← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 133

Sashe 113

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aa ina wani guri mai muhimmanci amman dai yanzu zan tafi gida, mu hadu a can”

Ya katse wayar ya saka aljihun gaban rigarsa da babbar riga ta tare sannan ya kalli Amma ya ce.

“Hajiya zan tafi gida yanzu, daya daga cikin iyayen maneman auren Khairy ne ya kira ni a waya, ya ce yana bukatar ganin a zai same ni ni kuma na fada masa mu hadu a gida zai fi, tun da ga Alhaji Musa ma a tare da ni sai mu ji ko minene”

“Allah yasa mu ji alheri”

“Amin, kuma dan Allah ki fadawa Bappa ba sai ayi min godiya ba, kar ya kira ni na ki dagawa yayi zaton wani abu, Wallahi godiyar ce bana bukata, kuma ina jiran kiranki idan an saka ranar tafiyar kar lokaci ta matse”

“In Shaa Allahu”

Amma ta amsa da murmushi, shi ma murmushin yayi.

“Na gode uwar biyu”

Ya fada sannan ya fice ransa fes buk'atarsa ta biya, hakarsa ta cin na ruwa. Daga gidansu Amma kai tsaye gidansa ya nufa tare da Alhaji Musa yana bawa Alhaji Musa labarin irin biyayyar da Iyami take masa wanda abu ne da duk wanda yake kusa da shi ya sani. Yayi mamakin tarardar mutanen da ba zai iya kiransu da baki ba a gidan domin shi da su suna kusan zama surukai ne a matsayinsu na iyayen Fadeel. Tun a waje Appa ya gaisa da su sannan yayi musu iso suka shigo cikin falonsa suka zauna tare da shi, ganin yanayin fuskarsu dake dauke da damuwa ya saka Appa be yi wata hubbasa gurin ganin an kawo musu wani abun tabawa ba, domin alamu ya nuna ba farinciki ne ya kawo su ba, sai kishiyarsa.

“Toh Allah dai ya sa lafiya, irin wannan ziyara da rana tsana ba tare da wani abu ba”

Wanda ake kira da Alhaji Hafeezu ya yi gyaran murya ya kalli Appa cikin kyautata ladabi ya ce.

“Alhaji lafiya amman ba lau ba, wato maganar ce da nauyi shiyasa na ce zamu sameka a inda kake ban so mun zo nan gida ba sai dan ka bukaci hakan, domin ka yi mana karamci da hallacin da be dace ace mun furta wata magana makamancinyar wannan ba a gidanka”

Appa yayi murmushi mai cike da takaici.

“Karka damu Alhaji Hafeezu daman na saka tsammanin faruwar hakan, tun a lokacin da abubuwa masara dadi suka faru a gidana, na shiryawa fuskarta ko wane kalar kalubale, kuma na san zancenku ba zai wuce ku ce Fadeel ya janye daga zancen neman auren Khairy ba?”

Sai duk suka kallo juna ganin yadda yayi saurin harbo jirginsu. Appa ya sake fadada murmushinsa.

“Karku ji komai, yayi abun da ya dace kowa yana son auren yar kwarai, kuma ita kanta Khairy ba wai bata da tarbiya ba ne, kaddara ce dai irin wanda ta saba fadawa bawa, shi kuma yayi abun da yake ji ya natsu da shi ne, babu ta inda zai zama mai laifi a gurin kowa, ni din nan ma mai shiga gaba ne a nema masa aure idan ya samu wata yar da yake so”

Appa ne mai magana Alhaji Musa kuma ya fara fada yana ganin kamar hakan be dace ba, Fadeel din be rumgumi kaddara ba.

“Kayya dai assha dai..! Ba haka aka so, amman yara ne basa jin shawara kuma basa jin maganar manya na su hangen dabam yake, ya same mu sa zancen ne kuma yace shi ya janye, mu kuma muka ta inda aka hau ice ta nan ake sauka, da ace ya janye jikinsa kuma baka ji wani bayani daga garemu ba kamar hakan be dace ba, a matsayinmu na iyaye”

Appa ya sauke ajiyar zuciya daman ya san za arina, sai dai kuma jin albishirin be masa dadi ba, ko kadan domin yana neman mai kwashe masa Khairy ne a yanzu da shi kansa baya sha'awar ganinta.

“Yaro yana da gaskiyarsa kowa yana aikata abun da yake jin natsuwa da shi ne, a addini ma ance ka bar abun da kake kwankwato zuwa ga wanda baka yi, ba wani abu ba ne”

“Mun gode Alhaji mun gode da Fahimta”

Alhaji Musa zai sake magana Appa ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu. Suka tashi suka fice cikin kunyar sakon da suka isar.

“Alhaji be kamata ka yi haka ba, taya zasu same ka har gida da wannan maganar?”

“Sun yi abun da ya dace Alhaji Musa, haka ake son iyayen na gari su kasance sun warware ne saboda su suka nema masa aure, to da ace anyi tsammanin shi zai aureta ko kuma mu ji shiru a kara tun wuri su sanar mana, kuma yana da gaskiyarsa babu namiji da zai son auren mace kamar Khairy saboda abubuwan da aka fada ta yi ma yar'uwarta ta jini, balle kuma ga maganar Fyade ta shigo ciki kuma ka san yadda society mu suke daukar abun da girma”

Cikin takaici da Allah wadai Alhaji Musa da ya kasance kane ga Alhaji Haruna ya ce.

“Ummu Khairy bata kyautawa kanta ba, bata kyauta ba ban jidadi ba ta bata maka suna ta lalata rayuwarta ina amfani haka”

“Idan ma akwai amfani a yanzu ta gani idan ma babu kuma ta gani, Allah ya shirya mana zuria”

“Amin, yaran ne yanzu hankalinsu da tunaninsu sai ka rasa ina yake zuwa, ita na Hurriya saboda bata aikata ba ne Allah ya dubeta ya kawo mata wannan yaron ban da haka ai da sun zame maka su biyu abun babu dadi”

“Ko su goma suka zama zan iya dauka Alhaji, yadda kaddara ta rubuta ai haka za a wanke a sha, Allah baya aje kayansa ga wanda ba zai iya dauka ba, jarabawa ce ta rayuwa Alhamdulillahi”

Appa ya fada cikin tsananin bakincikin da be isa ya boye a zuciyarsa kadai ba har sai da fuskarsa ta bayyana.

CAPTAIN JAMAL POV.

“Akwai wani abun da zan iya taimaka maka da shi ne?”

Captain ya girgiza kai ya kwanta jikin kujera kamar mai jin bachi.

“Aa anyi komai, daman ba wata hidima za'ayi ba, Ammy ta hana taron biki ta hana komai ka ga babu bukatar yin wani abu”

“Amman dazun ina jin ka a waya da Abdulkareem kake masa zancen gyaran gida”

Captain ya zaburo masa da fada ganin yana son matsa masa ya shigar masa hanci.

“Already ina da gidan a nan da Kaduna Salim ka sani, na hannata masa komai ne saboda yayi kwangilar kula da komai idan akwai abubuwa da za a canja ko a saka yayi saboda sabon gidaje ne, kai kuma ba sana'arka ba ce to miye abun takuwara dole sai ka shiga ciki?”

“Babu Allah bada zaman lafiya”

Salim ya fada a fusace shi ma ya mike tsaye zai fice Ammy ta dakarta da shi.

“Salim karka fita dan Allah karka yi fushi, na san halin Captain ba tun yau ba, kar abun da yake yi a yanzu ya dame ka, mu kan mu tarewar da muka yi a wannan gidan na dole ne, na sani yaushe rabon d mu zo garin nan mu yi kwana uku ma amman gashi yau har mun tare a gidan nan saboda wannan auren, ka sha kuruminka idan zaka zai yi auren kwarai da za ayi taro ayi biki na gani na fada ku zaku yi komai”

Salim be fita ba, sai dai kuma be dawo ya zauna a inda ya tashi ba, yayi karfin halin cika fuskarsa da murmushi.

“Ammy har yanzu kina kam bakinki dai?”

“Shiyasa ai ban gayyaci kowa ba, sai idan zai sake aure”

Captain ya karkato ya kalli Ammy yana murmushi.

“Allah Ammy?”

Ammy ta masa banza ta cigaba da magana da Salim.

“Karka biye masa, kai ma kasan wanda ya ke a cikin hankalinsa ya san me yake yi ba zai auri yarinya irin Hurriya ba ko da kuwa an hada masa da buhun zinari da gidaje”

Salim ya saka hannunsa aljihu yana fadin.

“Gaskiya kam, Captain ka yi jihadi babba”

A take murmushin dake fuskarsa ya Captain ya gushe.

“Sosai kuwa, kuma kai har ka mutu ba zaka taba samu mace irin Hurriya ba, shiyasa abun yake ba ni dariya idan Ammy tace zan kara aure bayan domin bana jin zan iya ganin wata macen ta burge ni a yanzu, kuma ni ba zan auro macen da zata hana ni zaman farincikid Hurriya ba”

“Baka ma bukatar kara aure Captain ko dan gudun a goranta mata, ni ma kuma bana fatan samun Hurriya a yanzu na fi karfinta, kai ma kuma ba zaka iya nunawa duniya ita a matsayin mata ba, ba zaka gane illar hakan ba sai nan gaba”

Captain ya mike tsaye anger na dibanshi.

“Hey Mr Salim daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanina da kai, kuma karka kara fadar wata kalma marar dadi akan Matata, kawai kana kishi ne saboda ni na yi dacen auren Hurriya ba kai ba, dan haka na datse alakarmu daga yau kar ma wata rana ka ce zaka shiga gidana ka ga Matata”

Salim yayi murmushi mai sauti.

“Kishi? Shiga gidan ka na ga matarka? Macen da kowa ya gama ganin tsiraicinta kamin ka gani? Ita kake cewa kar na shiga na gani?”

Captain ya saka hannayensa aljihu yana jin kamar ace da bindiga a ciki ya raba kam Salim biyu a gurin.

“Gun?”

Salim ya saka hannunsa aljihu ya dauko bindigarsa ya aje kasa ya turowa Captain, mai nema a duhu balle an haska masa Captain ya duka ya dauki bingidar ya saita Salim da ita ya danna sai ta amsa da kettttt alamar babu albashiru a ciki. Ko da acw akwai alhasashen harbawa Captain zai yi because he  found  it  hard to control  hia anger. Ammy ta fasa ihu.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Jamal miye haka? Kisan kai zaka yi?”

Cikin takaici Salim ya kalli Captain ya ce.

“Da gaske zaka iya harbina idan akwai halsashe a ciki?”

Captain ya wurga masa gun din.

“Ga zahiri kana gani? And daga yau babu kai babu ni, and the rest ka jira na dawo bakin aiki”

Salim ya duka ya dauki bindigar yana bakincikin da suka saka idonsa tara kwalla.
Chapter 113 · 0% Book details