← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 133

Sashe 56

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[11/28, 5:22 AM] AMINA KABIR CAPS: *KHADIJA CANDY*

*PAGE 2️⃣7️⃣*

“Ruwa duk ya jika ka fa”

Ya kalli jikinsa ya daga fadunsa.

“Na tuna baya ne”

Ya fita daga cikin ruwan ya karaso bakin kofar ruwan na siyaya a jikinsa. T-shirt din dake jikinsa na bayyana yadda Allah ya zuba hallita a jikinsa saboda jikewar da rigar ta yi da ruwan sama.

“Rayuwar baya kuma Captain? Ko dai akwai abun da yake damunka? Baka saba irin haka? Zuwa ka yi aiki a gidan nan, ga kuma tsaya a ruwan sama kamar wani karamin yaro kalli fa har wristwatch dinka ya jike”

Ya kalli agogon.

“Kudi ne nan ba zallar agogo ba, ruwa baya masa illa, lemme go and change set the table please ban ci abincin rana ba”

Yana fadar hakan ya nufo gurin da take tsaye sai ta masa ta ba shi hanya tana binsa da kallo gabanta na bugawa da mugun karfi, har sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta samu sa'ida. Hakika Jameel ya kai namiji ya cika ta ko'ina irin cikar da ake so a jikin kowane jarumin namiji, Allah ya hada masa abubuwa da yawa ya bashi kyauta ba tare da ya roka ba. Da kallo ta bishi har ya haye sama sannan ta dauke idonta ta nufi dinning domin duba abun da babu. Abu na farko da ya fara yi bayan shiga dakin shi ne canja tufafinsa ya saka wadanda ke karamar jakarsa. Ya saka kai wadanda ya cire a toilet sannan ya bude kofar na saka kafarsa waje Hurriya ta juyo da sauri tare da ihu domin bata san da mutum a dakin na Miwan ba, ya janyo kofar a hankali ya rufe yana kallonta ko'ina na jikinta siyayarda ruwa yake.

“Aljani kika gani?”

Ta girgiza kai.

“Karki sake min ihu”

Ta daga mishi kai tana kallonsa ido kamar za su fado.

“Daina kallona”

Ta yi saurin sauke idonta kasa, ta juya ta bude kofar dakinta da sauri ta shige ciki ta rufe. Murmushinsa mai tsada yayi sannan ya taka ya fara sauka stairs din da sassarfa.

“Tafiya zan dafa maka, saboda na san baka cin tuwo, ni san na manta ma tuwo aka yi yau Wallahi”

Namra ta fada tun kamin ya karaso dinning din. And she's right baya son tuwo baya cin tuwo ko da yunwa zata kashe shi ba ya iya cin tuwo. Ya dafa kujerar yana kallonta

“Ina yarinyar nan kanwarki?”

Ta dan motsa ido gafe da gafe.

“Hurriya?”

“Yea kira ta ta girka min”

“I can cook for you”

“You don't have to stress yourself Pretty, kira ta girka”

The way he said kar ta yi stressed kanta ya saka ta ji she's special kuma hakan ya nuna har a gurinsa tana da muhimmanci.

“Okay”

Ta amsa da murmushi sannan ta nufi hanyar stairs, shi kuma ya nufi gurin da ya zauna dazun ya zauna. Ya cigaba da aikin da yake, Namra bata dauki lokaci ba ta sauko.

“Sallah take amman na fada mata zata sauko idam ta gama”

Ya amsa mata da kai hankalinsa da natsuwarsa gaba daya yana gurin aikin da yake a yanzu. Momy ce ta sauko tana sanye da bakar abaya tana murmushi.

“Captain aiki ake take yi”

“Aiki nake Momy akwai abun da ya kamata na yi typing na aika Abuja kamin gobe”

Ita ma dai ya amsa mata ba tare da dago kai ba.

“Amman ka ci abinci?”

“Za a dafa min yanzu”

Momy ta kalli Namra dake tsaye.

“Namra tafi ki sama masa wani abun yanzu mana, kin san fa baya son tuwo”

“Na ce zan yi yace kar na yi stressing kaina Hurriya zata dafa?”

“Hurriya kuma? Bata gidan ma fa”

“Ta dawo tana ciki, dazun ai Inna Shatu ta gama gage gurin data bata da ruwa saboda ta jika tufafinta”

“Okay to kin fada mata”

“Eh”

“Bari na shiga ciki har ka gama aikin Captain”

“Okay Momy”

Still be dago ba, Momy ta juya ta koma ciki, Namra kuma ta zauna kusa da shi tana duba wasu daga cikin takardun da yake aikin. Captain be dago ba har sai da ya ji karar talkamin Hurriya tana saukowa daga stairs din, yadda sautin takun tafiyar ke fita ya fahimci ita ce, kamar an saka hannu biyu an rika fuskarsa da karfi an juyar da ita zuwa stairs din haka ya ji. Ba kwalliya ta yi ba amman green atamfar dake jikinta ta karbe ta sosai ta yi mata kyau, Brown hullar dake kanta ma ta fito da ita, ga dan gilashinta dake kara mata kyau a kullum. Ba tarbiyar ta bace yi ma wanda ya girmeta magana a tsaye ba, musamman ma ace mutumen a zaune yake dan haka ta risina a gabansa.

“Gani”

“Me yasa baki yi sallah da wuri ba sai yanzu? Baki san babu kyau sallah a makare ba?”

“Mun fita ne tare da Yaya Khairy kuma na yi bachi a can ban san an yi sallah ba”

“Da kika dawo kuma kika tsaya wasa da ruwa, wuce ki dafa min taliya”

Ya fada yana binta da kallo, ita kuma bata yarda ta kalleshi ba domin bata manta da kashedin da yayi mata dazun ba. Har ta fara tafiya sai kuma ta juyo.

“Momy tace na daina shiga mata kitchen fa, zata yi fada”

“Ka ji wani salon munafurci, zaki tafi ki dafa ko kuma sai na kira Momy na fada mata?”

Namra ta fada tana kokarin kare mahaifiyarta kar Captain yace suna yin abun da be dace ba. Captain ya kalleta

“Easy Namra”

Sannan ya kalli Hurriya

“Shiga ki dafa ni na saka ki”

“Toh”

Ta juya ta shiga Kitchen kamar wanda bata son tafiya. Ta yi iya kokarinta wajen ganin ta yi girkin da kyau da kasancewar ta kwana biyu rabonta da dafa ko da indomie ce balle taliya ko wani abincin dabam, amman har yanzu bata manta da yadda Amma take koya mata ba a lokacin da take gidan, bata cika yaji ba domin bata san sani ba ko yana son yaji ko baya so. Sai da ta gama dafawan sannan dauko plate ta zuba masa ta dauko katon tray ta dora plate din akai ta saka fork a gafe ta dauki yajin dake kitchen din ta dora a tray ta zuba ruwa a wata karamar roba ta zuba ruwa ta dora a tray ta dauka ta fito da shi, bata dire shi a ko'ina ba sai gaban Captain, ya dan karkarto ya kalli yadda take aje ruwan dake roba.

“Gashi nan idan da hannu kake ci ga ruwa nan idan da fork gashi nan, kuma ga yaji nan ka kara idan be isa ba”

Ta mike tsaye ta yi hakan ne na dan komai ba sai dan ta huta kar yace ta yi masa wani abun.

“Hurriya”

Ta juyo

“Na'am”

“Ina naki abincin? Kuma baki kawo min ruwa”

Sai kuma ya kalli Namra

“A zubo miki ke ma?”

“Aa”

Hurriya ta koma kitchen din ta dauki plate ta zubama kanta abincin ta saka spoon sannan ta dauko masa ruwa da cup ta dauko ma kanta ita ma, tana aje masa nasa ta wuce da nata sama. Sai da abincin ya sha iska sannan ya aje laptop din ya dauki abinci ya dora a cinyarsa ya fara ci, sai ya ci ya ji ya koshi sannan ya mikawa Namra plate.

“Zan je na yi sallah an fara kira”

Ya mike tsaye a daidai lokacin da Hurriya ta sauko rike da bokitin data matse kayan data jika, wuce su ta yi ta fita waje ta zagaya can baya gurin da igiyar gidan take ta dora kayan sannan ta juyo ta fito. Tana haura entrance din Captain na saukowa sai ta dan koma daga gefe so that ya wuce sannan ta shiga even tho gurin yana da fadi, a haka dai bata son ya zama ta jeru da shi. Kusa da ita ya matsa ya jefa mata wata takardar a cikin bokitin da take rike da shi ba tare da ya kalleta ba ya sauka yana warware hannun rigarsa bayan ya nade shi saboda alwalar da yayi. Tsayawa ta yi kallon takardar kamin ta kai hannu ta dauka.

“I rate your food 4/10 put more effort next time”

Ta daga kai tana kallonsa har ya shiga motarsa yayi reverse ya bar gurin, sannan ta maida idonta ta sake karantawa wannan karon murmushi ta yi ya jimke takardar a hannunta sannan ta juya ta koma ciki.

HAJIYA KALTUME POV.

Malam ya girgiza kai yana dauke idonsa daga kasar dake gabansa.

“Hajiya shiyasa ban fada miki komai ba, idan baki manta ba ai na taba fada miki cewar duk wanda nake yi ma aiki ina bibiyarsa na ga halin da abubuwan suke ciki”

Hajiya Kaltume dake lullube da farin mayafi ta daga kai.
Chapter 56 · 0% Book details