← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 133

Sashe 128

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka yi Murmushi. Yasir  ne mutum na farko da ya fara mikewa tsaye ya fice daga falon. Sai da ya dauki lokaci sannan Rukayya ta bayansa. Gingine ta same shi jikin motarsa ya rike kansa ya rasa me ke masa dadi a duniyar nan.

“Yasir...”

Ya dago ya kalleta sai ya kawar da idonsa.

“Minene Rukayya?”

“Ya kake?”

“Lafiya kalau”

“Dan Allah karka boye min ya kake?”

Da ya dube ta sai ya ga hawaye take zubarwa shi ma sai na shi hawayen dake makale suka zubo.

“Ban sani ba, ko za su zabi kai Hajiya gidan yare ko akasin haka, amman ba zan iya zama garin nan matukar mahaifiyata ta kasance a gidan yari, ba ni da sauran farinciki a yanzu. I respect your parents decision da suka hanani aurenki suna da gaskiya”

“Yasir shin har yanzu kana so na?”

Ya dubeta da kyau sai yayi murmushi ya dago wayarsa ya nuna mata hotonsa da yake a screen din wayar, sannan ya sauke ya tafi ya bar a gurin tsaye. Amma da yan'uwanta suka koma bangarensu suna tattauna abun da ya dace Appa ma yana tattauna da nasa yan'uwan. Captain kuma ya fito yana magana da Hurriya, so yake ya dauketa su je family house dinsu su ganta even though Magariba ta gabato, ita kuma tana son kasancewa da yan'uwanta a yanzu.

“Idan mun tafi can Nene zata iya cewa na kwana a can ai ko?”

“Ya za'ayi tace miki haka bayan kuma ta san kina da MiJinki?”

Ya duba yaga babu mai ganinsu sai ya kama fuskarta yana kallon kwayar idonta.

“Alhamdulillah you can see now my baby my heart my soul my duniyata”

Ta yunkura zata yi dariya sai amai ya cika mata baki, da sauri ta ja baya ta juya ta fara kwarara amai a gurin kamar zata amayar da yan hanjinsa. Captain ya shiga cikin ya dauko mata ruwa ya wanke mata bakinta sai da yayi da gaske sannan ya iya danne zuciyarsa domin shi ma aman ya ji yana taso masa. Ya taba jikinta.

“Sannu kina jin rashin lafiya ne?”

“Aa amman kai jikinka da zafi, ko zaka tafi asibiti ne?”

“Maybe gobe, amman ba yau ba dare yayi, ki shiga ciki ki huta gobe zan tafi na kai ki gurin su Nene”

“Toh.. Sai da safe..”

Har ta juya sai ta ji an riko hannunta an dawo da ita.

“Hurry na.. Me kika ci ya saka ki aman nan? Me yasa kika yi amai?”

“Ban sani ba”

Ta dan yamutsa fuska.

“Turarenka nan ne bana so yanzu”

Yayi murmushi ya rika hannunta ya nufi gurin motarsa.

“Me ye ina zamu je?”

“Asibiti”

“Babu asibiti da yamma fa..”

“Ta barrack zamu tafi likotocinsu kullum available”

“To ai ni lafiyata kalau”

“Ni zaki raka”

Ya bude motar ya saka ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga yayi ma motar key. Sannan ya kama hannunta daya ya rike yana tuka motar.

“Ban a kwashe aman ba, idan wani ya gani zai ji kazanta”

“Idan mun dawo sai ki fada a kwashe”

Be tsaya ko'ina ba sai asbitinsu na Barrack yana zuwa aka hau yi mata gwaje gwaje mamaki ya hana ta magana bayan kuma yace shi zata raka, ba ayi taru ba sai a gurin da za a debi jininta a auna, nan kam sai da ya zauna a kujera ya rumgume da karfe ya rike hannun sannan aka dibi jinin. A nan ya barta ya tafi yayi sallah ya dawo sannan ya karbi results. Be bude ba sai da suka isa gurin mota yana karantawa yana murmushi.

“Me suka ce? Ka shafa min rashin lafiya ko? Kai ne fa mai ciwo”

“Baby na kin dai shafa min laulayi”

Ya kashe mata ido daya, sai ta yi fuskar rashin fahimta.

“Ban gane ba?”

“Minene Albarka aure?”

Ta dan yi shiru...

“Kwanciyar hankali da zaman lafiya”

Ya daga kansa sama yayi dariya sannan ya jata jikinaa ya rumgume yana jin wani irin kaunarta a ransa.

“Silly Girl, albarka aure haihuwa”

Ta dago da sauri ta kalleshi tana kwalo ido baki sake, sai ya daga mata kai ya sumbaci goshinta.

“Uhmmm”

Ya shiga sumbantar fuskarta ta ko'ina, kamar ba a public place suke ba, he just got lucky inda suke babu kowa gurin aje motoci ne kuma ko akwai bariki babu ruwan kowa da rayuwar kowa.
[1/5, 9:04 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

5️⃣7️⃣

“Hajiya me yasa baki ki tunanin makomarki ba da ta mu kamin ki aikata? Wane irin abun kunya ne wannan? Har yaushe zuciya zata bushe ki aikata hakan ga dan mijinki dan be miki komao ba, be tare miki komai ba? Idan ma kishi kike da mahaifiyarsa shi meye nasa a ciki? Gashi har kina fadar sanadinki Salma ta mutu...”

Hajiya Kaltume ta kyalkyale da dariya ta buga kafa. Ta janyo jakarta ta ciro maganin da ta dawo da shi ta zube a gurin.

“Ai ba Shikenan ba, ni na saka Khairy ta dauke gilasan da suke dakinka na Hurriya, ni na yi ma Hurriya da Appanta farraqu, aka saka masa tsanar Hurriya, ni na saka aka saki Iyami Yasir ni na yi mata wannan asirin kuma na ce a kwantar da ita ciwo, kuma na ce ayi mata asiri kar wani ya ganta ya aureta, yanzu wannan maganin shi kuma bokan ya fada min idan na yi amfani da shi Alhaji zai zo Jiki na rawa ya maida aurensa, kuma Fadeel zai dawo ya auri Khairy... Kawata Hajiya Fatee ita take kai ni ko'ina ita ma kuma tana can da ciki cikin haihuwa wanda ta saka malam ya danne, na biyawa Malam makka saboda na jidadin aiki, na mallaka Alhaji sai abun da nace yake min... Tabbas na aikata Hamad kuma ni na dauke shi ni ce nan na aikata, kuma na yi shiga gaban Alhaji da Sapna na kawar masa da ita a zuciya ya fita maganarta na shashantar da ita a zuciyarsa...”

Kusan duk wani abu da Hajiya Kaltume ta aikata tun cancan da har zuwa yau sai da ta fadawa yaransa da wanda suka sani da wanda ba su sani ba. Yasir sai ambaton Allah yake be taba tunanin mahaifiyarsa ta yi nisa haka ba sai yau be taba tunanin ita ce sanadin barin Amma a gidan ba sai yau, be san ita ta shiga tsakanin Hurriya da Appa ba sai yau, be san ita ta aikatawa Hamad haka ba sai yau. Ya rasa ta ina zai fara ya rasa ina zai saka kansa ya samu sassaucin rayuwa.

“Ku shiga da ita cikin daki ku rufe karku bari ta fito”

Ya fada sannan ya share hawayensa yana jin kamar ace ya mutu kamin yau. Ruma ta kalleshi tana kuka.

“Yaya yanzu idan da gaske Hamad ya dawo gidan yari za a kai Hajiya Kenan?”

Ya cije baki ya saka cewa komai sai hawaye ke sauko masa. Tashi yayi ya fice daga falon ya nufo bangaren mahaifinsa ya zauna a gurin yana jin wani bala'in gabas da na yamma yana hade masa, da ma ace wata ce daga cikin kannensa zai ji sauki amman uwarsa? Abun yayi masa muni gaba daya ma sai ya rasa abun da zai yi, tun farko be ga dalilin Hajiya na aikata hakan ba, domin bata rasa komai a gidan Appansa ba idan ma ta tasa me yasa ba zata barwa Allah ba. Yanzu wa gari ya waya? Karshenta jifan akan wa ya dawo? Waye yayi mummunan karshe? A yanzu ya kara jin kaunar Amma a ransa domin ita da ta wakkala ga Allah gashi yayi mata mafita kuma yana kan mata, Hurriya ma haka, Amman Khairy gashi ta girbi abun da ta shuka tun abun be yi nisa ba, Hajiyarsa ga abun na kokarin taba hankalinta ko ma ya taba.

Allah kawai yake ambato ya rasa me zai yi, wa zai tunkara da maganar ya rasa ina zai bullowa lamarin. Yana zaune a gurin har la'asar, sallamar ma yana yi ya sake dawowa gurin ya zauna tunani yake amman tunanin ya ki tsaya masa ya tasa wanda zai ba shi shawarar abun da ya dace ya aikata. Asibiti zai dauki Hajiya ya kaita? Ko kuma dai ya sanar da Iyayenta da kanenta domin babu iyaye a yanzu, ko kuma dai ya samu mahaifinsa da maganar. Daga balcony din da yake zaune ta bangaren Appa ya hango shigowar motar Maama, hakan ya saka shi tashi ya nufi bangaren mahaifiyarsa, a dakin ya sameta tare da sauran yan'uwanta Khairy da Ruma suna kuka har lokacin Hajiya Kaltume bata daina tonawa kanta asiri ba.

“Ku kira su Hajiya Fanna da Mama Zainab ku fada musu halin da ake ciki, idan asibiti za a kai ta sai mu tafi...”

Maama ta juya ta kalleshi tana hawaye

“Haka Jarabawar ta zo mana Yaya? Ni gidan aure babu dadi Hajiya kuma nata auren ya kare, Khairy an fasa yanzu kuma wannan ya biyo baya?”

Yasir ya daka mata tsawa kamar zai daketa.

“Laifi duk na waye ba naku ba? Idan ta kauce ko zata aikata wani abun da ba daidai ba kun fi kowa sani, me yasa ba zaku nuna mata illar hakan ba? Amman ke kuke zugata kuna tayata kishi ku nuna abunda take daidai ne, ke Khairy lokacin da kika aikatawa Hurriya haka bata ma sani ba, saboda zuciyarku babu kyau, ke kuma idan abun kwarai ne gashi yanzu kin yi aure kin girba, kar wanda ya sake saka min baki akan lamarin uwata kar wanda ya sake wata magana ku bar ni na ji da zafi daya”

Ya share hawayensa ya fice daga dakin, ya sauko kasa wayarsa tana ringing da ya duba sai yayi arba da number Appa, and for the first time sai ya ji ba zai iya amsa kiran ba, a yayinda wayar yake rike a hannunsa tana ringing. Ya jingina da kofar falon ya cije bakinsa ya buga ginin ya girgiza kai. A karo na biyu wayarsa ta sake yin ringing ya dago ya duba wayar Appa ya sake kira wannan ya dauka sai dai yana kara wayar a kunnesa sai ya fashewa Appa da kuka kamar mace.

“Subhanallahi... Yasir.. Lafiya kana ina?”
Chapter 128 · 0% Book details