← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 34

Sashe 16

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka ne yaci karfi na nakifa kaina da guiwa na nayi ta kuka kamar raina zai fita.
najima sosai zaune a gurin ina ai kin kuka, mai cike da kuna da bakin ciki. da kanshi hawayen ya tsaya badun na tsai da shi ba, sai dai kukan zuci danake, a hankali na mike cikin matsananciyar ciwon kai wan da dakyar nake iya buÉ—e idona duka sabo da zafin ciwon kan, na nufi ciki.
direct bedroom na shige kana shiga bathroom wanka nayi nafito na sauya kaya na zo na kwanta bakin gado,
karatun Alkur'ani na kunna cikin wayata a hankali nake bin karatun, a sannu narika jin zuciya ta tana samin salama da nutsuwa, a hankali narika jin bacci na fizgata ta, na lumshe idanuna.
can cikin baccin da ya É—auke ni da nisan ta baifi na minti 20 ba.
najiyo muryar su Nasmah, da gudu suka haye gadon suna faÉ—in
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
ida nuna na rumtse da É—an karfi dan har lokacin kai na bai bar yimin ciwo ba,
mike wa zaune nayi jin sun zube a jikina na É—ago su ina faÉ—in
"Wai har kun dawo? amma dai ba'a tashi ba ko."
nayi maganar ina duban agogo, karfe 12 har da rabi,nayi mamakin gani in da lokaci yatafi har haka, ranar yau karfe 12 saura suke dawowa har sun dawo anyi musu wanka an sauya musu kaya.
lallai najima ina kuka har ban san lokaci yatafi har haka ba, tausayin kaina ya kamani, É—an guntun kwallar da ke kokarin sauka a idona É—aya nayi saurin kai yatsata na tare shi kana na gyara zama ta ina faÉ—in
"Ashe dai lokacin tashin naku yayi, to yaya karatu yau ansha wasa ko."
nayi maganar ina shafa kansu.
baki Nasmah ta washe ta mike tsaye a kangadon tace
"Mommy yau Aunty'n mu tayi mana haka."
tarike kugu tare da girgizawa, dariya nayi ina faÉ—in
"Au kice yau Aunty rawa tayi muku."
"Ba haka bane haka ne".
Naseem yafaÉ—a tare da mike wa yarike kugu yasoma tsalle.
ido na ware nace "Kai kuce yau kunsha rawa." cikin tsallen yace "Eh ai hadda chocolate ma."
tsai da tsallen da yake yayi sai kuma ya dira a godon da gudu yafita sai gashi ya dawo da School bag É—in sa, a tsakiyar gadon ya zazzage School bag É—in sai ga Chocolate masu yawa haÉ—e da littattafan sa sun zubo,
da mamaki nace
"Yau kuma Talatu kayan zaki tacika muku a jakar."
nakai hannu na É—ibo chocolate dasuka kai guda biyar kala daban daban, ga kuma wasu a gaban sa, da É—an mamaki nake kallon su dan asanina babu kalar waÉ—annan chocolate É—in acikin kayan cime-cimen su kalar nasu ba irin wannan bane.
"Kai Naseem a ina ka samo waÉ—an nan chocolate É—in?."
nayi maganar ina duban sa, da sauri Nasmah tace
"Nima akwai nawa." ta dira agadon da gudu tayi waje, Naseem ko bai bani amsa ba sai kokawar buÉ—e laidar chocolate É—in yake.
ta shigo da school bag É—in ta itama ta zazzage, nace
"Kai wai waya baku wannan abun haka, Talatu Talatu."
nashiga kwaÉ—awa Talatu kira dan na fara tunanin ko rikici sukayi mata gun shirya su tabuÉ—e wani katon É—in chocolate É—in daban.
Naseem da yakai Chocolate É—in baki ya kutsura yana É—aga kafaÉ—a alamun yana jin daÉ—in abun yace
"Daddy yace mucinye wannan duka dai kaya mana wani."
"Ai yace idan ka kaiɓa min baye kaya maka ba ni de bani da yawa."
cewar Nasmah tana kai wan da ta ɓare baki.

Ido da baki na waro da mamaki tuno wan da suka taɓa kiran sa da Daddy a makarantar su nace "Wani Daddy mutumin nan ko?, a ina kuka san shi dan gidan ku da har zaku rika ce masa wani Daddy."
Naseem daya cika chocolate a bakin sa yace
"Ai Daddy yace kuma dai jo ya auke mu ya kai mu can guyin kifi babba."
cikin tsawa nace "Bana ce muku kada wani yasake baku abu ku karɓa ba? ashe bakuji ba so kuke nazane ku ko?, bana ce muku nice Daddyn ku nice Mommy'n ku ba, shi ba Daddy'n ku bane, baku san shiba shima bai sanku ba, bakuda Daddy nice Daddy'n ku, kuna jina dai ko?."
nariko kunnuwan su ina jijjigawa a hankali, suka gyaÉ—a kai.
shiru nayi tare da komawa na jingina bayana da jikin gado jiki a sanyaye nashiga maganar zuci
"Kuhi hakuri Æ´aÆ´ana ni zan cigaba da zame muku uwa kuma uba a duniyar na."
jin kwalla nakokarin zubomin nayi saurin dakatar dashi...

A ranar nasa aka kawo musu chocolate dawsu kayan makulashe aka kara kan wan da yake gida.
washegari ranar asabar bamu wuni a gida ba yawon guraren shakatawa muka tafi, ni Faty Naseem Nasmah da kuma Talatu, sai direba. sai yamma muka dawo niki niki da kayan makulashe, washegari ranar Lahadi ma muka kuma fita, shima sai yamman muka dawo a part ɗin su Inna wuro muka yada zango sai bayan isha muko koma side ɗin mu, ai ko muna shiga su Nasmah suka ɓingire da bacci.
koda gari ya waye dakyar nata da su Talatu ta tafi da su dan yimusu wan ka da shirin makaranta, dan tare jiya muka kwana da su.
kamar kullum na rakosu muna É—agawa juna hannu suka fita.
ina komawa ciki wanka nayi nashirya cikin les copie colour da É—an ratsin gold ajiki,
da misalin karfe 10 da rabi nasauko kasa da mayafi akai na sai Æ´ar karamar jaka mai É—auke da wayoyina da wasu Æ´an kuÉ—i dana saka ciki,
dinning area na nufa, in da na tadda Zulai tagama shirya komai na breakfast, a É—an gaggauce nayi breakfast É—in, ina yi ina duba agogo, dan fita zamuyi da Bappa zuwa asibitin da ake ginawa dasunan Inna ganin yan da ai kin ke tafiya, ina saurin ne dan jiya nace mishi karfi goma da rabi zamu tafi nasan kuma yanzu haka yagama shiri ni yake jira.
koda na fita a kofar masallaci dake ta nan cikin gida na taddashi zaune, na karaso in da yake tare da gaida shi, daga nan muka shige mota muka nufi asibitin.
masha Allah asibiti yayi kyau saura kaÉ—an a kammala aiki, bamu bar asibitin ba sai wajen karfe 12:20pm nacewa Yakubu muwuce makarantar su Nasmah mu É—auko su.

Abakin get É—in makarantar Yakubu ya faka mota yafita da sauri yana faÉ—in
"Bari naje na fito da su". yayi cikin makarantar da sauri, muna nan zaune can yafito da sauri kamar zai kife kasa yakaraso gefen da nake yace
"Hajiya wai an zo an É—auke su."
ido na waro da mamaki nace "Wa yazo ya É—au kesun bayan kai muna tare da kai ina ce kai ne me zuwa É—aukar su."
Bappa yace "Zancen banza kai wani direban akayi musu sabo ne da zaizo É—aukar su? ko dai bakaji abun da suka faÉ—a da kyau bane?."
yace "Wlh haka mai gadin yafaÉ—a Bappa."
da sauri Bappa ta buÉ—e motar yafita ai ko nima da sauri nafita narufa masa baya har ina haÉ—awa da sassarfa.
babu kowa cikin makarantar sai mai gadi da masu kula da tsaftar makarantar sai shara da goge-goge suke, hankali tashe Bappa ke tambayar mai gadi, mai gadin yace
"Ai ko minti goma basu da tafiya ba duk É—azu muna tare da su anan da wasu É—aliban mota tazo tafaka nan bakin get suna ganin motar suka zuba a guje zuwa gurin motar suna murna, da naso hanasu dan ganin ba É—aya daga cikin irin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane, to ganin yan da suke ta murna sukayi gun motar a guje yasa nayi tunanin É—aukar su a kazo, dama badaga gida akazo É—aukar su ba!."
maigadi yakarashe maganar yana buga kirji.
Yakubu da gumi yafara keto mishi kamar zai fashe da kuka yace
"Ina ni ke zuwa É—aukar su kuma gani a gaban ka sai kuma hajiya wata rana,ko mutumin yasako irin fuskata ce ya zo."

Bappa yace "Amma kuwa abun da mamaki amma ya kamata lokacin da kaga ba É—aya daga cikin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane yazo kama yayi kaje kaga ko waye ne,amma wani abun mamakin da kace wai sun je gurin motar da gudu kuma suna murna to ko wani ne daga gida yazo É—aukar su tun da sun san mun fita har da direba?."
ni dai kasa magana nayi sai ɓari da jikina yake cikin matukar tashin hankali tuni idanuna suka kawo ruwa kan kace me hawayen suka fara sauka.
murya na rawa Yakubu yashiga tafa hannu da salati yana faÉ—in
"Dama ance yanzu masu garkuwa da mutane sun canza salo akwai wani abun da suke yi sai dai kaga mutum na ta binsu kamar ya sansu harsu tafi da shi, wayyo Allah Naseem da Nasmah ko dai sune."
cikin gwalalo ido mai gadi yace
"Wayyo Allah nashiga uku wayyo ai kina shikenan dama ance idan aka sami matsala to abakin ai kina, ashe dama tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi kenan? shi yasa yarannan sukayi ta tsalle kamar doki suka ruga in da motar take, ashe jansu ake taciki kamar kuran karfe."
ɓarin jikina ne yakaru yayin da zuciya ta ke bugawa da karfi gudun hawaye na yakaru.
Bappa yace "Kai ya isa haka Falyakum khairan au yasmuq, in sha allahu babu abun da zai faruku muje gidan mugani wata kila daga gida ne akazo aka É—auke su tun da sunsan bama gidan."
yadube ni yana cigaba da faÉ—in
"Kice Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un."
kalmar nashiga nanatawa kana muka juya gun mota, muka bar maigadin nan tsaye yana ta rafka salati dafaÉ—in shikam yau yasan ai kin sa yazo karshe har in sace yaran akayi.
acikin mota Bappa yarika zuba addu'o'i yakuma hanani kukan danake shirin yi yace nayi ta faÉ—in
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
a haka muka isa gida.
Chapter 16 · 0% Book details