← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 133

Sashe 94

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ka kawar da komai a ranka, daman shi aure ya gaji haka, a tsaba kuma a shirya ko a yanzu dare be maka ba, lokaci be kure ba zaka iya gyara inda ka yi kuskure ka share inda ka bata, kar wannan jin nauyin ya hanaka sanar da yarka Hurriya cewar ka bada aurenta a yau, kai da kanka nake son ka fada mata wannan”

Ya amsa mata da kai sannan ya mike tsaye yana hade rigarsa.

“Zamu jiraki a waje Hajiya sai ki shirya mu tafi”

“Toh...”

A waje suka jira Hajiya ta fito tana rike da sadakin jikarta, ta shiga baya Appa da Yasir kuma suka shiga gaba. A motar Hajiya sai godiya take yi ma Allah na yadda ya kawo auren Hurriya a kusa kuma da mutumen da ba ayi tsammani ba, Appa kuma fargaba da kunya na lullube shi a yayin da Yasir yake kara kusanta gidansu Gwaggo.

“Ni na manta ban tambaya ba, yaron dai yana da kirki ko? Murna da farinciki sun mantar da ni wannan”

“Ba shi matsala Hajiya na san shi, yana da kirki kuma babu wanda zai fadi sherinsa, Hurriya ta yi dacen miji fatan mu dai Allah ya bata lafiya kuma ya basu zaman lafiya”

Hajiya Binta farinciki sai ya kara ninkuwa, ta kara yi ma Allah godiya.

HURRIYA POV.

“Wannan jaraba da kuke ta fadawa Allah ya yaye muku, idan wannan ya wuce sai kuma wani ya zo, ke kin tashi baki ya bude ita kuma ido ya rufe”

Gwaggo ta kalli Hindu wanda ke kallon Hurriya tana lalaben gini har ta iso gurin da Amma take zaune tare da Gwaggo da kawar Amma wato Hindu ta zauna.

“Abun da Allah yayi annabi sai ceto, likitocin sun ce wai damuwarce ta taba mata ido, amman ni ban yarda ba na fi zaton wani aikin ne aka yi mata idon ya rufe gaba daya, gashi an yada hotunanta kin ga shikenan an gama da rayuwarta, ba ido balle ta yi karatu ta gina kanta kuma babu wanda zai aureta a haka”

Hindu ta rafka uban tagumi.

“Oh Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, wannan mugun kishi da me yayi kama? To ko ita ma za mu nema mata taimakon a gurin da aka nemawa Amma? Tun da gashi dai mun fara ganin haske”

Amma ta kama Hurriya ta kwantar da ita a cinyarta hawaye na sauko mata.

“Mun dai ga haske Hindu, Wallahi ban dauka zan iya kara yin magana ba, na dauka kalmaina sun kare a duniyar nan, ina kallon abu na zan iya cewa a bani ba, ina da maganganu da yawa a bakina amman ba zan iya furta ko daya ba, bana iya motsa jiki bana iya komai, amman ki duba yanzu magana fa nake yi, bana jin karfi a jikina sosai amman Alhamdulillah na gode Allah”

“Shi ma duk zai bari da yardar Allah, lafiya daman da rarafe take shiga a jiki har a tashi tsaye, ciwo ne yake jefar da mutum farat daya”

Cewar Hindu. Kamin su daga kansu gaba daya su kalli kofar gidan, Hajiya Binta ce ta shigo Appa yana bayanta sai Yasir a bayan Appa.

“Sallamu Alaikum”

Gwaggo da Hindu suka amsa mata, Amma kuma ta sauke kai kasa tana nadamar kallon Appa da ta yi kamar wanda ta yi arba da bakin maciji.

“Maa Shaa Allahu, Iyami ce a waje? Haka nake so lafiya ta samu”

“Alhamdulillah, Rukkaya dauko tabarma ki kawo ma baki”

Gwaggo ta amsa tana bawa Rukkaya umarni. Appa ya kasa daga ido ya kalli kowa kamar wanda ya aikata abun kunya. Rukkaya ta fito rike da tabarmar ta shimfida kusa da wanda Amma take zaune. Hajiya ta fara zaunawa sannan Appa Yasir, daman haka tarbiyar take, sai iyayen sun fara zama ake zama, idan kuma suna zaune ba ka tsaya a kansu ba sai dai rankwafa ko na zauna a kasa.

“Jama'a ina kwananku ko wuni zan ce domin dai yanzu ai 12pm ta yi”

“Lafiya Kalau Hajiya ya gidan”

Gwaggo ta amsa ba yabo ba fallasa. Appa ma ya mikawa Gwaggo gaisuwa, ba dan yana a gaban Hajiya Binta ba da kuma tunanin dalilin zuwansa wata kila da ba zata amsa gaisuwar Appa ba.

“Lafiya Kalau”

Amma ta daga kai ta kalli Rukayya dake zaune ta ce.

“Dauko min hijabina Rukayya”

A rude Appa ya dago kai ya kalli Amma, Hajiya Binta ma ta kalleta Yasir ma kallonta, dukansu sun yi turus suna mamakin jin furuci ya fito daga bakinta.

“Iyami kina iya magana yanzu?”

“Allah ya nufa Hajiya”

Amma ta guntun murmushi tana amsawa Hajiya Binta dake rike da baki.

“Allah da iko kake, kai Alhamdulillah yau farinciki ya mana yawa”

“Amma....”

Yasir ya kirata sai ta kalleshi ta yi murmushi ta amsa.

“Na'am Yasir”

“Alhamdulillahi”

Wannan karon Appa ne ya jaddada godiyarsa ga Allah yana kallon Amma, irin kallon da ya dauki shekaru be yi mata ba, nadama da damuwa bayyane a fuskarsa karara. Rukkayya ta kawo Hijab ta mikawa Amma, sai Amman ta karba ta saka domin tana ganin Appa da Yasir ba muharramanta ba ne a yanzu.

“Hurriya ta so mahaifinki na son magana da ke”

Hurriya ta amsa kiran da Hajiya Binta ta yi mata ta tashi zaune, sai ta lalaba ta matsa gurin da Hajiya take ta zauna, Appa ya kai hannayensa ya kama nata hannayen ya juyo da ita ta fuskance sai ta nade kafafuwanta irin zaman da musulunci ya koya mana yayin da zamu ci abinci, wato ta nade kafafuwanta tana fuskantar mahaifinta.
A lokacin da Appa ya kalli yarsa sai tausayinta da kaunarta da kuma kunyarta a lokaci daya mamayeshi. Ya sauke ajiyar zuciya sau uku sai a hudu ya samu damar hada kalmomin da zai gamsar da yarsa da su ya hada guri daya ya fara magana.

“Hurriya na san kin san cewar ni mahaifinki ne, a cikin abubuwan da Allah ya dora min nauyinsu akwai ciyar da ke da shayar da ke da tufatar da ke da halak, idan kuma kin kai munzali Annabi yace na zaba miki mijin na kwarai wanda na yarda da addinsa da dabi'arsa kuma mai abun yi. Ban sani ba ko na kokarta a tarbiyarki, wata kila na yi jarumta a ciyar da ke da tufatarwa, ba zan gane hakan ba sai ranar alkiyama, a cikin kokarin sauke nauyin da Allah ya dora min, na aiwatar da wani a yau. Yake ƴata yau kina zaune a gabana ne a matsayin matar wani, wanda cin ki da sha da tufatarwarki za su koma a kansa, a yau kin shiga sahun manyan mata, a yau kin tashi daga budurwar kin zama matar aure, daga yau ladarki zata riɓanyya har zuwa lokacin da za ki bar duniya, neman aljannarki a yau ya sauka daga kan kafata ya koma karkashin kafar mijinki.... A yau na aurar da ke Hurriya...”

Ta daga kanta ta kalli gurin da take kyautata zaton fuskar Appa take, bata iya ganin komai saboda rashin masoya biyu, wato idanuwa, amman a haka zuciyarta take ayyana mata yadda fuskar mahaifinta take. Bata ganin komai sai duhu, sai dai makanta bata hana idanuwanta suke zubar da hawayen da tun da Appa ya fara magana suke mata zuba. Appa ya dauki sarkar dake gaban Hajiya Binta ya dora a cinyoyin Hurriya.

“Wannan sadakinki ne... An umarci iyaye su bawa yarinya sadakinta domin nata ne... Wannan naki ne Hurriya...”

Hurriya ta kasa cewa komai bata jin komai sai _A yau na aurar da ke Hurriya_ haka kalmar ta yi ta maimaita kanta a kunnenta kwakwalwarta na juya kalamin.

“Aure....”

Amma ta tambaya domin Mamaki ya hana Gwaggo cewa komai.

“Hajiya ban fahimta ba, wane irin aure kuma? ”

“Ki kwantar da hankalinki zaki fahimta”

“Ban gane na kwantar da hankalina ba, taya zai shigo cikin gidanmu kai tsaye ya fada mana ya aurar da Hurriya? Saboda ya mayar da mu talakawa? Ni ba ni da hakki akan Hurriya kenan? Wane irin magana ne wannan?”

“Kin fini hakki akanta Iyami, Annabi ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci Uba... Ban aurar da ita yau saboda na wulakanta ki ba, ban aikata hakan da wata manufa ba sai dan ina ganin hakan ne abun da ya cancanci ko wane uba na gari aikata, na aurar da ita ne a inda nake kyautata zaton za mutunta a rike ta amana, Iyami ki yi hakuri tabbas na yi kuskure ban nemi shawararki ba na aurar da Hurriya”

“Wa ka aurawa ita? Saboda abun kunyar da ya faru ne ka yanke shawarar aikata haka?”

Gwaggo ta tambaya a fusace. Appa ya tausasa murya ya ce.

“Aa Wallahi su suka zo neman aurenta da kansu, sunan yaron Jamal da ne ga Nafisa, dan wajen Alhaji Aliyu Turaki...”

Hawaye ya subucewa Amma.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, me ya sa zaka aurar min da ya a inda ba a san darajar mutane ba? Macen da bata son hada hanya da talaka? Zaka dauki Hurriya ka jefa a cikin danginta? Yarinya karama ta kafa fuskantar irin bala'in da na fuskanta a gidanka, da na san haka rayuwa zata zama gaba daya Wallahi da ban aureka ba, amman kaddara ta yi min zanen da ban isa na goge ba”

“Subhanallahi Subhanallahi Subhanallahi”

Appa ya maimaita har sau uku sannan ya ce.

“Na san ban kyauta miki ba Iyami, amman ki tausasa ko dan yaran nan”

Amma ta masa wani kallo na takaici da bakinciki.

“Yara? Wadannan twins din da aka haifa ka kasa zuwa ka tara hannu ka karba? Ko kuma ďan da aka kama ka ce ba zaka bada kudin fansar sa ba! Sai da na hada komai da na mallaka na bada, sannan Hajiya Kaltume ta baka umarnin biya? Ko kuma Hurriyar da ka juyawa baya?”

Appa ya kasa amsawa ya sauke kansa kasa yana mai jin kunya da nauyin abun da ya aikata.

“Bari na fada maka da bakina ka ji, yata bata auru ba, ba zan bada ita a inda za a wulakanta ta ba, abun kunyar da aka yi mata kazafin aikatawa ni zan iya rumgumarsa”

Ba tare da Appa ya dago kai ba ya ce.

“Iyami karki furta kalami cikin fushi”
Chapter 94 · 0% Book details