← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 133

Sashe 130

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Hamad me zaka ci?”

“Haba Baby ina lallabaki ki ci abinci ke kuma da wannan gwaskan kike? Babu inda be sani ba a garin Addis Ababa ki daina damun kanki da cinsa”

“Ko a gida haka muke, inda har zan ci abinci to zan zuba masa ne ya ci, ka yi hakuri

Yaja hancinta yana murmushi.

“Tsokanarki nake, tambaye me yake so sai na siyo muku”

Hamad yayi murmushi yana ganin kamar mafarki ne, wai yayarce da mijinta zaune tare da shi a yau.

“Yayata mai kaunata yar'uwata abar alfaharina”

“Ba ka ce ni ba yayarka ba ce?”

Ta tambaya tana hawaye shi ma hawayen yake yana murmushi.

“Ada kenan yanzu na bar miki girman”

Ta yi murmushi cikin hawaye, Captain ma Murmushi yayi ya tashi ya fita.

Ya sake daukarsu awa biyar da mintuna kamin su iso Nigeria daga babban birnin Ethiopia. A Abuja suka sauka, ba su tsaya komai ba suka sake booking flight from Abuja to Kaduna, Ammy ta yi musu tarba ta musamman tana ta na'am na'am da matar danta kamar daman can babu wani abun da ya taba shiga tsakaninsu. Sai da suka yi wanka suka huta sannan suka hadu a teburin cin abinci da yake gidan. A nan Hurriya ta gane ubanta Alhaji Haruna Mai Yadi karyar arziki yake domin falon Ammy ma ba tile ba ne wani abun ne aka shimfida mai kamar ruwa, ga manyan kujerun da bata taba ganin kalarsu ba a rayuwarta, dinning din ma wani abun kallo ne a gurinta balle kuma dakin da suka sauka. Ko'ina na gidan kyalkyale ni kamar an watsa zinari. Bakauya ta zama a gidan komai ta gani sabo yake zama mata, a nan ta yarda da Momy take ganin kamar bata dace da auren Captain ta bangaren arziki. Masu aikin gidan ma kansu abun kallo ne basa barin komai ya zuba a kasa da zarar an aje abu za su zo da gudu su dauke.

Captain da kansa yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna yana magana da mahaifiyarsa da ta zabi serving din matarsa da kanta ba kamar Momy Ikilima da Mama Rukayya da masu aiki suke zuba musu abinci ba, sai da ta fara ajewa Hurriya plate din abinci sannan ta zubawa Captain ta aje masa warin kwai dake kan salad ya saka shi jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai.

“Me ya faru wani abu ka gani a abinci?”

“No kwan ne na ji shi wani iri, bana son warinsa”

Ammy ta dauke plate din ta zuba masa wani abinci babu kwai har ya fara ci sai kuma ya ji baya son abinci kawai wani abun kwadayi yake so.

“To ko dan kun yi tafiya a jirgi ne?”

“Ammy karki sa na ji kunya mana, yau na saba hawan jirgi?”

Hamad ya kalleshi.

“Ko dai baka da lafiya ne?”

“I think so, jikina ma yayi zafi, tun da muka je ba wani lafiya nake ji ba, kawai dai ina daurewa ne saboda akwai abubuwa da yawa a gabana”

Ammy ta kalli Hamad.

“Wannan ne yaron? Shi da wanda kake yawan zuwa Ethiopia gurinsa daman? Da zarar ka samu sarari sai ka tsallake ka tafi Ethiopia ashe duk saboda shi ne?”

“Wallahi kuwa Ammy”

“Bari na kira Family Doctor ya dubaka kamin ku tafi”

“Okay”

Ammy ta tashi ta bar dinning din, Captain ya kalli daya daga cikin masu aikin gidan ya ce.

“Samo min wani abu mai ruwa ruwa na sha”

“To ranka ya dade”

Sai da Ammy ta kira likitansu na gida ya zo ya auna Captain ya duba shi ya fada musu fever ne kawai yayi masa allura ya kuma dorashi akan magunguna sannan suka bar garin Kaduna a business flight din Daddy da baya kasar domin ta waya ya gaisa da Hurriya yayi mata maraba da zuwa gidansa kuma ya saka Ammy ta hada mata goma ta arziki a madadinsa.
[1/8, 9:53 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*

5️⃣9️⃣

Ya bude Mota ya saka matarsa sai da ya sumbanci hannunta sannan ya rufe motar ya zagaya dayan side din ya shiga ya sake sumbantar ya kama hannunta ya rike yana tuka motar.
Wani irin farinciki yake ji marar misaltuwa a zuciyarsa, be taba tunanin haka ake ji ba idan mace tana dauke da cikin ďan mijinta sai yau, baya iya bayyana yadda yake ji a zuciyarsa son matarsa ya ninku a ruhinsa.

“Ki kula da kanki please”

Ya fada a lokacin da ya bude mota ta fito. Ya waiga ya ga idan babu mai kallonsu sannan ya juyo ya rumgumeta ya sumbanci goshinta. Ya kama fuskarta ya aika mata da wani killer look.

“I Love You so much sanyin idanuwana, thank you for this”

Ya taba cikinta. Hawaye ya zubo idonta ita kanta she can't believe ciki ne a jikinta so she's going to be a Mother now..

“Ni ya kamata na gode maka, you came in to my life by accident sai kuma ka zama cikar farincikina, abokin rayuwata, silar share hawayena, ka min alkawarin kyakkyawar duniya mai ciki da farinciki kuma ka fara va ni tun a yanzu... Buri yana ta cika saboda kana kusa da ni, ina matukar kaunarka Jamal duk mace da ta samu namiji irinka a matsayin miji hakika ta dace da Abokin Rayuwa na gari mai son farincikinta, kai din wata babbar kyauta ce da Allah yayi min ta inda ban yi zato ba kuma a lokacin da ban yi zato ba...”

He weep her tears yana murmushi ya sumbanci bakinta ya latsa kasan lips din.

“My cute Baby my happiness, anything for this Girl”

Ta yi murmushi ta sauke hannunsa kasa.

“Kar wani ya gan mu fa...”

“Zaki kwana gidan nan ne just for today, i can't wait na bude ido gobe na gan ni a kusa da ke, i love you”

Zata amsa masa da i love you too Hindu da Inna Uwani suka fito, sai ta yi saurin juyawa daga fuskantarsa da take ta kallesu.

“Hurriya ke kika yi amai dazun? Twin yace mana ga aman nan a waje Rukayya ta kwashe kuma sai ba mu ganku ba..”

“Eh Captain ne yayi ba shi da lafiya tun a gida shi ne yau sai yayi amai, yanzu ma na raka shi asibiti ne aka ce malaria ce take damunsa”

Captain ya kalleta da sauri, jin yadda ta daure shi a take tace shi yayi mai kuma shi ta raka asibiti.

“Subhanallahi... Jamal babu lafiya?”

Hindu ta tambaya, sai dan yi shiru kamar wanda ya rasa me zai ce.

“Eh...... Amman da sauki asibiti muka fito yanzu suka ce Hurriya...”

Ta kalleshi da sauri tana zare masa ido. Sai ya sauya maganar daman yayi haka ne kawai saboda ya tsorata shi ba zai iya fadar tana da ciki ba a gurin yan'uwanta.

“Sai suka ce ma Hurriya ina dauke da malaria”

Ta daga mishi kai alamar haka ne daidai.

“Sannu har da gajiya ai, kana kokari sosai Wallahi....”

“Na gode zan tafi sai da safe...”

Ya musu sallama ya bude Motarsa ya shiga yana jin zazzabin da Hurriya ta kira masa yana kara rufe shi. Hindu da Inna Uwani suka nufi gate Hurriya kuma ta shiga bangaren mahaifiyarta tana jin komai kamar ba gaske ba. Ta daga kai tana kallon bangaren bayyana yadda farinciki yake a gurinta yanzu abu mai wahala, mahaifiyarta ta dawo a karkashin inuwar mahaifinta a yayinda ita kuma take karkashin kulawar nata mijin, ga dan'uwanta a kusa da ita. To yanzu me ya rage mata? Mai hakuri mawadaci wahala ko bakinciki basa taba daurewa a rayuwa, haka ma dade da farinciki basa dauwama har abada, sai an bude ko wane shafi na rayuwa... Ta shafa cikinta tana murmushi ta samu amincewar ubangiji zata iya ganin abun da ta haifa nan gaba. Jin kukan Rukkaya ne ya kawar mata da duk wani tunani da take a lokacin sai ta yi hanzarin shiga cikin falon dake dauke da mahaifiyarta, Gwaggo da kuma Rukayya.

“Ashe baki da hankali har yanzu? Ke yanzu duk wannan abun da ya faru har sha'awar auren Yasir kike...”

“Allah yana fitar da mai kyau daga mummuna gwaggo kuma yana fitar da mummuna daga mai kyau, ni ban ce sai na auri Yasir ba, ban zan iya auren mutumen da zuciyarku bata gamsu da shi ba, amman dai na sani farinciki ko wane ďa yana tare da uwarsa, idan aka kai Hajiya Gidan yari, Yasir ba zai sake farinciki ba, ni kuma nawa farinciki yana tare da Yasir, dan Allah Yaya Iyami karki saka a rufe ta Allah ya riga ya gama miki komai...”

Tassss Gwaggo ta wanke fuskar Rukayya da mari.

“Ke yanzu soyayya har ta isa ta rufe idonki ki ce kar a hukunta Kaltume akan abun da ta yi?”

Amma ta bata rai sosai tana kallon Gwaggo da alamar dake nuna bata jidadin marin da Gwaggo ta yi ma kanwarta ba.

“Da baki mareta ba Gwaggo, soyayya babu abun da bata sakawa, idan har so zai rufe idon mutum kamar Jamal ya yarda da Hurriya ya aureta a lokacin da take cikin tsananin rayuwa da damuwa, me zai hana so ya rufe idon Rukayya? Kuma gaskiya ta fada, ni Allah ya gama min komai daman idan mutum ya cutar da kai karka ce sai ka rama kawai ka bar shi da Allah sakamakon da yake zuwa daga gurin Ubangiji ga azzaluman mutane mai tsanani ne, irin wanda ruhi baya iya jurewa. Kuma Yasir ya cancanci ko wace kalar alfarma a gurina ko a gurin yayana, yana da kirki be taba nuna min banbanci da mahaifiyarsa ba ko sau daya...”

“Ko ma dai minene ba za a kyale ta ba, tun da na gane hankalinki da nata ya zama iri daya”

“Daman maganar ba a gurinmu take ba, tana gurin jami'an tsaro ne sai yadda suka yanke..”

Gwaggo ta ja tsaki tana jin haushin yadda Amma take da sanyi a wannan bangaren. Hurriya ta karasa ta zauna a kusa da Rukayya tana bata hakuri.

“Barta ta yi ta kukan, ta dade bata mutu ba yara ba su da kunya soyayya na rufe musu ido su kasa ganin daidai”
Chapter 130 · 0% Book details