← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 133

Sashe 3

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo ta fada cikin kuka, sai a lokacin Appa ya samu courage din fice daga cikin gidan tare da Hurriya, a mota ma Appa ya wahala kamin ya samu Hurriya ta yi shiru, hankalinsa be kara tashi ba sai a lokacin da take bada labarin yadda abub faru. Duk wani abu da ya kamata su tambayeta sun tambaya kuma ta ba su amsa sannan Appa ya dauko ta a motarsa tare da Direbansa suka nufo gida.

“Appa ka kar ni a gurin Amma please bana son nan”

“Zan maida ke can Hurriya, ita ma ai ganinki zai saka ta dan ji sanyi, zaki dauki tufafinki, sai kuma Yasir ya baki dayan glass dinki da yake can”

“Toh”

Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa gidan. A harabar Momy Appa ya umarci direban ya faka, sannan ya fito direban ma ya fito da sauri ya budewa Hurriya mota Appa ya rikata ta fito, suka nufi bangaren ransa a jagule gaba daya shekarar nan ta zo masa a yadda be yi zato ba. A hankali ya tura kofar falon Momy sai da ya fara shiga sannan ya rikota ta shigo. Captain dake zaune ya mike tsaye yana amsa sallamar Appa, Appa ya karaso cikin falon cikin yanayin dake nuna yana cikin tsananin damuwa.

“Momy bata nan”

“Oh to ina taje? Ina zuwa Hurriya”

Ya saki hannunta ya juya ya fice daga falon.

“Ance kananki?”

Captain ya furta a hankali yana kallon kwayar idonta dake ta juyawa alamar bata ganin komai. Kamar ya tsikaro mata allurar kuka sai ta fara hawaye tana rawar murya.

“A yadda Namra ta fada min ke suka zo dauka, kin san su waye?”

Ta girgiza kai.

“Waye kai?”

Ta tambaya domin bata wayanci ko waye ba. Yayi shiru yana juya invitation card din dake hannunsa for some seconds.

“Soja ne...!”

Ta mika hannu ta fara lalaben inda take jin sautin muryarsa.

“Dan Allah zaka nemo min kanena?”

Tana daf da taba fuskarsa ya kawar da fuskar ya kai hannunsa ya rika hannunta, ba tare da ya amsa mata da eh ko aa ba.

“Dan Allah ka nemo min kanena idan zaka iya, shi ne farincikinmu, shi yake tare min fada dan Allah ka taimaka Malam Soja ka nemo min shi”

Yayi shiru har lokacin be ce komai ba ya saki hannunta daman ya rika hannun ne kawai a kokarinsa na kawaicewa taba fuskarsa. Shi dai abun da ya kawo shi gidan dabam ya zo ya tararda wannan tashin hankali.

“Malam Soja...”

Jin shiru kamar babu kowa a gurin. Sai ya kai hannunsa ya rika 5 fingers dinta ya matsa a hankali domin tabbatar mata yana tsaye a gabanta har lokacin.

“Dan Allah ka nemo min kanena, ku ne sojoji ai ku kuke kama masu aikin yan ta'adda”

Kallon fuskarta yake kamar ance masa tana ganinsa.

“Dan Allah ka taimaka mana, Appa na kudi zai iya ba ku please”

Ya sake rika 5 fingers dinta ya matsa hannunta.

“Idan ka min alkawari ka matsa sau biyu...”

It take him ten seconds kamin ya sake matsa 5 fingers dinta for the third time, sannan ya saki hannunta ya zari Invitation card daya a cikin wadanda suke dayan hannunsa na dama, ya dora su akan mini table dake kusurwar kujerar ya juya bayan dayan card din ya yaga ya ciro pen dinsa yayi rubutu akai sannan ya maida pen din ya sake barkar takardar ya kama hannunta ya danka mata rabin.

“Karki fadawa kowa, kuma karki taba jefar da wannan takardar matukar ina fatar Kanenki ya dawo”

Ta jimke yar ficikar takardar a hannunta tana sauraren takun tafiyarsa har ta ji lokacin da ya bude kofar falon ya rufe. Bayan kamar minti biyar tana tsaye a gurin aka sake bude kofar falon aka shigo.

“Hurriya Appa ya ce na zo dake”

Yasir ta karaso ya rika hannunta yaja suka fita daga falon.

“Na duba ko'ina ban ga gilashinki, zamu je asibiti a siya miki wani yanzu kamin a ga wadancan”

“Ya Yasir yaya zai dawo ko?”

“In Shaa Allah”

Yasir ne ya kaita asibitin gurin likitan da ya saba dubata, suka bata wani gilashin da ya dace da idonta, sai dai idon nata sun sake samun matsala ko da ta saka gilashin bata iya gani da kyau kamar da, hakan ya saka likitan ya sake duba idonta kamin ya rufe ta fada da kuma Yasir wai an barta ta yi kuka mai karfi da yawa har yana son tana gilashin idonta, daman idon lafiya be ishe shi ba. Magani ya bata wadanda zata shafa a idon safe da kuma dare idan zata kwanta sannan ya bata wanda zata diga a idon kamin ta kwanta. Sannan suka dawo gida, kusan duk wanda ya kalleta ita yake tausayawa domin ita ce bata da uwa a gidan kuma ita ce kadai take da kane daya, Hankalin Hurriya be kara tashi ba sai da ta zo zata dauki tufafinta da suke bangaren Momy ta kalli dakin Hamad sai sabon kuka ya taso mata, tana ganin kamar mutuwa yayi ya barsu. Ta saka tufafin da zata iya diba a jaka, ta fito tana kuka ta fice daga falon Momy. Momy dake aikin duba invitation card din da ta tarar a falonta ko kallo gurin da Hurriya take bata yi ba sai yana katin take, Namra ta tashi ta bi bayan Hurriya ta rakata har gurin motar Appa, domim shi yace zai kaita gurin Amma da kansa, sakamakon kiransa da Hajiya Binta ta yi ta ce ya zo ya dauketa ya kaita gurin Amma kuma ya kawo mata Hurriya. Namra ma sai da ta yi kuka saboda yadda Hurriya take ta kuka. Sai da suka fice sannan Namra ta dawo bangarensu tana share hawaye.

“Wallahi duk wani mai imani sai ya tausaya, kowa ya aikata haka Allah ya hana shi zaman lafiya”

Momy ta daka mata tsawa.

“Ina ruwanki shegiya yar iskar yarinya yar neman suna, ke aka sata? A gidan nan wa kika ga yana damuwa da rayuwar wani?”

“Haba Momy idan aka sace ni ya zaki ji?”

“Allah ya mayar miki da aniyarki, ni ai wanda ya sace yaron kuma ya gama da yar wajen Kaltume ya kyauta min Wallahi, daman shi Hamad ya fitini kowa, karshen mai cin amana kenan, ita kuma Ruma satarta zai hana Kaltume kwanciyar hankali”

Miwan dake saukawa ya karbawa Momy.

“Wallahi kin fadi abun da yake zuciyata, daman shen yaron nan ya isheni, saboda shi nan kwanan baya babu fadan da Appa be yi miki ba, har kuka sai da kika yi, kuma saboda shi aka mari Musib Allah yasa ma su kashe shi”

“Ato... Da ma Hurriya ce wata kila na tausaya mata, amman Hamad shegen yaro. Kaji min yarinya wai ita mai zuciyar tausayi, ke idan ke aka kama waye zai yi wannan kuka? Kuma ni bana raba dayan biyu, Wallahi Kaltume zata iya sakawa a sace yaran nan saboda muguwar mata ce, yaushe ta dawo? Ta sace kanta kudin be mata ba yanzu kuma ta koma gurin yara, balle kuma ta san Hurriya Alhaji yana ji da ita, ke ma kuma idan baki kula ba sai ta saka an dawo kanki, wannan bakar matar mutuwa kawai zata yi kowa ya huta, ni daga yau ma ba zaki sake komawa makarantar ba, canja miki makaranta zan yi, kuma direba dabam zai rika kai ki yana dawowa dake”

“Amman Momy baki ga yadda Hajiya take kuka ba, haba Momy za'ayi ta sace yarta?”

“Kukan munafurci ne, ke yarinya ce baki san kan duniya ba, ni dazun da na san Captain zai zo ai ba zan ma shiga bangarenta ba, ke kuma kika ki kirana gashi har sake zuciyar ya tafi”

“Shi yace kar na kira ki na barki sai kin kare abun da zaki yi, bayan ya tambaye ni abun da ya faru”

Miwan ya zauna yana daukar katin ya duba.

“Wallahi Momy Captain yana sonki sosai if not wulakancin nan da aka yi ta masa ba zai sake dawowa ba”

“Ai nima na san haka, shiyasa nake son zage dantse na kyautata masa a bikin, ga abu dai ya matso kusa”

Daga haka suka dauko zancen bikin kamar babu ruwansu da damuwar kowa. Appa sai da ya biya unguwar Gidan Dawa ya dauko Hajiya Binta sannan ya nufi gidan Gwaggo, a mota Hurriya na kara fadawa Amma abun da ya faru tana kuka. Appa be shiga ciki ba, daga Hajiya Binta sai Hurriya suka shiga, Hajiya ta hadu ita da Gwaggo suka yi ta bata magana suna kwantar mata da hankali. Sannan taja ma Hurriya kunne kan fita waje duk kuwa da ta san Hurriya ba ma'abociyar yawo bace, daman kuma Appa yayi mata nasa jan kunne a mota.

*** *** ***

Wasa wasa aka kwashe kwana uku shiru babu Hamad da Ruma babu labarinsu, police din da aka damkawa case din kuma ba su samu wani bayani ba, sai dai suna ta kokarin zafafa bincike iya yinsu. Tun daga ranar kuma Amma bata iya bachi, dare take rayawa tana fadawa Allah bukatarka ya kare mata danta ya dawo mata da shi cikin aminci. Abinci ma Amma bata iya ci sai Gwaggo ta yi da gaske. Hurriya kuma tun daga ranar bata sake zuwa makaranta ba saboda tsoron fita da take ko kofar gidan bata yarda ta tafi, daman kuma Appa ya daukarwa yaransa hutun sati daya a school dinsu har zuwa lokacin da abun zai dan sake su. Appa ma ya yarda Hurriya ta zauna a gurin Amma ne kawai saboda Hurriyar ta zaki haka, kuma ya san hankalin Amma zai dan kwanta idan Hurriya tana kusa da ita, ba dan ransa yana so ba, domin gani yake ko a can za a iya tafi a dauki Hurriya ko Amma.
Chapter 3 · 0% Book details