← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 133

Sashe 11

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta daga masa kai, sai da ya wuce sannan ta kwankwasa kofar part din kamar wata bakuwa bayan ba haka ta saba ba, idan zata shiga bangaren Appanta sai dai ta tura ta shiga da murnarta tana rangada sallama. Sai da ta yi knocked sau uku sannan ta tura kofar falon ta shiga, sanyin ac ya fara yi mata maraba da zuwa, kaminnta juyo muryar mahaifinta a dayan falon da alama waya yake, babu komai a hannunta sai carbin Amma da ta dauko, tufafinta ma sai daga baya za a dauko mata ko kuma ta yi using wadanda suke gidan na bangaren Momy. Hawaye na sauko mata kamar ba gobe haka ta shiga karamin falon tana ta son ta bude baki ta yi sallama amman ta kasa. Appa na ganinta a take annurin dake fuskarsa ya gushe kamar wanda yayi arba da bakin maciji, a take ya yanke wayar da yake ya mike tsaye ya nufota yana fada.

“Ya aka yi? Kin dawo kina ta yi ma mutane kuka mutuwa aka yi? Ni ba dan Kaltume ta matsa ba ai sai ki zauna can a gurin uwar taki”

“Appa”

Ta furta tana kallonsa gilashin dake mata garkuwa na daf da faduwa. A madadin ya amsa sai yace waye bana son jin muryarsa ba ke ba, a take korata ya saka ta gaba.

“Muje can bangaren Nafisa tafi tafi”

Ta tsaya a gurin tana kallonsa kamar hoto har ya iso, ganin ba tafiya zata yi ba ya saka shi fisgar hannunta ya wuce gaba ya hanyota sai kallonsa take har suka isa cikin falon Momy ya sannan ya saki hannunta. Kamin ya ce komai Momy ta aje plate din doyar dake hannunta ta rafka salati.

“Haba Alhaji, ina laifi ka barwa Iyami yarinyar tana ganinta tana jin sanyi? Ni dai tsakani da Allah hankali ya fi kwanciya yarinyar ta zauna a gurin uwarta”

Ita ma kamar Appa na jiranta sai ya rufeta da fada.

“A nan nake son ta zauna, a nan zata zauna ke kanki gurin da na ga dama zaki zaun balle kuma ita da take yata, karki sake fada min abun da ya kamata na yi, ba shawararki nake nema ma”

Tabe baki ta yi bata sake cewa komai ba har ya fice, sannan ta ce

“Ni ma dan an rasa ya za'ayi da ni ne, na cika na make gurin kuma sai hakuri Wallahi, ni da zai maida Iyami ki koma can gurinta ya fi min kwanciyar hankali, ina zan iya da rikon yayan wasu yayan da idan suka girma suka samu arikin uwarsu za su nema”

Hurriya dai tana tsaye a gurin da Appa ya barta ta kasa matsawa ko'ina sai hawaye take. Mahaifinta ya canja mata, ta rasa dan'uwanta kuma ta rasa mahaifiyarta a kusa da ita.

“Lafiya kika tsaya nan kika zuba min ido? Mahaifinki ma baki da amfani a gurinsa yanzu balle kuma ni, wuce ki tafi dakinki tun da an kawo min kaya ya zan yi, Iyami ta haifa mana ta tafi ta bari”

Huriyya ta dauke kai da sauri ta fara tafiya, sai kuma Momy ta kirata.

“Hurriya”

Ta juyo a hankali ta kalleta ta kasa amsawa har lokacin hawaye take.

“Zo ki zauna yi hakuri kinji”

Hurriya ta dawo ta zauna saman kujerar dake dama da Momy.

“Gaskiya dai Alhaji ya ci amanarki Wallahi, ni ai ko da bala'i sai na karbi yayana, ko da yake Iyami ba zata iya ja da Alhaji ba, ta ina talauci zai ja da arziki, amman dai gaskiya be dace ya rabaki da Iyami yanzu ba, ai sai tunanin ya hade miki ga na dan'uwa ki kamu da hawan jini da kurciyarki, kai Kaltume bata da imani, haka fa ta raba Sapna da ubanta, Sapna bata isa ta tako garin nan ta ce zata zo gurin ubanta ba, tana can kauye cikin talauci shi kuma ya kyaleta... Hmmmm”

Ta mike tsaye tana kwalawa mai aikinta kira.

“Bilki”

Tsohuwar ta fito da gudu daga kitchen, daman haka take da yan aiki idan tana falo sai dai su boya a wani guri bata zama daki daya da su, idan har ka gansu a falo to tana dakinta ne ko kuma ta fita.

“Hajiya ga ni”

“A dauke plate din nan kuma ga yar Iyami nan idan zata ci abinci a zuba mata”

“Toh Hajiya”

Tsohuwar ta dauke plate din sannan ta kalli Hurriya dake zaune.

“Hurriya a zuba miki abinci?”

Hurriya ta girgiza kai alamar aa, Momy tabe baki ta dauki wayarta.

“Dan kan masa in ji sure, cikinki ko na wani, kin san dai ba rarrashinki zan yi dan ki daina kuka ko ki ci abinci ba, ina da tausayi da zuciyar imani amman laisa son dan wani kamar nawa kam karya haram babu boye boye ba munafurci, shiyasa ni na fi sha'awar uwarku ta dawo ta rike yayanta”

Tana fadan tana hawa sama har ta haye ta shige dakinta, Mai aikinta kam tuni ta san inda dare yayi mata. Hurriya ta bi ta kallo har ta haye stairs din, ji ta yi kamar ace wani na nan ta fada jikinsa ya rumgume ta yi kuka ammab babu wannan damar, saukowa ta yi daga saman kujera ta zauna kasa sai ta dora kanta sama kujera ta takure guri daya. Ta rufe ido hawaye na sauko mata. After like 30min ta ji an zungureta sai ta farka da sauri gilashin idonta ya fadi da sauri ta dauka ta saka ta gyara mayafin abayarta ta kalli Musib dake tsaye kanta.

“Miye na yi ma mutane bachi a kujera kin wani takure salon wani ya shigo ace ke ce marar gata a gidan ke ga munafuka, wato kin dawo babu zaman lafiya, mun rabu da Hamad ke kuma zaki kirkiri mugun abu ko?”

Kamar wani mace haka yake fada da ita yana gautsina fuska, gently ta mike tsaye domin ita ma bata san bacci ya dauke ta sai da ya tasheta. Tafiya ta fara yi ta haye sama ta dade a tsaye tana kallon kofar dakin Hamad tana jin kamar idan ta tura zata ganshi kwance ya ba kofar baya kamar yadda ya saba kwanciya. Wani hawayen ya sake cika idonta wani abu mai kama da dutse ya tsaya mata a tsakiyar zuciya ya mata nauyi. Cikin karfin hali ta kai hannu ta tura kofar dakinta ta shiga sai da maida kofar ta rufe ta jingina jikin kofar ta rumgume hannayenta not knowing what to do ita dai ba kuka take ji ba a yanzu, hawaye ne kawai ke mata zuba, tunanin dake mabanbantan duniyoyi ya hade mata guri daya, idan ta tuna Hamad ta tuna Amma, ta tuna Appa. Jin ta yi an yi knocking kofar dakin wani abu mai kama da tsoro ya fisgeta ta tashi tsaye da sauri jikinta na rawa ta yi baya tana kallon kofar, Namra ce ta turo kofar ta shigo da far'arta.

“Hurriya kin dawo”

Kamin ta rufe baki Yasir ya shigo cikin yanayi na damuwa yana kallonta.

“Hurriya”

Ta kasa amsawa Namra balle Yasir da ya shigo bayanta, ta hade yawu da karfi tana kallonsu. Yasir ya nufi gadonta ya zauna ya rasa me zai ce mata shi kansa be jin dawowarta gidan a yanzu mafita ne a gareta, babu yadda be yi ba wajen ganin ya fahintar da Hajiya Kaltume akan ta hana Appa dauko ta amman ta kasa fahimtarshi.

“Hurriya zauna”

Ta zauna a gurin kamar wata wadda tunani ya birkicewa kwakwalwa. Namra dai ta tsaya jikin kofar ita ma tara ran duk babu dadin ganin yar'uwarta cikin damuwa.

“Hurriya ki yi hakuri dan Allah, idan kina kukan nan sai ki saka kanki a damuwa”

Yasir ya daga ma Namra hannu alamar ta daina maganar sai ta yi shuru ta juya ta fice daga dakin, dan zumudin da ta zo da shi na murnar dawowar Hurriya sai ya gushe.

“Hurriya kina son zama nan ko kin fi son zama gurin Amma? Idan gurin Amma kike so zan mu tafi tare da ni dake mu yi ma Appa magana, idan be amince ba sai mu fadawa Hajiya Binta”

Ta girgiza kai alamar bata aa.

“Kina son zama nan din?”

Ta daga masa kai.

“Shi ke nan zo ki kwanta, kin yi sallah ko?”
Chapter 11 · 0% Book details