← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 133

Sashe 57

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To ai shi ne abun da ya bani mamaki, na ce ya aka yi baka tuntune ni da maganar ba”

Hajiya Fatee ta daga mata hannu.

“Dan saurara Hajiya bari yayi mana bayanin komai, shiyasa ai na kira shi na ce ya zo, gaki gashi ayi magana zai fi yi a waya, tun da mu ba zamu iya zuwa garin ba”

“Wato Hajiya Fatee ina cikin tashin hankali ne, maganar auren nan Alhaji ta daga min hankali kwana biyun nan har mafarkinta nake, kuma ga ďana Yasir ya sako ni gaba da zancen auren Rukayya kanwar Iyami”

Hajja Fatee ya daki kirji.

“Kanwar Iyami fa kika ce Hajiya Kaltume”

“Ita fa, kin san ai ba banza suke barin maza ba, ga fitinar Maama da fitinannne mijin nan nata, kai ni kam haukacewa ne kawai ban yi ba, amman hankali ba shi a kwance yanzu, idan na toshe wannan hanyar wata ce zata bullo”

“Dole ki shiga cikin tashin hankali kam, Malam kana jin wannan lamari”

Malam yayi murmushi.

“Babu abun da bana gani na a cikin kasar nan duk dare ina duba abubuwa kuma ina ganin yadda suke gudana, wasu abubuwan ina ta iya kokarina na ga na danne abin wani abun kuma idan ya gagareni sai dai na yi shiru, na shiga tunanin da bincike yadda zamu samu mafita, shiyasa ban fada mata ba”

“Malam akwai matsala kenan?”

“Matsalolin ba ma kadan ba, kuma ina gudun ki shiga tashin hankali ne shiyasa bana tunkararki da irin kalaman nan”

Hajiya Kaltume ta kalli kawarta da ita kallonta take dukansu suna cikin tashin hankali da damuwa, musamman ma Kaltume da ita abun ya fi shafuwa.

“Malam dan Allah dan Annabi karka rufe min komai ka fada min gaskiyar komai da komai”

Malam ya sauke ajiyar.

“Gaskiya ne Alhajinki yana neman aure, kuma magana ta yi nisa yanzu haka yarinyar ma shi yake bata kudi tana hada lefe, yarinya ce karama da ba zata wuce sa'ar yarki ba....”

Hankalin Hajiya Kaltume ya kara tashi domin ba ta yi zaton, da gaske Salma take ba sai a yanzu, wani gumi ya karyo mata mayafin dake kanta tana jin kamar yana shaketa.

“Malam ta ya muna da kai a garin nan? Kuma tuntuni baka fada min ba Malam sai yanzu da na tunkareka da maganar amana bata ce haka ba Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, na shiga uku ni Kaltume ban gama warware wasu matsalolin ba wasu na son karuwa? Yaushe Iyami ta bar gidan? Ga Nafisa ma ta hana ni rawar gaban hantsi ita ma fata nake ta tafi, sai kuma ka ce min Alhaji na neman aure? Haba Malam ka dai sake bincikawa”

“Babu bukatar sake bincikar abun da yake zahiri nake gani kowane dare idan na duba, ban sanar da ke ba ne saboda ina ta kokarin ganin na daidaita abubuwa, kuma ki kwantar da hankalinki yadda Iyami bata gagaremu ba, ita ma da take gidan balle wannan da bata shigo ba?”

Hajiya Kaltume ta ranka tagumi kamar zata fashe da kuka. Hajiya Fatee ta kai hannu ta dafa ta

“Ki kwantar da hankalinki Hajiya babu abun da zai gagara, Malam yanzu me ye abun yi?”

“Abun yi za'ayi aiki, amman zata kashe kudi sosai daga kan Mijin nata har zuwa kan danta, za a musu Farraqu da ita yarinyar, mijin nata ma za a masa irin aiki”

“Amman Malam kai da bakinka ka ce mana yanzu babu kowa a gaban Alhaji yanzu sai ita, taya kuma har maganar aure ta shiga tsakaninsa da wata?”

“Wato Hajiya Fatee akwai abubuwan da rufewa muke yi saboda kar hankalinku ya tashi, amman maganar gaskiya ita kanta yarinyar tsaye take akanta kuma da karfi da yaji so take sai ta shigo gidan mijinki, shiyasa kika ji na ce miki za a kashe kudi, domin aiki ne mai matukar nauyi, duk kokarina abun yana neman gagarata wata kila sai koma gudin malamina sai shi fa da rakuma gake aiki, sai dai babu makawa duk abun da aka bukata ana samu”

Cikin wani irin yarinya na razanarwa Hajiya Kaltume ta kalleshi ta ce

“Malam wace irin yarinya ce da zata gagareka har sai ka tafi gurin malaminka? Malam ita ma bokanya ce ko kuma Aljana”

“Ba ko daya, amman tabbas tana da karfi sosai, na gani shi kansa mijin naki hankalinsa tashe yake akanta, baya iya musa mata fiye da yadda baya iya musa miki, gashi kuma mun riga mun saka masa tsoronki balle ya tunkareki da maganar, duk wani abu da yake a boye yake yinsa, amman ki tunkare shi yau da maganar, zaki tabbatar da abun da nake fada”

“Yanzu Malam babu yadda za'ayi a hana auren nan?”

“Akwai fa, amman na fada miki za'a kashe kudi, dan haka ki je yi shawara idan kin ga zaki iya sai na sanar masa?”

“Malam kana ganin za a kashe nawa?”

“Kudi mai yawa, domin sai an yanka rakumi kuma ba zan iya yanke hukuncin kudin yanzu ba, domin sai an bincika anji ko nawa yake, shi kadai za'ayi ba, bayan nan kuma za a bashi karam alkamin kamin a biya kudin aiki idan bukata ta biya”

“Shikenan Malam zan yi shawara, zan kiraka daga baya”

Cewar Hajiya Kaltume cikin tsananin damuwa, ta saka hannunta a jaka ta ciro kudin da ba za su wuce 5k ta aje masa.

“A kara a hau mota”

Ta mike tsaye ta dauki jakarta, Hajiya Fatee na ganin haka ita ma ta mike tsaye ta bi bayan kawarta, sai da suka fito harabar gidan sannan Hajiya Fatee ta ce.

“Na so ki kwantar da hankalinki ki yarda ayi miki aikin nan kawai”

“Rakumi kika ji fa yace na bayar Hajiya, kin san nawa ne kudin rakumi a yanzu?”

“Biya bukata ai ya fi dogon buri, da ace Alhaji ya sake yin aure ya dauko muku wata ita ta zo ta fara nata yayan ana fifi ta ta akanku ai kara ma ba'ayi ba”

Hajiya Kaltume ta leka bayan Hajiya Fatee sannan ta kama hannunta ta kara janta gefe.

“Ni fa ina ganin kamar mutumen nan akwai yaudara a lamarinsa? Bayan na min alkawarin cewar Alhaji ba zai sake auren wata ba kuma ba zai so wata ba sai ni? Ta ina to yaga yarinyar har ya so ta? Kuma yanzu ya na zancen na siya rakumi, yana kwance aikin da yayi ne saboda ya bukaci wani abu, haka kwanan baya yake ce min wai haske a dakin Hurriya kuma ya tare masa ganin komai, ke idan na yaudara ba ta ina zai ce baya ganin komai? Akwai abun da yake boye min dai shiyasa yake fadar haka”

“Idan ma wani abun yake bukata, ki ba shi kawai, ke fa naki mai sauki ne, kudi ne kawai matsalar, ni fa aljannu ne da kansu suka bukace ni”

“Ke tsaya wai ke me ya bukata a gurinki”

“Aljannun da yake aikin ne da su suka bukaci sai sun kwanta da ni amman a jikinsa, kuma tun da na amince sai komai ya wuce, bukata ta biya ciki ya koma, ai na fada miki yadda Fadeel yake dokin auren Khairy a yanzu, da kuwa idan na masa magana kamar na fada masa mutuwa haka yake bata rai, wannan Afrah da ta gagara ma yanzu na samu kanta, ya juya mata baya, ashe daman a baibaiye nake aikin, wai ita baya kamata ni kuma ban gane kan zaren ba sai a yanzu shi da kansa yace Fadeel din ya kamata mu yi ma aikin ba ita ba, kuma yanzu komai ya daidaita”

Hajiya Kaltume ta yi wani sukuku tana kallonta kamar wata mai tunani. Hajiya Fatee ta dafa kafardarta.

“Ki kwantar da hankalin, wannan mutumen amintacce ne, ni Wallahi na yarda da shi dari bisa dari, yanzu haka akwai kudin da na damka masa, zai siya min gona a kauye, wata shekara ni ma zan fara noma, yace min babbar gona ce zan yi mamakin abun da za a girba idan aka yi noma a gurin!”

“Yanzu amincinki da mutumen nan ya kai har ki dauki kudi mai yawa ko bashi ya siya miki gona? Kuma da alama ma baki je kin ga gonar ba?”

“Na yarda da shi ne fa”

“Yarda? Mutumen da ba danki ba ba dan'uwanki ba? Kuma ba dan cikin gari ba? Anya kina cikin hayyacinki kuwa Hajiya Fatee? Mutumen nan fa abun da ke tsakaninmu da shi mu bashi kudi yayi mana aiki”

A wani yanayi na rashin jindadi da kuma gamsuwa da maganar da Hajiya Kaltume take, Hajiya Fatee ta gyara tsayinta ta ce.

“Yarda ta kawo haka? Idan babu yarda ai ba zamu bada kudin aikin ba ma, kuma ke ma da baki jidadin aikin da yayi miki ba a akan Hurriya da Iyami da baki kai shi makka ba, kuma ni ina ganin babu laifi a cikin shawara, shawara ce yayi min na abun da yake ganin ya dace ke kanki da kika kawata baki min irin wannan shawarar ba, kuma da babu yarda ba zan kira shi ya shigo har cikin gidana ba”

“Duk wani abun da zamu masa a babin kyautata ba laifi ba ne, amman kulla kasuwanci ko fada masa sirrinki har ya san nawa ke ganinki wannan abu ne na sirri da be kamata ki yi ba, dan Allah Hajiya Fatee ki farka daga wannan bachin da kika fara”

“Hmmm ba zaki fahimta ba Hajiya Kaltume, ke dai tafi kawai sai kin natsu zamu yi magana”

Tana maganar tana girgiza kai tana mamakin yadda kawar tata ta kasa fahimtarta a yau.

“Shikena zan kira a waya”

Hajiya Kaltume ta nufi motarsa ta bude ta shiga, direbanta dake zaune yana jiranta. Hajiya Fatee kuma ta juya ta koma gida. Ita dai har ta isa gida mamakin amince da yarda da kawarta ta dauka ta bawa Malamin da za a iya kira da boka, ita da bata da saurin yarda da mutane, ko da tsoronsa take ne. Can kuma wata zuciyar ta tuna mata da abin da ta manta.

‘Ai ya kwanta da ita, wata kila ta nan ya samu sa'ar mallakarta da wannan mallaka ce kawai’

“Ai ka ji matsalar, ba kwanciyar ba mallaka, da babu mallaka ma ai da sauki”

Ta fada a fili, har direbanta ya juyo da sauri yana amsawa.

“Na'am Hajiya”
Chapter 57 · 0% Book details