← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na dubi Naseem da Nasmah ina faÉ—in
"Kutashi muje ko." ido
Naseem ya kura min yayin da hannayen sa biyu ke dafe da kuma tun sa kana ya ce "Mommy mataiyaci amuje?".
Nasmah ma tace "Tayan kaya amuje ko Mommy?." kai na girgiza musu nace
"Ba siyan kaya ko masallaci zamu je ba, kasar mu zamu koma can kasar mu in da aka haife mu."
ido yaran suka ware suna kallona kana Naseem yakuma cewa "Mommy kasar mu in da aka haife mu?."
yy maganar yana zura yatsarsa cikin baki alamun mamaki irin na yara.
kai na gyaÉ—a masa tare da ruko hannunsu ina faÉ—in "Kutashi muje." dan nasan idan nabi na surutun su sai mu makara anan har Bappa yakuma kira.
Ukhtee kuwa tuni idanunta suka kawo
ruwa kan kace me hawaye yafara sauka,
hannunta na rike cikin rauni tare da girgiza mata kai dan nima idanuna sun fara tara kwalla.
cikin harhaÉ—a larabci nace
"Dan Allah Ukhtee kar kisa jikina yayi san yi, baga waya ba zamurika magana ai tafiya ba mutuwa bace ai dai bamu rabu ba tun da akwai waya zamu rika gaisawa, bakin ce zaki zo kasar mu ba?."
kai ta gyaÉ—a min alamar Eh nace
"To dan Allah kada ki karya min guiwa da tafiyar kizo muje kin ga Bappa sai kira yake."
jiki a sanyaye ta mike.
koda muka fito parlour sai gani nayi babu akwatin kayan mu in da nafito da shi na ajiye É—azu bayan nagama shirya mana kayan mu.
nan Ukhtee take sanar min direba ne yashigo ya É—auka.
koda muka fita farfajiyar masarautar, a tsaye jikin mota muka tadda direba da alamu mu yake jira.
da sauri na juya na nufi side É—in su Ukhtee dan yiwa Mammaa sallama,
narika bin part-part na masarautar ina yi musu sallama duk in da na shiga sai na fito da ƙwalla dan suma da kwallar suke rako ni,haka narika bin side mafi kusa da mu ina yi musu sallama dan idan nace zanbi na nesa da mu sai na kusan sai na ɓata lokaci mai tsawo ban gama ba.
daga karshe nashiga can cikin masarautar in da lokacin da mukazo aka canza diamonds É—in nan aciki.
direct cikin katafaren parlour wan da aka kawata shi da adon zinari mai matukar É—aukar ido muka shiga, adalin shugaba na zaune a mazaunin sa na alfarma, yayin da Alkur'ani ke gaban sa yana bita cikin nutsuwa. a gaban sa muka rusuna, cikin ladabi nayi masa barka da war haka,kafin nakuma cewa wani abu ya É—aura hannunsa a kai na yana yimin fatan isa kasata lafiya, nayi mamakin yan da yasan abun da ya kawo ni dan ni a zato na bai san da tafiya ta ba. naji daÉ—in addu'o'in da yayi min kwarai da gaske, na mike cikin jin daÉ—i yayin da jikar sa wato Ukhtee ta rufamin baya, bayan itama ta gaishe shi, gaba É—aya cikin parlour'n suka shiga yimin fatar isa gida lafiya ina amsawa da amin har muka fita.
a jikin mota na tadda su Mammaa cikin matukar bege kowa sai hawaye yake har sai da suka sa hawaye na ya karu.
direba na ganin mu yayi saurin buÉ—e motar yariko hannun su Naseem yasa su cikin motar, rungume juna mukayi da Ukhtee muka saki kuka a tare, gaba ki É—aya gurin hawaye suke babu mai iya rarrashin wani,
zame jikina nayi cikin sauri nashige cikin mota, direba yatada motar.
motocin da suke jere a gaban mu guda uku sai wasu biyu a bayan mu,
motar farko mai tambarin masarautar haÉ—e da jiniya, shi ya fara fita, kafin biyu suka bi bayan sa sai kuma motar da muke ciki.
motoci biyu da suke bayan mu suma suka biyo mu, kamar dai ranar da muka shigo masarautar sai gashi yauma a haka muka fita.
muna isa airport batare da ɓata lokaci ba muka shige cikin jirgi, nan motocin suka juya.
bada jimawa ba jirgin ta É—aga...

Bayan wasu ƴan awanni jirgin mu yasamu sauka cikin yar dar Allah da buwayar sa, cikin babban birnin tarayya Abuja da ke cikin kasata ★NIGERIA�.
bayan saukar jirgen da kamar minti 15 fasinjojin ciki suka fara sauka.
da sauri ganin Naseem da Nasmah sun mike kan kace me sun rufa da gudu sunyi bakin kofar fita in da mutane keta sauka,
cikin hanzari na rufa musu baya da sauri ina faÉ—in
"Kai kutsaya fa kar kuje ku faÉ—i."
ai ko da gudu suka fara sauka daga matattakalar jirgin suna dariya.
bayan su nabi ina dariya ganin inda suke sauka cap-cap-cap daga matattakalar kamar zasu kefe kasa ina cigaba da faÉ—in.
"Zaku faÉ—i fa kutsaya."
kan kace me sun sauka kasa, sauri na kara ina sauke kafata kan shinfiɗaɗɗiyar kasan kasata abun alfahari na ƙasata Nigeria, naja wani irin numfashi tare da shakar daddaɗan iskar dake kaɗawa acikin ƙasata.
ganin suna kokarin cigaba da gudun nayi hanzari na ruko su tare da faÉ—in
"Idan yaro ya faÉ—i yayi min kuka zan kara masa."
baki suka washe cikin kyakyata dariya Naseem yace
"Mommy baya mu faÉ—i ba." goshin sa na dungure nace "Zaku faÉ—i mana in zaku faÉ—in zaku sani ne wan nan gudun da kuke ai sai dai kuji ku a kasa kuzo nan ku tsaya."
na janyo su gefe guda.

Daga can gefe guda
da sauri aka buÉ—e wata motar da suke jere É—an nesa da mu, wasu mutane biyu suka fito da sauri suka karaso in da muke, sannu da hanya sukayi min, na amsa ina kokarin janyo su Nasmah mu matsa gefe, daya daga cikin su ya mika min waya, kallon wayar da yake mika min É—in nayi kana na mai da duba na kansa,
kai ya É—aya tare da faÉ—in
"Ana maga na." ya fada yana kallon kan screen É—in wayar, a hankali na sake Nasmah dake rike a hannun dama ta na amshi wayar, shikuma yayi saurin ruko hannun ta yaÉ—an matsa gefe kaÉ—an in da É—ayan mutu min ke tsaya ya harÉ—e hannu da bakin gilashi a aidon sa,
a sannu nakai wayar kunne na tare da yin sallama, daga cikin wayar akace
"Barka da isowa kasa Nigeria ki bisu su isa da ke masauki."
É—an shiru nayi kamar naso nagane muryar mai maganar, sai kuma na sauke wayar batare da nace komai ba na mika masa wayar.
a hankali na soma tafiya suna biye da ni har gurin mota, da sauri É—ayan ya buÉ—e min murfin motar muka shiga in da tuni suka saka jakar mu cikin motar.
jere motocin suka fita kamar yan da aka kawo mu airport a can kasar Saudiyya.
muna fita daga cikin airport ɗin muka ɗau hanya, shiru nayi cikin motar ina raba ido cikin ƙasata yayin da zuciya ta ke kunshe da ɗin bin farin cikin gani na cikin ƙasata, ina jin wani farin ciki tabbas ƙasata abun alfahari na ne.
munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katafaren hotel, hotel ne irin wan da manyan kusoshin kasa suke sauka a cikin ta...

Awani haÉ—eÉ—É—en É—aki aka sauke mu sai da suka rako mu har bakin kofar room É—in kafin suka juya, wan da ke rike da jakar mu kuma yashi ga ya ajiye, kana ya miko min waya yace "Ana magana." na amshi wayar a raina nake faÉ—in
"To yanzu kuma ina zai kuma cewa na bisu."
a sannu nakara wayar a kunne na sai jin muryar Bappa nayi yana faÉ—in
"HAMDAH sannun ku da hanya ya gajiyar hanya."
washe baki nayi dajin muryar Bappa da sauri nace
"Laaa Bappa mun iso lafiya kalau Bappa kana ina?."
nafaÉ—a ina washe baki cike da murna jin muryar Bappa da nayi yace
"Kuhuta ku kwanta ku huta sosai ina nan zuwa."
nace "To Bappa." na mika masa wayar ina cigaba da washe baki, mutumin ya fita tare da jamin kofa, numfashi na sauke tare da bin É—akin da kallo, na isa bakin gado na zube bakin gado, in da tuni Naseem da Nasmah suka haye gadon sai salle suke.
kokarin tuɓe kayan jikina nake dan so nake naɗan watsa ruwa, naji ana knocking mayafi na naɗauka na mayar jikina, na mike na nufi kofar na buɗe ma'aikacin hotel ɗin nagani tsaye rike da babban tray, baya naja na bashi hanya yashigo ya dire try ɗin kan table kana yafita na mai da kofar narufe na murza key.
na dawo bakin gadon na tuɓe kayana nashige bayi,
wanka nayi sosai nafito na tuɓe su Naseem suma nayi musu wan kan.
bayan na shirya su nima na sauya kaya, kana na zuba mana abinci mukaci.
muna gama ci muka koma gado...
Chapter 8 · 0% Book details