← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 133

Sashe 93

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ya kara tabbatar masa da yarsa bata shiga mugun hannu ba. Appa ya takasu tare da Yasir har gurin motarsu suka shiga sannan ya koma ya cire dabino da goro ya nufi bangaren Momy yana murmushi kana ganinsa ka san yana cikin farincikin da ya dade be yi ba. Yasir ne ya rabawa mutanen da suka shaidin daurin auren a gurin sannan ya dauki sarkar Zinarin da Appa ya ba shi riko ya shiga bangaren mahaifinyarsa yana murna. A falo ya tararda Hajiya Kaltume da Khairy zaune a kujera daya.

“Hajiya kina nan har yanzu”

“Wallahi kuwa, ka ga tun da na raka Hajiya Fatee nake zaune a nan muna hira da Khairy, wai kiran me mahaifinka ya shigo yana maka a gaggauce?”

Ya zauna saman kujera yana rike da kwatin na zinari.

“Auren Hurriya aka daura...”

Khairy da Hajiya Kaltume suka kalleshi jin abin banbaragwai.

“Baka da hankali wane irin aure kuma?”

Yasir yayi murmushi daman ya san ba lallai kowa ya ji ya yarda ba.

“Aure dai Hajiya, Wallahi aure aka daura mata yanzu nan, wasu ne suka zo tambayar aurenta Appa ya ce ba za su tafi ba sai an daura auren”

“Allah sarki to su ba su da labarin abun da ta yi ne? Ko kuma yan'uwan Adam din ne suke neman a rufawa juna asiri?”

“Ba su ba ne, yarinyar nan fa ta rantse Hajiya bata aikata ba, be kamata ki fadi haka ba”

“To ko da bata aikata ba ai dai mutuncin ta ya zube, duk wanda ya aureta kila ba zata wuce gobe ba zai sake ta, da alama ba su da labari ne, shiyasa suka zo shi kuma Appanku yana neman a raba shi da abun kunya a dole ya rike su a daura auren a gurin, ko dai shi yayi sadaka da ita? Wa ta aura dan baro ko dan shara? Ko cikin masu ban ruwan fulawoyin gidan nan”

Yasir girgiza kai yana murmushi, ya bude akwatin zinari dake hannunsa.

“Wani ne mai daraja Hajiya, dan'uwan Momy ne da Zinari mahaifinshi yayi sadakinta, na naira miliyan hansi...”

A take fitsari ďan tsirin ya kubucewa Hajiya Kaltume ta cire dankwalin kanta ta aje a cinyar Khairy tana kallon zinarin kamar zata yaga ido....

**** **** **** ****

Bayan Daddy ya rufe motarsa, suka jero tare da yan'uwansa suna tafiya ya ce.

“Mahaifinta yayi dabara ni ma na jidadin haka, ka ga mun tsallake ma duk wani tarko a yanzu, shi kan shi Jamal sau biyu ana saka ranar aurensa ana fasawa saboda fushi da wasu hujjoji da ba su kai ba, mu kuma muna biye masa ne saboda farincikinsa muke nema, amman yanzu ka ga wannan duk ya kau a yanzu”

“Gaskiya haka ya fi, ka ga an huta da fitinar Hajiya Turai”

“Daman fitinarta ai zan iya da ita, matata ce fa abun da dai nake tsoro ta canjawa Jamal din ra'ayi gaba daya”

“Wannan gaskiya ne”

Cewar Alhaji Sadiq. A falon Nene suka zauna gaba dayansu, sai Daddy ya sa a kira masa Captain dake dakin sama tun safe be fito ba, kamin ya fito Daddy ya kalli Momy Ikilima ya ce.

“Ikilima ki shiga gurin Turai a cikin kayana akwai wata shadda irin wannan ta jiki sabuwa ce a cikin leda, a dauko ta ta hado miki da sabuwar hula, da turaren da ba a fasa ba”

“Toh Yaya”

Ta tashi ta fice, domin bangaren da Daddy yake sauka dabam idan ya zo gidan. Fitarta da minti biyu Captain ya shigo falon, a kasa ya zauna ya gaishe da iyayensa.

“Ya karfin jikin Captain”

“Alhamdulillah daman stress me kawai Abba na ji sauki”

Ya amsawa Alhaji Munzali, kamin ya daga kansa yana kallon dinkakkiyar Shaddar dake Ikilima take mika masa, ya saka hannu biyu ya karba.

“Shiga ka yi wanka ka saka wannan shaddar ka feshe turaren nan gaba daya a jikinka”

“Daddy why?”

Ya tambaya da confused.

“Ina son ka raka ni airport ne kuma ina son mutane su ga yarona cikin mutunci, kuma karka dade ka fito yanzu nan ina jiranka”

“Toh Daddy”

Captain ya mike tsaye ya fice daga falon na Nene. Dakin da ya zama masaukinsa ya shiga ya cire tufafin jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa mai ya saka shaddar ya dauko turaren ya feshe jikinsa gaba daya sai da kwalbar turaren ta kai kasa sannan ya dauki hula ya saka a kasan shi kansa, ya dubi kansa a jikin madubi shi kanshi ya san yayi kyau abun da ake kira da kyau, farar shaddar ta haske shi matuka... Wayarsa ya dauka ya saka aljihu da wallet dinsa sannan ya nufi kofar dakin ta bude ya fita yana wani irin kamshi mai sanar da zuwansa tun kamin ya iso. Ga mamakinsa sai ya samu babban falon na kakarsa a cike da mutane ciko har da mahaifiyarsa da kakarsa da abokiyar zamanta da duka wanda yake gidan a lokacin. Da mamaki ya sauko falon yana kallon kowa kowa kuma yana kallonsa...

“Zo nan Jamal...”

Daddy ya fada yana murmushi, Captain ya nufi gurinsa sai Daddy ya mike tsaye ya saka hannunsa aljihu ya ciro goro da dabino ya ce.

“Bude min hannunka... ”

Captain ya bude tafin hannunsa na dama ya mikawa Daddy, sai Daddy ya zuba masa dabino da goro dake hannunsa.

“Mun je jaje, kuma mun roki iri, kuma an ba mu, na nema maka auren Hurriya a yau, kuma an daura mun bada zinari na miliyan 50, a matsayin sadakinta, saboda dka fada mana mai tsada ce, shiyasa muka siye ta da kima, yau mai tsada ta zama mallakinka, Hurriya ta zama matarka halak malak...”

Kamar an aje hoto haka falon yayi tsit kamar babu wani abu mai rai a ciki, daga Captain har iyayensa babu mai motsi....

MASU KARATU BA BIYA A ZO A BIYANI HAKKINA A SAUKE NAUYI A HUTA

500 to Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/18/2023, 2:14 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

4️⃣3️⃣

Hajiya Binta ya jinjina kai tana kara girmama labarin Allah, a duk lokacin da ake son mutun ya kunyata idan Allah yana tare da bawa ba a taba ganin abun da ake bukata, kariyace da sakamako mai kyau tare da kyau da kariya mai yawa daga Allah zuwa ga bayinsa da suka rike shi kuma suka dogara a gareshi.

“Duk wanda ya aikata wannan abun ya aikata ne saboda ya ci mutuncin Hurriya ya ci namu, ashe be sani ba yana kara kusance da mata da alheri ne”

Appa yayi murmushi a yayin da yake zaune a kasa rike da sarka ya kalli Yasir dake gefensa ya mika masa sarka.

“Budewa Hajiya ta gani”

Yasir ya karba ya mike tsaye ya bude mata sarka, Hajiya Binta ta saka hannu ta karba idonta na cika da hawaye.

“Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar, Allah ka sakawa wannan auren Albarka, kuma ka nuna min na sauran yaran”

“Amin Hajiya Amin”

Appa ya amsa da kansa, fadar irin farinciki da yake ciki a yanzu bata lokaci ne, farinciki da yake a yanzu ya fi wanda ya samu kansa a lokacin da aka haifo masa ita.

“Be kamata mu zauna ba Tsoho tafiya zamu yi mu sanar gidan mahaifiyarta da kuma ita yarinyar halin da ake ciki”

“Haka ne... ”

A nan kam sai yanayin Appa ya canja, ya sauke kai kasa damuwa na bayyana a fuskarsa. Yasir ya aje sarkar zinarin dake hannunsa ya mike tsaye ya fice daga dakin yana taba wayarsa. Appa ya bishi da kallo har ya fice sannan ya juyo da kansa ta inda Hajiya Binta take zaune ya ce.

“Ina jin kunyar hada ido da mahaifiyar yarinyar Hajiya, abun da na yi mata ban kyau ba, be kamata na aikata hakan ba, ban san me yasa na sake ta ba, kuma na kasa samun dalilin har yanzu da muke maganar nan dake, Iyami bata min komai ba face biyayya da kyautatawa, amman na saka mata da mafi munin sakamako na juya mata baya na wulakanta yaran da ta haifa min”

Ya shigar da lips dinsa duka biyu a bakinsa ya rufe dantse bakin zuciyarsa na ƙuna da abun da bakinsa yake furtawa.

“Alhamdulillah, ganin ka gane kuskure ni a gurina abun farinciki ne, babu daren da bana addu'ar Allah ya baka ikon gane gaskiya, domin abun da ka aikata kamar baka aikata shi cikin hayyacinka ba”

“Ban san me ya rufe min ido na aikata haka ba, ina jin nauyin iyayenta da ita kanta Iyamin a yanzu”
Chapter 93 · 0% Book details