Sashe 18
Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai gadi yashiga jan hanci yanaci gaba da faɗin "Sam babu wan yafita ai da nasani dana shiga ciki naje na karɓi makullin mota naje na ɗauko su ai, na ɗan iya mota ba sosai ba amma da wasu su ɗauke su gara ni naje a haka na ɗauko sun, wasu matsiya tane masu niman jaraba suka ɗauke su, duk tai makon da akewa mutane baiyi musuba har sai sun haɗa da sata, wayyo Allah Naseem wayyo Nasmah, ashe da rabon ragowar shayi da nama gobe bazan shaba, kullum sai sun kawo min na haɗa da nawa duk na kallame." zuwa yanzu tashin hankalin Bappa yafara bayyana yashiga faɗin "Kanu innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ahjirni fi musibati²." bakina na toshe da tafin hannuna jin kuka mai sauti yana son suɓuce min najuya ina kokarin barin gurin Bappa yakira sunana najuyo ina hawaye yace "Je ki zauna kada ki ɗaga hankali sosai na tabbata zasu kira kuma bazasu cutar da su ba dan kuɗi suke bukata za'a kuma basu babu komai." kai kawai na gwaɗa najuya nasoma tafiya, maigadi yabiyo ni yana cigaba da jan hanci yace "Anyi bako Hajiya." ban iya juyowa ba bare nabashi amsa Bappa ne yace "Ina bakon?." yace "Gashi can a mota yana shigowa kuma kuka shigo," "Wanene?." cewar Bappa, yace "Gashi can cikin mota ai da naso hanashi shiga ganin baiyi kama da irin waɗan da za'a dakatar ba shine na barshi ya shigo." yayi maganar yana nuna wata mota dake fake gefe a farfajiyar gidan. Bappa ya girgiza kai kana ya soma tafiya yana faɗin. "Ana cikin wani hali ta ya za'ayi a saurari wani bako." Cikin matukar da muwa da tashin hankali nake tafiya, "Me zaisa su ɗauke su in dai kuɗi ne akan su ɗauke su ni da sun faɗa min ko nawa ne zan basu, me yasa suka zaɓi su cutar da yaran da basujiba basu gani ba. wlh Allah sai yabi musu kadin su tun suna ciki ake cutar dasu da zaluntar su, har suka fito duniya." wasu zafafan kwalla ne suka rika wanke min fuska bana ko iya ganin gabana, tunani na ɗaya awani hali suke yanzu.. Bappa har ya wuce motar da mai gadi yace masa bako ne ciki, sai kuma ya dawo sanin da yayi kan cewa bako rahama ne, gilashin motar ya kwankwasa, a hankali aka zuge glass ɗin. cikin matukar mamaki Bappa ke lallon mutumin da waɗan da ke tare da shi, yana zaune a mazaunin direba waya na rike a hannunsa yana ta faman latsawa, Nasmah na zaune a gefen sa tasaka kanta jikin kafaɗar sa tana ta cin chocolate, Naseem kuwa na zaune a gefen mai zaman banza rike da waya a hannunsa yana buga game yana kuma taunar chocolate. cikin tsananin matukar mamaki Bappa ke cigaba da kallon mutumin da mamakin ganin sa tare da su Naseem, tabbas bazai taɓa mance wannan fuskar ba, mutumin daya samar musu da ingantaccen ilimi a rugar su,mutumin da ya yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin an cafke ƴan ta'addan da suke shiga rugar su suna kaɗa musu shanukai su kashe musu makiyaya. cikin girmamawa mutumin yashiga gai da Bappa, Bappa ya amsa fuska ɗauke da annuri yana yi masa kallon sani, shiko mutumin ga duk kan alamu bai gane shiba, cike da al'ajabin ganin su tare da su Nasmah Bappa yace, "Ikon Allah kai ne nan tare da su Naseem da muke zaton ko ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke su." da sauri Bappa ya juya yana faɗin "HAMDAH taho gasu nan." cak naja na tsaya dai-dai lokacin dana ke kokarin ɗaura hannuna jikin kofar side ɗina, najuyo da sauri, magana Bappa yaci gaba dayi yana nuna cikin motar. "Gasu nan cikin mota Allah yayi ikon sa." dagudu na nufo gun motar ina share hawaye na da bakin mayafi na, ina isa gun motar nawuce gaban Bappa da sauri batare da duban cikin motar ba duk da glass ɗin motar a sauke take, hankali na nakan murfin motar dana saka hannu ina kokarin buɗe motar sai jin ta nayi a rufe, da sauri na ɗago karaf idanun mu ya haɗu da juna, da mamaki nake kallon sa sai kuma nan take naji raina ya ɓaci, mutumin da yace wai arika turo mai wayo yarika ɗaukar su Naseem a school ba ni ba, wan da kuma suke kiran sa da Daddy yayi ta tara musu chocolate kamar sun zama shazumame sar kin shan zaki. fuska na ɗaure tamau ina duban su Nasmah nace "Ku sauko nan!." nayi maganar cikin tsawa da zare idanuna. Bappa yaɗan matso yana faɗin "Wlh mun shiga tashin hankali sosai da akace wani mota daban yazo ya ɗauke su ba ɗaya daga cikin motocin gidan nan ba, mungama zaton masu garkuwa da mutane ne, suka ɗau ke su." kai ya jinjina tare da yin murmushi wan da yayi sana diyyar bayyanar kyakkyawar dimple ɗin fuskar sa, batare da yayi magana ba ya kai hannu ya buɗe marfin motar, baya na ɗan ja kaɗan ya buɗo marfin, ya zuro kafafun sa waje, Nasmah dake gefen sa yaɗago ta cak yafito da ita ya aje ta kasa, kana asannu yafito daga cikin motar,tsayuwar sa ya gyara kana yaɗan sunkuya jikin kofar yamika hannu cikin motar Naseem ya rike hannun nasa yaɗago shi cak yafito da shi, sai da ya ajiye Naseem kasa kana ya ɗago da murmushi yace. "Idan za'a cigaba da barin su har kowa ya watse a makaranta ba'a je ana ɗaukar su kan lokaci ba to kuwa zasu iya fuskantar hakan,domin su masu garkuwa da mutanen babu ta in da basa nan." kai Bappa ya jinjina cike da gamsuwa da maganar sa kana yace "Tabbas kuwa, Allah yashiga sakanin nagari da mugu." a kufule nace "Babu ranar da ba'a zuwa ɗaukar su kan lokaci in ban da ranar da nayi ta kiran Yakubu bai ɗaga ba, sai kuma yau, yau ɗin ma ai bawani makara akayi ba tun da karfe 12:50pm muka isa makarantar kuma karfi 12 da rabi ake tashin su, kuma tun kan ɗalibai su watse mai gadi yace aka ɗauke su, to ashe dai ba'a makara zuwa ɗaukar su, ana zuwa ɗaukar su tun shabiyu ajira su har sai an tashe su a ɗauko su a dawo da su, babu wani ɓata lokaci a zuwa ɗaukar su, kai kuwuce mushiga ciki!." nayi maganar cikin haɗa haushi biyu zuwa uku, akan me zaice ba'a zuwa ɗaukar su kan lokaci. sannan kuma wace dalilin ne yasashi zuwa ɗaukarsu ina ruwan shi dasu dakuma rayuwar su, yasa nayi kuka da tunanin ansace su ne. sannan ganin yan da yaran suka manne masa sai kiran sa da sunan dana hanasu suke. tun da nafara maganar idanunsa akaina yayin da yake shafa sajen fuskar sa, kafaɗa yaɗaga kana yace "Kinyi kokari, kiyi wayon sanin hakan tukun dan da kaɗan kikafi yaran wayo." ido na waro amma lallai mutumin nan yana da rainin wayo karo na biyu kenan da yake cemin wai bani da wayo, yaran dana haifa yake cewa wai dakaɗan nafisu wayo. wani kallo na watsa masa tare da murguɗa baki nace "Allah yasa wayon suka fini, mece ce matsalar ka?." nayi maganar tare da kuma murguɗe baki. Bappa yace "Um to hakane kam amma ana zuwa ɗaukar su akan lokaci sai dai ɓacin rana, amma akiyayen shiyafi, mun gode sosai, in sha Allahu za'a kara azama wajen zuwa ɗaukar su." hannunsu na fizgo ina faɗin "Kuzo ku wuce ina magana kuna tsaye." najanyo su fuuu muka nufi ciki anan na barsu shi da Bappa, cikin haushin jin Bappa yana saurarar sa, har shi zai gwada wa mutane yan da zasuyi da rayuwar su, ina ruwanshi, irin mutane masu shegen shishshigi kan abun da bai shafe su ba. sai da muka shiga parlour kafin na sake hannun su, na zauna kan kujera, ina duban su sukam ma ko a jikin su sai wata tsafgar su suke. kunnuwan ko wannen su na rike naɗan murɗa da karfi, suka haɗa baki wajen cewa "Wayyo Mommy." nace "Sai na sinke kunnen har idan baku dai na abun da na hana kuba, wato duk hanaku da nake tayi bakuji ba ko shine yau abun naku yagirma har da binsa, kunsan shi ne? baku san mutum ba kukama binsa har da shiga motar sa, ina kuna so a yanka kanku ne?." kai suka girgiza da sauri tare da faɗin "A'a-a'a Mommy." nace "To ban hanaku ce masa Daddy ba bana ce muku ku bakuda Daddy nice Mommyn ku nice Daddyn ku ba?, ban ce kada wani ya sake baku abu ku karɓa kuci ba?, shine har yau zaku bishi kushiga motar sa, kunsan shine?, to sai nayi muku duka yau sai na kaiku wa ɗawisu ta caccake ku bari ku gani." namike tsaye tare da ruko hannun su ina cigaba da faɗin "Ɗawisu kawai zan kai ku wasu sune zasu yin maganin ku." kuka suka sake da karfi suna faɗin "Wayyo Mommy kai ki kai mu." "Ai bazaku bari ba sai na kai ku gurin su su hana ku da kansu." nayi maganar ina jansu. ihu sosai suke suna faɗin "Mommy mun bayi." komawa nayi na zauna kan kujera ganin sun tsorata sosai najasu jikina na rungume su, ina faɗin "To kuyi shiru nafasa kai ku amma idan kuka kara sai na kaiku, zaku kara ko?". kai suka girgiza da sauri nace "Kada ku sake zuwa gurin wan da baku sanshi ba bare har kushigs motar sa, kuma kada ku sake ce masa Daddy shi ba Daddyn ku bane nice nan Daddyn ku kunje jo?." kai suka kuma gyaɗa wa suna jan shashsheka. a hankali narika shafa kansu cikin tsananin tausayin su, wasu zazzafan kwalla ne suka ciko ido na, ban dakatar da su ba har sai da suka gangaro kan fuskata ta, nakai tafin hannuna na goge, yayin da nake daɗa mannna kan su a kirjina, ina jin tausayin su na daɗa shiga na. maganar zuci nafara yi yayin da zazzafar hawaye mai cike da ɗin bin kuna ke cigaba da zuba a ido na. "Kuyi hakuri bana so ku sanya wa ranku abun da babu shi a rayuwar ku, nafiso ku tashi da sanin cewa bakuda shi ni zan zame muku garkuwa uwa uba." daɗa rungume