← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 34

Sashe 3

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kame kame Æ´arrakiyar tashiga faÉ—in
"Um..um mijin..ta..mijin ta."
sai kuma tayi shiru. duban mai labour É—in yayi da kyau yace
"Kirawo mijin ki yanzu yazo kice masa bazamu karɓe kiba har sai yazo."
kasa tayi da kanta batare da tace komai ba sai hawayen da ke cigaba da sauka a idon ta,
girgiza kai yayi kana yace
"Ba miji kenan wannan ciki ba uba baya da uba ko?".
da sauri ƴar rakiyar ta gyaɗa kai tana tsilli-tsilli da ido kamar an tare ɓera kana cikin in-ina tace
"Wlhy likita tsautsayi aka samu bata da miji, kuma yanzu iyayen ta sun kore ta da sukaga tana labour sun ce tafita musu a gida taje can ta haihu ba a gidan suba,
shine tazo gidan mu nikuma naga kamar zata mutu shine na rakota asibiti, dan Allah likita ka taimaka mata."
gaba É—aya suka zuba musu ido. wani murmushi Raliya ta sake.
ido Na'ima ta bita da shi dan tasan ma'nar murmushin nan nata tace
"Aminiya sabon shiga harka ko?". baki Raliya ta taɓe tare da faɗin
"Oh yaro man kaza har yaushe zakayi sake irin haka ta kasance, ka É—aukar wa kanka wahala shi ba mai uba ba wahalarka a banza, uban titi da bazai kalleka cikin halin labour yace ma sannu ba, tuni ban wanke shi na zubar ba in ma yasami shiga kenan mttss".
taja wani dogon tsaki tare da faÉ—in
"Kara mar Æ´ar iska bata san yan da zatayi iskancin bama."
Dr Mukhtar da Na'ima kasan cewar suna kusa ne suna juyo duk abun da take fata akasin su da suke tsaye a sakiyar office É—in.
Dr Mukhtar yayi murmushi tare da faÉ—in
"Ko zaki sata a hanya ne idan ta sauke kayan dake jikin ta".
harara ta dalla masa tare da kuma jan wani gajeren tsaki.
Dr Mukhtar ya mai da duban sa kan yaran sannan yace
"To a gaskiya bazamu karɓi haihuwar ba, na ɗaya babu kuɗin karɓar haihuwa sannan babu wani babba a tare da ku, bazamu karmi haihuwar ba saboda gudun matsala, bugu da kari kuma ɗan bashi da uba,
muzo mu karɓi haihuwa wani abu ya faru azo a dakatar min da asibiti gaskiya yanzu na daina irin wannan kasadar gaskiya kuje kawai kuje wani asibitin."

Da sauri Na'ima da Raliya suka juyo a tare tare da yiwa junan su
kallon-kallo, sai kuma da sauri Na'ima ta juyo gun Dr tace
"Dr a taima musu a karɓi haihuwar ni zan biya kuɗin duk wani ɗawai niyar da za'ayi ni zan biya, zan kuma tsaya wajen ganin ba'a sami wata matsala ba, aje a kaita labour room."
kai Dr Mukhtar ya jinjina kana yace
"Okay." yadubi nurse É—in yace
"Akai ta labour room.
tace "Okay sir." tajuya da sauri tana faÉ—in "Kubiyo ni."
suka fita dukan su mai labour'n da kawar tata.
suna fita da sauri Raliya ta dubi Na'ima zatayi magana Na'ima tayi saurin soma yiwa Dr mukhtar magana.
"Dr irin su ne idan suka haihu suke kashe É—an, har idan akabar ta ta tafi bazataje wani asibitin ba wani gun zataje ta haihu ta kashe É—an, ko kuma ta jefar da shi to ni ina son abun da zata hai fa har idan na miji ne."

Dr mukhtar yayi wani dariya tare da faÉ—in
"Ai tun É—azu na fahimci hakan ai tun da naga kuna wannan kallon-kallon Na'ima Raliya bakuda kyau sai an haÉ—a da wanka, ai na san hali tun a makaranta har idan kukayi wannan kallon-kallon to wata tsiyar za'a kulla."
dariya suka sheke da shi suka tafa kana shima ya miko hannu suka tafa da shi dukan su.
zaman sa zagyar da kyau sannan yace
"To meye kaso na a ciki?."
Na'ima tace "Kana da kaso mai tsoka yanzu dai kaje ka bata kulawa ta haihu kuma kayi fatan namiji zata haifa, yau nima zan haihu."
yace "kwarai kuwa har an shiga dake labour room".
dariya suka saka dukan su.
Nan sukayi ta wasu magan ganun su sakanin su batare da ni naji ko fahimtar me suke nufi ba..

Bayan awa uku, kukan jariri ne ya soma tashi daga cikin labour room, Na'ima da Raliya da har yanzu suna zaune a office É—in Dr Mukhtar suka wani saki murmushi, lokacin da sakon Dr Mukhtar yashigo wayar Raliya wato tex message yana sanar musu da abun da aka haifa,
ciki murmushin mai kunshe da ma'anoni da dama Raliya tace
"Kai sannu Na'ima kin sauka lafiya kai gaskiya haihuwa akwai wuya kinsha fama yau."
itama wani dariya ta sake cikin kware wa a zunzurutun makirci da hatsabiban ci tace
"Na haihu yau ni Na'ima gaskiya haihuwa a kwai wuya".
darika suka kuma shekewa sukatafa.
Dr Mukhtar da yanzu shigowar sa office É—in bayan ya amshi haihuwar, zama yayi kan kujerar sa yana faÉ—in
"Gaskiya yau ba sauki oga SALEEM ya haihu um wayaga oga SALEEM da É—a abun ba sauki hhhhh".
"Shima yazama baba ni kuma mama".
Na'ima ta faÉ—a tana wani faÉ—i.
nurse ce tayi knocking tashigo taÉ—an dukar da kai tana faÉ—in
"Sir an gama kimsa komai sai dai har yanzu tana bledin, munyi iya kokarin mu bai tsaya ba ko zaka zo ka duba ta."
kai ya girgiza kana nurse É—in ta fita da sauri,
a tare Na'ima da Raliya suka mike ganin Dr shima ya mike sukabi bayan sa.
dukan su suka shiga É—akin da aka tanada domin haihuwa.
nan da nan yasoma baiwa yarin yar taimakon gaggawa ganin yan da jini ke fita a jikin ta,
batare da ɓata lokaci ba tadawo cikin hayyacin ta ,jinin kuma ya tsaya.
jaririn da nurse's suka gyara shi suka kunshi cikin É—ankwalin mahaifiyar sa sai musu-musu da kuka yake ga dukkan alama niman abinci yake,
nurse ta É—ago shi ta maso gaban gadon da mamarsa take, wan da a Æ´an min tunan da ta sami kanta bayan Dr yabata taimakon da ya kamata har ta iya mikewa tazaune.
tamika mata shi tana faÉ—in
"Ga abun da kika haifa nan kuma da alama niman abinci yake gashi bakuzo da flas ba, bare a bashi ruwan zafi ya sha."
kin karbar sa tayi sai kukan da ta fashe da shi.
kawar ta da suka zo tare ita ta karɓi ɗan tashiga jijjiga shi, wayar ta dake cikin aljuhun wandon makarantar jikin ta yasoma kara alamar shigowar kira,da sauri takai hannunta guda ta cusa cikin aljuhun wan donta,
É—aya hannun kuma ta gyara rukon jaririn da kyau ta zaro wayar.
ido ta waro kan screen É—in wayar murya cike da tsoro tace
"Mama." sai kuma da sauri taÉ—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da yin sallama.
É—an shiru tayi sai kuma tace
"Mama gani nan dawowa an tashi ne bansami abun hawa ba shine yasa na tsaya".
tana sauke wayar da sauri tadubi kawar tata tace
"Mama ce takira ni taga lokacin tashi yayi har yanzu ban koma gidaba, bayan ko makarantar ma banje ba,ni sai yanzu ma na ga agogo tun É—azu lokacin tashi yayi, tofa zantafi gida yanzu yaya zamuyi ina tsoro kada Baba yadawo yasamu ban dawo ba,
kema zaki tafi gida ba kawai tun da yanzu kin haihu? muje na rakaki gidan ku nima sai na wuce gida,
karfa Mama tasa yayu na su biyo ni kin san fa in nakai wannan lokacin sawa take aje a nimo ni".
tana maganar ne cikin tsaro sosai.
itako mai jego kuka kawai take takasa cewa komai.

Dr yace "A'a taya za'ayi ta tafi yanzu bayan yanzu ta dawo hayyacin ta,sai mun daÉ—a ganin yanayin jikin nata kafin mu sallame ta, yanzu kam ma allurar da akai mata zai fara ai ki in tayi bacci ta farka mukaga yanayin karfin jikin ta sai mu sallame ta, yanzu dai ke kije tun da ke a na kiran ki."
to tace da sauri ta mika mata É—an,
yanzu ma kin karɓar ɗan tayi.
Raliya ce ta karɓi ɗan a hannunta tace
"To kije kawai."
ai ko tafita da sauri.
bayan fitar ta Dr Mukhtar ya dubi yarinyar yace
ta kwanta ta sami bacci, a hankali ta gyara kwanciyar ta,su kuma suka fita suka koma, office É—in sa.
suna zama Na'ima tace
"Bani É—an na ganshi."
Raliya ta mika mata kyakkyawa fari kuwa da shi, sai dai yaron bashida girma É—an kankani ne hakan kuwa bazai rasa nasaba da rashin samun kulawa da ya kamata tun aciki ba.
takafe shi da ido tana wani irin murmushi tana É—an jijjiga yaron.

after 4 hr.
hakan kuwa yayi dai-dai da farkawar yarinyar da ta haihun a bacci, alhmdllh taji karfin jikin ta kwarai.
nan tanimi tafiya gida nurse tazo ta sanar wa Dr yace taje ta kira ta.
tare nurse É—in suka shigo da yarin yar,ya nuna mata kujera ta zauna kana yacewa nurse É—in taÉ—an basu guri, nan ta fita tajawo musu kofa.
duban yarinyar yayi kana ya ce
"Inane gidan ku".
cikin kame-kame tashiga faÉ—in
"Um..um..gidan mu gidan mu."
sai kuma tayi shiru.
da kyau yakuma duban ta sannan ya ce
"Bana son wani ɓoye-ɓoye nasan wannan ɗan bashi da uba cikin shege ne dan haka kawai tan bayar ki nake ki bani amsa inane gidan ku?."
kwalla ta matse tare da mutsutstsike yatsun ta kana ta soma magana,
"Gidan mu yana..yana Unguwar Bakaro".
kai ya jinjina yace
"A Bakaro kike?."
ta gyaÉ—a kai, Raliya ta jinjina kai kana ta ce
"Ah to shikuma uban É—an a ina yake shima a Bakaron yake?".
tace Eh.
"To yan zun ina zakije keda É—an idan kika fita daga nan?".
Raliya tayi mata tambayar tana dubam ta, shiru tayi tare da musutssuke yatsun hannunta.
Dr Mukhtar yaÉ—an tsura mata ido kana yace
"Yanzu ina zaki kai É—an idan aka baki shi?."
kuka tafashe da shi tana faÉ—in
"Wlh idan na tafi da shi gida yan kani za'ayi wlh iyayena sun ce sai sun yanka ni yanzu ma in na koma gida nasan suka na za'ayi idan na tafi da shi zasu yanka ni".
Chapter 3 · 0% Book details