← Book details Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 133

Sashe 101

Hurriya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin shidewa ta yi luuuuuuu jikinta ya sake saki, har sai da matan suka jin tsoron wannan suman nata na biyu, Hajiya Kaltume kuma tana zaune a gurin ta kasa aikata komai sai kuka take kamar ita kadai ta rasa Malam. Ruwan aka sake zuba mata sannan ta farfado tana kallon matan karkarrar dake juya mata tana jin sannun da suke mata kamar a mafarki, fada mata da matar ta yi cewar Malam ya rasu ma sai ta ji abun shi ma kamar mafarki ne ba gaske ba.

“Abun da zai fi akaisu gidan Matan Malam ko kuma a kaita asiri”

Wata daga cikin matan dake rike da ita ta fada, Hajiya Kaltume ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce.

“Ina ne gidan”

“Daga nan ne yamma kusa da kuka uku, Sslmanu wuce gaba ka kaisu”

Yaron da aka kira da Salmanu ya dauki tayarsa da karen kada tayar ya wuce gaba yana zumuncin nuna musu hanya, ganin mutanen daga birni suka zo. Ba dan taimakon Allah da rahmarsa ga bayinsa ba da Hajiya Kaltume bata kai kanta gurin motar da suka shigo ba, domin gaba daya kafafuwan rike mata suka yi, Hajiya Fatee kam sai da aka riko aka saka ta motar idonta sai juyawa yake kamar bata san inda take ba. Yaron ne ya wuce gaba da tayarda yana turawa su kuma suna cikin motar zaune a baya, Hajiya Kaltume ce kadai ke iya kuka a yanzu Hajiya Fatee kam kai kawai take juyawa kamar mai kokarin fita daga hayyacinta, direbansu na biye da su har suka isa katon gidan ginar bolu kana ganin gidan da ba'ayi ma filista ba ka san ba duk kauye ba, ko a kauna sai wanda ya tsaya da kafafuwansa.

“Wai yanzu da gaske Malam ya mutu Hajiya Kaltume? Shikenan Malam yayi tafiyar da babu dawowa? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, shi ke nan ta kare min dari ta hade min da dubu, Wallahi ganin nake kamar ba gaske ko dai mafarki nake Kaltume?”

Hajiya Kaltume kam kaddara ta riga fata, bata iya cewa Hajiya Fatee komai a yanzu domin ita ma bata da wannan kwarin guiwar. Hajiya Fatee ta unkura zata fita ta kasa saboda jiki yayi nauyi a zaunen da take ma jiri ke debanta yana zubarwa.

“Dukiyata.... Cikin nan..... Ga Afrah... Indai Malam ya mutu a yanzu Malam be kyau min ba”

Direban motar ya juyo ya kalli Hajiya Fatee dake sabbatu tana wani mashalo kamar mashayiya. Cikin gidan Hajiya Kaltume ta shiga babu ko sallama sai tafiya take a gajiye, daga a tsakar gidan ta fadi zaune tana kallon matansa dake zaune da kayaransa.

“Daga tsohon gidanku muke aka fada Malam ya rasu, dan Allah ku ce mana ba gaskiya ba ne”

Karamar ta sauke kai kasa idonta na cika da kwalla, mai karfin halin ce fa amsawa Hajiya Kaltume.

“Malam kam rai yayi halinsa ya riga mu gidan gaskiya, sai dai mu bishi da addu'a, ba Malam kadai ba har da yara biyu”

Hajiya Kaltume ta rushe da kuka tana dora hannu akai tana ihu kamar zata tara musu mutane.

“Kashi na ya bushe a yau, ashe shiyasa komai yaki daidai, na zuba kudi ina duban Malam yana nan yana aiki ashe Malam yana barzahu, na kira waya shiru ashe babu Malam”

Matan suka taso suka rika Hajiya Kaltume suna kuka domin ta tsikaro musu bakincikin rasa mijinsu da suka yi. Hakuri suka rika bata sannan suka rikata suka zaunar da ita a ciki barandar gidan (Balcony) dayar ta debo mata fridge ta aje mata sannan ta zauna tana bata labarin abun da ya faru tana kuka.

“Kin ga gidan nan be dade da gama shi ba, ya saka komai a ciki tv da fridge irin na yan birni ya saka mana, kayan daki ma masu kyau ya zuba mana, na dubu 70k, duk kauyen nan sai labarin gidan nan yake ashe Allah be kaddara a koma tare da shi ba sai bayan ransa”

Hajiya Kaltume ta sharce kwalla ta girgiza kai tana kuka, kai ka ce kukan rashin Malam kawai take da gaske ba kukan neman mafitarta ba.

“Yaushe ya rasu?”

“Yau kwana tara, kuma mutuwarsa ta bawa kowa mamaki, shiyasa har wasu suke zargin ko jifansa aka yi, domin Malamai suna haka, idan aka ga ka taso ana yi da kai a gari sai hassada ta shiga ciki”

Dayar ta karba mata.

“Ai ba kama ba ce wannan abun jifa ce kawai, domin yana cikin aikinsa karfe daya na dare sai wuta ta fara kamawa a dakin, ihunsa kawai muka ji muka fito aka yi ta dukan kofar ta ki budewa sai da ta cinye shi tass, kuma wutar bata tsaya nan na haka ta bi gidan nan ta cinye komai har da yarana biyu iro da dan inna, zane wannan na daurawa ba mu fita da shi ba, sai da makota suka kawo mana Hijabai, bayan wutar ta cinye komai ta kama ginin gidan ta kone kamar watsa fetur, wannan abun ya bawa kowa mamaki bayan an yi masarar kashe wuta aka bude dakin wuta ta ci Malam abun babu kyau gani, haka ma aka saka shi ba tare da an yi masa wanka ba sallah akwai aka yi masa aka saka shi a rame, saboda jikin ya kone wanka ba zai yi ba”

Ta karasa cikin kuka.

“Dole ayi masa jefa mana, a kauye ne wane Malami ne yake irin aikinsa? Babu shi kuma gashi Allah ya amince masa komai girman gona ko gida sai aji Malam be ya siye va dole hankalinsu ya tashi ba, mota ma wannan wanda Malam yake hawa abar kallo ce”

Hajiya Kaltume ta Kalli babbar matarsa tace.

“Amman duk wanda ya aikata nasa wannan abun mu ya aikatawa ba Malam ba, mu ya jefa a matsala”

“Haka kowa yake fada, ga Malam da mutane manyan mutane kala kala gari gari zuwa ake saboda iya aikinsa, kowa ya zo cewa yake ba mu aka yi ma mutuwa ba su aka yi ma”

“Wannan abu be yi dadi ba, Kawata na kiran wayarsa a kashe kullum ina sauraren ko zai kira amman shiru ashe wani labarin ake na dabam”

“Malam ai be fita da komai ba, wayarsa ko ganinta ba ayi ba”

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya, idanuwanta suntun suntu tsabar kukan da tasha.

“Kuma be bar muku sakon komai ba?”

“Ina zancen barin sako a mutuwar da ba a san da zuwanta ba balle a shirya mata, kuma ko da ya bar wani abu ai wuta ta kone komai ina za a gani ma”

“Ba shi nake nufi ba, sako haka ko na kalami cewar an turo masa kudi ko kuma kudin da filin da yake guri kaza ba nasw ba ne? Ko gona?”

“Aa babu kayan kowa a hannun Malam, domin idan ya siye gida ko gona ko fili ya kan kiramu ya fada mana cewar gidan da yake guri kaza ko fili ko gona sun zama mallakinsa ya siye, har takardun da ake yi na shaida yana nuna mana, kuma yawanci idan sai siya da aminsa yake zuwa Malam Musa, bayan rasuwarsa kuma Malam Musa ya hannata mana komai na Malam kuma ya bi mutane da dan abun da yake hannun malam na mutane aka biya, babu hakkin kowa a gurin Malam yanzu”

“Da dai zan samu ganin Malam Musa na yi magana da shi, saboda akwai mai yawa da na turo masa a account da sunan zai tafi gurin Malaminsa yayi min aiki, kuma kawata ma Hajiya Fatee ta bashi kudi mai yawa ya siya nata gona da fili a kauye, da zan ga Malam Musa sai na tambaye shi ko ya san wani abu a kai”

“Gaskiya babu, kuma wani be taba zuwa mana da irin wannan maganar ba sai ke, amman saboda kaucewa zargi, bari a kira Malam Musa sai ku yi magana da shi”

Amaryar ce ta aika yaro gurin da ta san aminin mijinta na zama aka kirashi, da ya iso ya shigo cikin gidan suka gaisa da Hajiya Kaltume ta yi masa gaisuwa sannan ta kora da bayani.

“Ni sunana Hajiya Kaltume akwai kawata Hajiya Fatee tana mota yanzu haka, mutuwar ta taba ta sosai ba zata iya takowa nan ba, ni na tura masa kudi kwana goma da suka wuce ko sha daya, kudi mai yawa akan cewar zai kawai Malaminsa ayi min aiki domin wannan aikin ya fi karfinsa, yace Malaminsa zai siye rakumi da kayan aiki, shi ne nake tambayar ko ka san wani abu akan haka”

Mutumen da ake kira da Malam Musa ya girgiza kai.

“Aa Wallahi be yi wata magana kamanciyar wannan ba, kuma Malam ai Malaminsa ya dade da rasuwa shekara kusan goma sha wani abu yanzu”

Hajiya Kaltume ta yi tagume.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un...”

Tana jin wani sabon kuka na taso mata.

“Ita kawata dake mota har filaye take bashi kudi ya siya mata da gona ita be yi maganarta ba ko? Ko kuma ya bar wata wasiya? Ko a cikin gidajen da yake siye yace wannan na Hajiya Fatee ne ko na wata”

“Aa babu wannan, Malam be taba fada min haka ba, Maimuna a cikinku akwai wanda ta taba jin magana makamanciyar wannan abakin Malam”

Uwar gidan ta girgiza kai.

“Aa ai na fada mata ba mu san wani abu da Malam ya siye ya ce na wani ne ba, sai dai idan sheri za'ayi masa anji ya bar dukiya a haka kai da mutanen birni azo ace za a kwace”

“Aiko ba zata sabu ba, komai ai sai da hujja ake yinsa, Malam yana kafa shaida idan zai siye abu, har takardu ana yi sai dai wutar da ta kone komai yasa ba a tsira da takardun ba, amman shaidu ai suna nan da ransu, babu wanda ya isa ya zo mana daga wani guri da sunan dan boko ya karbi duniyar Malam, idan ma manufar ku kenan to tun wuri ku tashi ku kama hanyar garinku ko na tara muku mutane yanzu nan”

Hajiya Kaltume ta daga kai ta kali mutumen da ya mike tsaye yana nuna mata kofar fita bakinsa da asuwaki hannunsa kuma rike da carbi.
Chapter 101 · 0% Book details