← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 133

Sashe 121

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka take sosai tana jin kamar ace adam din yana kusa da ita ta kashe shi ko ta rage zafi, can kuma ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta kama number Adam ta aika masa da sako.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[1/2, 7:00 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

5️⃣5️⃣

*Shafin nan sadaukarwa ce gareki  UMMU FAISAK my albasa my tomato my pepper, jikar Iya kawar Amo da Hajiya Kaltume. Alherin Allah ya kai miki har a gadon baccinki*

***    ***    ***

_Wallahi baka taba yin farinciki a rayuwarka ba Adam kamar yadda ni ma ba zan yi ba, ba zaka taba ganin haske ba, sai na bayyanama duniya abun da kake boyewa sai na hana ko wace mace aurenka, baka da zabin rayuwa daga yanzu har zuwa mutuwarka, idan ban auru ba ba zaka auru ba Adam..._

Yana gama karanta sakon ya dan dago ya kalli mutanen dake falon sannan ya maida kansa yayi mata reply.

_Mu zuba zuwa Khairy, ni da za a ga shege, kuma ni sai na auri macen da nake so nake ra'ayi amman ke ba zaki taba auren mijin da kike so ba, saboda kowa ya san me na yi miki kuma idan kika matsa asirin ba nawa kadai zai bayyana ba har da naki domin ke ma yanzu ya shafe ki kin ga sai mu yi jinya tare_

Yana bata amsa ya aje wayar ya cigaba da kallon tv rai a bace, Salim ya taso daga inda yake zaune ya nufo Adam.

“Ara min wayarka zan sauke app wayata ya ki sauke shi”

Without second though Adam ya mikawa Salim wayar ya tashi ya hanyar dakinsa. Salim ya zauna a gurin da Adam ya tashi yana.

“Akwai pin a jiki”

Adam ya dawo ya cire masa pin sin sannan ya shige dakinsa. Kai tsaye a Salim ya shiga whatsapp dinsa yana duba recent chat ne ga wani abun daga hankali ko bata rai ba, yana kokarin fitowa daga whatsapp din sakon Khairy ya sake shigo ta SMS.

“Mu zuba zuwa ni da kai shege ka fasa Adam”

Ya haka ya samu bin sakon ya karanta har wadda ta aiko masa da farko. Salim ya dan dago da mamaki kamin ya sake maida kansa, wannan ne karo na biyu da ya sake ganin wani abu da ya daga masa hankali a wayar Adam. Da kansa ya shiga dakinsa ya mika masa wayarsa sannan ya fito harabar gidan zuciyarsa na zafi. Domin ganin yakw yanzu ya zama loser shi ya fara son Hurriya amman abokinsa yayi masa overtaking duk kuwa da irin yadda aka bata sunan Hurriya,  it pain him yadda abokinsa yayi betrayed dinsa. Number Namra ya kira domin sauke mata haushin dake ransa.

Namra ta share hawayenta sannan ta kalli wayar dake gefenta ta dauka.

“Hello”

“Burinku ya cika? Kun nani Hurriya kun bawa wani?”

“Wane irin magana ne wannan? Wa yake murna da wannan auren ne? Kai kanka ka san Hurriya bata dace da Captain”

“Bata dace da shi ba ta aure shi? Na yi zaton ma kina can gurin raka amarya ai”

“Zan aje wayar idan baka da wata magana mai muhimmanci, ina cikin damuwa ba zan yarda ka kara min wata ba”

“Baki da matsala daman saboda ba ke kika rasa ba”

“Idan har da gaske kake kana kaunarta me ya hana ka fitowa ka aureta kamar yadda Captain yayi?”

“Captain ne silar lalata komai, a duk lokacin da na yi masa maganar Hurriya ture min maganar yake, saboda yana min kallon wani dan iska, daga baya na fahimci sonta yake shiyasa kansa yake yi ma campaign”

“To kai miyasa baka kirkiri taka Jam'iyar ka yi takara da shi ba? Da ka yi hakan da auren nan yanzu be faru ba”

“Ban yi tunanin zai yi jihadin aurenta a haka ba, na dauka zai hakura da ita ni da shi duk mu rasa...kuma na yi tunanin da gaske din ta aikata sai bayan da gaskiya ta bayyana abun ya zo min a wani iri”

“Ya fika kaunarta shiyasa ta tari yakin gaba da gaba, gashi kuma daga karshe gaskiya ta bayyana cewar bata aikata ba, ka ga ya ci riba, kark sake kirana Salim”

“Ni zaki ce kar na sake kiranki?”

“Ubana ne kai? Alakar dake tsakanina da kai saboda Hurriya ne, yanzu kuma ta yi aure dan haka babu sauran wata alaka  tsakaninmu, gaskiya Captain ya fada kana wasa da zuciyar mata shiyasa ko wace macen ka gani sai na nuna kana sonta, da farko ni daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, ai kara da ya hana ka aurenta hakan zai koya maka darasi”

“Ko kuma ya koya masa darasi ba, idan har aboki zai iya cin amanar abokinsa na kurciya ya karbe masa yarinyar da yake sannan ya datse alakarsu har ya nuna shi da bindiga kuma yayi masa barazanar rasa aikinsa me kike tunani? Dole shi ma hakki zai bibiye shi”

Namr taja tsaki ta yanke kiran. Daga ita har Salim Momy Hajiya Kaltume da kuma Khairy kwanan bakinciki suka yi a ranar duk saboda bikin Hurriya.

WASHE GARI...

Misalin karfe goma na safe Hurriya na kwace jikin mijinta yana gyara mata baki bayan sun gama cin abinci da breakfast da aka aiko musu daga Family house din su Captain.

“Tashi mu zagaya na fada miki yadda gidanki da dakinki yake”

Ta dan dago kamar bata son motsi, cikin siffar shagwaba da son kuka ta ce.

“Ni dai da ka bar shi, ba amfani tun da ba gani zan yi ba”

“Zaki taba ai, kuma idan ya bude zaki gani”

“Wannan idon abu ne mai wahala ya bude, Appa ya kashe kudi mai yawa akan ido, kullum kara rufewa yake ba budewa ba, yanzu kuma ya rufe gaba daya”

Ya dora gemunsa a saman kanta yana taba fuskarta.

“Zai bude Hurriya zai bude da yardar Allah... Ina ta shirye shirye akwai abun da nake jira ina son nan da dan lokaci zamu tafi Ethiopia akwai wani asibiti ido mai kyau zan saka a dubaki a can zasu Miki aiki kuma ina da yakinin Allah ba zai kunyata mu idonki zai bude”

Ta yi shiru tana sauraren yadda yake gangarawa da hannunsa zuwa gurin da bata tsammani.

“Idan kuma idon be budewa gaba daya fa?”

“Zai bude, ki daina fadar hakan ki yarda zai bude”

Ta zabura ta tashi zaune daidai da sauri ta ture hannunsa. Sai yayi murmushi ya cige baki ya kashe mata ido kamar tana kallonsa.

“Iya daga kafar na yau ne kawai, you better get ready for tonight...”

Ya rada mata a kunne sannan ya mikar da ita tsaye tana bata fuska kamar zata yi kuka, gaba daya sai ta ji tausayin kanta ya kamata.

“Kin tuna ranar da kike fada min na yarda dake na ce miki na yarda baki aikata ba, amman ban tabbatar ba, to anjima zan tabbatar”

Ji ta yi kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunya a yanzu ta fahimci inda zancensa ya dora tun a karon farko da yace mata zai tabbatar. Dariya yayi ya rumgume ta ta baya tana takawa a hankali har suka fita dakin. Kitchen suka fara yana fada mata abubuwan dake ciki wadanda aka siya gurin Khadeeja Candy, sannan suka fito suka shiga dayan dakin nan ma ya fada mata abun da ke ciki idan ya fada mata sai ya kai hannunta ta taba ta ji yadda yake da haka har suka fito harabar gidan nan ma ya rika fada mata yadda tsarinsa yake.

“Amman wata zata zauna da ni ko? Idan ka fita”

“Saboda me?”

“Zan ji tsoro ni kadai ai, kuma ban zan iya komai ba ai”

“Baki bukatar yin komai for now, kuma idan zan fita zan tafi dake gida gurin Ammy ki zauna idan zan dawo sai na dauko ki kamin su bar garin nan”

“Wani garin za su koma”

“Kaduna  suke zama, ni ma ai da zarar lokacin da aka ba ni a nan ya kare can zan koma a zamu zauna, amman kamin mu zauna can sai mun fara tafiya ayi miki aikin idonki tukuna...”

“Da ace idon zai bude, kai nake son na fara gani Captain...”

Ya kwantar da kansa a kafadarta.

“Ba zan ce Aa ba, amman maybe zan zama mutum na biyu da zaki fara gani saboda iyaye suna raye”

Ta juyo ta saka hannayenta ta lalaba inda saitin fuskarsa yake ta rike fuskar.

“Kana karfafa min guiwa, kai kake fara yarda da ni kamin kowa, na jihadin lokacin da ka yarda ban aikata ba, kuma idan a rufe ido da kunnenka daga jin duk wani abun da za a fada a kaina, har ranar yau ta kasance, duk wata macen mai dacen aure a bayana take a yau...”

Ta yi dage ya duka mata da fuskarsa ta sumbanci shi a gurin hancinsa.
Chapter 121 · 0% Book details