai ake yi, ni damuwa ke damuwa abu ya taru yayi mana yawa, ni na rasa ina ma zan saka kaina na ji sanyi”

Hawaye ya zubo a idon Khairy.

“Da na san haka abun nan zai zama Wallahi ba zan aikata ba, kuma Wallahi ba ni na yada hotunan ba, ni dai kawai na nasa barazanar zan yada ne, shi ne yayi min shairi yace ni na aikata, gashi ya fadi zancen fyaden nan kowa ya ji, na muzanta Hajiya na ji kunyar duniya”

“Ba ke kadai ba, abun ya shafi kowa ai, da murna nake da Hurriya ce ta janyo sai gashi reshe ya juye da mujiya, ga abokiyar taya ni yakin tana can babu lafiya, ni na rasa ma ina zan kama, abubuwa sun tsaya min cak...! Ina tunanin shiryawa zan yi na tafi gurin Yaya Altine...”

Bata rufe zancen ba Alhaji Musa ya turo kofar falon ya shigo da sallamar fuska kuma babu annuri. Hajiya ta amsa Khairy ta sauke kai kasa tana jin kunyar hada ido da kanen mahaifin nata, ruma kuma ta gyara zamanta tana masa sannu da zuwa sai ya amsa yana zaunawa.

“Yauwa... Sannu dai Hajiya barka da gida”

Hajiya Kaltume dake jin kamar ya zo yayi mata albishir ne na ganin ya daidaita tsakaninta da Appa ta amsa masa tana murmushin karfin hali.

“Lafiya Kalau Alhaji Musa ya yaran?”

“Alhamdulillahi...”

“Maa Sha Allah...”

Sai kuma shiru ya biyo baya tun bayan da Hajiya Kaltume ta yi magana ta karshe. Khairy ta daga kai kadan ta kalleshi ta ga ita yake kallo sai gabanta ya fadi, ta mike tsaye zata bar falon ya katse shirunsu ta hanyar dakatar da ita.

“Zauna Ummulkhar maganar ai duk a kanki ne... Wato Hajiya dazun ni da Yaya mun tafi gidansu Hajiya Iyami, to ni ina daga waje saboda na dan ba su guri ne su gana, sai gashi ya fito yana fada min iyayen yaron nan ne suke son ganinsa....”

Daki daki Alhaji Musa ya jera musu abun da ya faru har zuwa karshe.

“A takaice dai yanzu shi yaron yace baya ciki idan ta samu wani ta yi aurenta”

Khairy ta fashe da kuka mai karfi daman ta saka ran haka, ganin yadda yaki ya daga wayarta tun daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau da aiko musu da mummunan sako, Ruma ma kallon Khairy take cike da tausayinta domin ta san abubuwan za su mata yawa ne. Fasa auren na Khairy da aka yi ba daga hankalin Hajiya Kaltume ya jefata a tunani ba kamar jin cewar Alhaji Musa ya bawa Appa da Amma guri domin su gana sai ta ji kamar an watsa mata garwashi a zuciya.

‘Su gana kamar yaya? Daman ganawa suke a yanzu? Ko da yake ga zahiri tana ganin shirye shiyen auren Hurriya da ake sai dai ta ji labari yadda aka yi ko za'ayi a gurin ďanta Yasir idan ta shinshini gulma, be bawa Momy ta yi komai ba ita da take karkashinsa a yanzu balle kuma Ita da igiyar aure ta raba, yanzu hankalin Appa ya koma gurin Iyami kenan? Gashi har da zuwa da kanensa ko dai auren zai maida? Tun da yanzu ta samu lafiya kamar yadda ďanta ya fada mata tun kwanakin baya? Ita kam abubuwa sun ribchabe mata a yanzu komai ya shige mata hudu...’

Bata gama sakar zuci ba Alhaji Musa ya kira.

“Hajiya kin fahimce zancen nawa?”

Sai ta kalleshi kamar wata yar marainiya idonta na cika da hawaye, ta rasa laifin me ta yi abubuwa suka zo mata a haka.

“Na fahimta Alhaji Musa, to me zan ce kaddarori ne gasu nan sun rufe mu..”
Chapter 115 · 0% Book details