← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 133

Sashe 132

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amman ai wani baya zama daya da wani, idan ita tana yanke alaka dake ke sai ki sada ai ke din jininta ce babu yadda zata yi”

“Amman dai Allah yana gani na yi iya yadda zan iya na janyo ta a jikina ta ki ba ni hadin kai, idan na kirata da waya bata dagawa idan na mata magana bata amsa min, haka haihuwar nan da ta yi ina shiga gidanta sai ta bata rai ta dauke min fuska to ya zan yi?”

Ya zauna bakin gadonsa ya maida Aliyu a hannunsa.

“Zo ki ba shi nono, laifinki ne da kike bari yayi kukan ai baki kusa...”

“Ni yar aikinsa ce da zan rika zama kullum kusa da shi saboda kar yayi kuka?”

“To miye aikin ki a gidan idan ba kula da yarana ba? Kin ga ni Baby idan kika yi wasa Allah zan ki sha wahala a garin nan kin san dai baki da kowa a nan sai Allah ko? Ina Manal?”

“Na siyar da ita miliyan biyar na ci tsire”

Yayi dariya ya girgiza kai

“Wallahi da ke ma sai na siyar da ke, bukin nan na Musib da za mu je kawai Appa ya ga babu ke...”

“Wallahi Appa ba zai barka ba, idan ya fara maka masifa sai ka rikice”

“Baki san Appa ya fi so na dake ba yanzu?”

“Ni kuma Daddy da Ammy sun fi ko da kai...”

“Aa aa dama dai jikokinsu kika ce sai na yarda amman ke din? Ta ina?”

Ta bude ido.

“Zan nuna maka kuwa, Allah ya kai mu Kaduna lafiya”

“Ameen bashi nono dan Allah kuma ki daina wofintar min da yaro dan Allah”

“Ban masa komai ba kawai zuciya ce fa, Ammy tace haka ka yi kana karami da an kyaleka sai kuka sai fushi....”

“To miyasa za a aje ni din? Kuma Ammy ta daina zama da ke tana baki labarin kurciyata haka kawai”

Ta ra kwafar da kai tana daga masa gira daya.

“To yaya?”

Yayi dariya yana mika mata Babanshi.

“Wato baki horu ba ko? Duk abun da na yi Miki jiya sai da kika samu baki fada min magana yau har da su daga gira?”

Yana fadar haka sai murmushin dake fuskarta ya gushe ta bata fuskar.

“Na bari yi hakuri”

“Matsoraciya, babu abun da za a fasa yarinya, kara ma ki saba soja fa kika aura ai sai hakuri kawai”

Ya sumbanci goshinta sannan ya mike tsaye yana dariyar keta ta fara shafa mai. Tana rumgume da Haydar tana ba shi nono har ya gama shirinsa ya saka uniform sannan ya zauna kusa da ita yana amsa kiran da Namra ta sake masa.

“Lafiya Kalau ya yaranki?”

“Lafiyarsu kalau, Ya Hurriya da su Manal? Da Daddy”

“Lafiya Kalau”

“Captain daman ni ce nake son na je Gusau yau kuma babu flight, shi ne nace bari na tambaya ko zan samu ta bangarenka lefen Musib za a kai kuma bana son aje ba tare da ni ba”

Captain ya daga hannunsa ya dafa matarsa.

“Wallahi Daddy ya karbe komai nasa a gurina, ya cire sunana a komai ba ni da ikon komai nasa yanzu sai dai ki kira shi ki yi magana da shi”

“Me yasa?”

“Saboda na ki yarda na aje aiki na tsumduma a harkokinsa”

“Okay bari na kira Momy sai ta mishi magana ko Ammy”

“Okay ki gaishe da Sadiq”

Captain na sauke wayar Hurriya ta kalleshi sai ya sumbanci idonta

“Yaushe yayi haka?”

“An kwana biyu”

“Amman kansan baka kyauta masa ba ko? Be kamata ka yi haka ba”

“Babyna mutum be da ra'ayin kansa ne? Bana son kasuwanci Allah ya gani na fi jindadin aikina”

“Haba Noor idan baka maka ba wa zai masa? Kai kadai yake da shi fa, kuma wani abun ko bama so haka zamu daure mu aikata saboda iyaye”

“Baki fatan na kai Major General ne? Yanzu gashi an kara mukami kuma a haka sai na bar aikina na koma ga wanda ban saba ba, ba wai ba zan yi ba ne gaba daya, zan yi amman na hada biyu”

“Ni daman ba son aikin naka nake ba, kullum muna wannan garin gobe muna can ni dan Allah ka aje ka ka bi abunda Daddy yake so if not...”

Ta aje masa babynsa ta mike tsaye sai yayi hanzarin mikewa ya rumgume ta ta baya.

“Me zai faru haba yan matana my one and only daga ke ba kari idan ina soja, idan na zama dan kasuwa kuma... That's the whole different story”

Ta Bude baki ta juyo ta kalleshi.

“To me kake nufi”

Da dariya yayi ya rumgume ta yana sumbantarta.

“Uwargidata kuma amarya wasa nake, kar a hana ni abinci a yau”

Ta yi dariya tana lilo a jikinsa.

“Karamin aikina ne kuwa”

Ya shiga gyara mata girarta.

“Ai na sani, uwar Manal da Haidar sarakuwar AA Turaki in-law din Hajiya Turai, yar gatan Jamal farincikin Amma, sanyin idon Appa, aminiyar Hamad”

Ya sumbanci bakinta yana shafa jikinsa kusan a kullum kamar amarya take a gurinsa, saboda sonta da yake mata ya fi wanda take masa, ita kuma tana kokarin ganin ta kyautata masa ta rike kambunta a gurin mijinta.

“Dadadadadada..”

Yana jin muryar Manal yayi hanzarin dauke bakinsa a na ta ya kauce daga shu'umin rikon da yayi mata ya kalli kofar dakin da aka turo. Yarinya ce yar shekara biyar rike da pen da ipad ya raba gashin kanta gida biyu an mata two babys da pink ribbons. Kusan fuskarta gaba daya fuskar Captain ce kadan ta debo daga Hurriya. Captain ya rage tsayu ya duka daidai yarsa yana gyara mata gashin kanta.

“Ammyna ina ta tambayarki...”

“Ina daki ina drawing, Dada na zana ka look”

Ta nuna mishi zanen dake ipad dinta sai ya karba yana yabawa.

“Wow Ammyna kin yi kokarin excellent”

Manal ta yi dariya ta yi tsalle tana jindadi. Captain ya sumbance ta sannan ya daga ta sama ya dauke ta ya fice daga dakin.

*** *** ****

An yi bikin auren Musib da Ruma da aka hade lokaci daya, cikin jindadi da barin naira, domin Musib shi ne dan Momy na karshe da zata aurar a yanzu, bayan Miwan da ya auri wata Abokiyar karatunsa da kuma yar gudaliyarta Namra wadda ta auri Dr Sadiq abokin Yayanta Miwan, hakan ya saka Momy ta fitar da kudi ta yi hidima sosai kamar yadda ta yi a sauran bikin yayanta ko ma fi.

Amma ta zage dantse wajen ganin ta zamewa Ruma uwa duk kuwa da irin abubuwan da Hajiya Kaltume ta yi mata a lokacin da take gidan, Amma bata duba wannan ba daman hali ba daya ba, dan haka ta rike Ruma kamar yarta, duk wata siyayya da za'ayi ta auren Amma ce ta yi domin Momy tana can tana fama da nata hidiman na auren danta.
Duk wata hidima da ya dace uwa ta yi Amma ce take yi, domin bayan komawar Ruma da Khairy a gurin yan'uwan mahaifiyarsu sai zaman yake yi musu dadi, bakinciki sai ya taru yayi musu yawa, suna kallon mahaifiyarsu da bata iya komai sai tona asirin kanta har ta kai ana rufe ta a daki sai idan za a bata abinci ko abin sha ko gyara mata jikinta sannan za a bude ta, ko kuma idan wani ya kawo mata ziyara. Gashi kuma ba sa jindadin zaman gidan, Ruma da kanta ta zabi dawowa gidan mahaifinta a karkashin kulawar Amma ta san ko ba komai zata fi rika ta da daraja fiye da Momy da har yanzu take nuna musu banbanci. A lokacin da ta dawo sai Amma ta saka hannu biyu ta karbe ta kamar komai be faru ba, har zuwa lokacin da ta kammala karatunta ta samu Miji Amma ta yi mata komai da ya kamata tare da taimakon Sapna da Amma take janyowa a duka al'amurran gidan kasancewarta babbar yar Appa gashi kuma yanzu ta dawo kusa da su da zama saboda Appa ya siya mata gida a cikin garin Gusau.

An yi biki cikin farinciki da jindadin yan'uwa da yawa sun samu halarta ciki har da matar Fadeel da zumunci ya daure tsakanin Yasir da Fadeel din kamar wasu yan'uwansu, matansu ma suka kulla, waton matar Yasir Rukayya da ta zame ma Ruma, kamar babban yaya gurin shawarwari da wasu abubuwan na rayuwa. Yasir ya tsaya kamar Appa idan ana bukatar wani abun shi ake yi ma magana ba Appa ba domin ya dauko girman ya rayata a wuyansa tun kamin yayi aure ma balle kuma yanzu da yake da yara biyu da matarsa. Kusan kowa tambaya Khairy yake yaushe zata yi aure ganin ita ce Babba amman shiru har yanzu ko mashinshi babu, Yayarta Maama ce take dan tare mata wani lokacin tana cewa ai aure lokaci ne ita ma zata yi idan lokaci yayi, gashi kanenta Hurriya da Ruma sun yi sun barta, abun ya taba ta sosai domin tambayar mace yaushe zata yi aure ba abu ne mai dadi ba balle kuma ita da kaddara da fadawa. Har aka ci aka shude bakin Namra be hadu da na Hurriya ba, har yanzu da kowace ta yi aure take da Yaya Namra bata shiga safgar Hurriya ta riga ta tattara lamarinta ta aje gefe daya.
Ko a lokacin bikin aurenta ma haka ta yi mata kamar ba yar'uwarta ba, zata yi magana ko mu'amala da kowa ban da Hurriya da zarar sun gaisa bata sake tambayarta komai. Tun abun yana damun Hurriya har ya daina domin ta san babu ta inda take da laifi, abu ne da Allah ya riga sa ya tsara shi babu yadda za a canja.
Chapter 132 · 0% Book details