← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a gefe in da aka tanada dan ajiye motoci suka faka suka fito suka nufi cikin sibitin.
kofar wani office direct suka nufa tare da yin knocking,
daga cikin office É—in aka basu izinin shigo wa.
wanda ke cikin office É—in yana zaune cikin shigar likitoci yana ganin su ya washe baki tare da faÉ—in.
"A'a manyan kasa kune tafe?".
cikin fari da ido Raliya taja kujerar da ke fuskantar sa ta zauna tana faÉ—in.
"Kanana dai ai kune manyan kuna zaune AC na ratsa ku kuÉ—i na shiga yadda yakamata me yamuku saura?".
Na'ima ma kujerar taja tazauna kana suka shiga gaisawa,
suna ɗan taɓa hira da dariya sakanin su da kagan su kasan tabbas sunyiwa juna farin sani.
Dr Mukhtar Lawan abokin su Na'ima ne sosai abota ne na tun a makaranta duk kanin su gar tasan garne, duk wani iskanci da sheke ayar da sukayi lokacin suna makaran ta tare sukeyi, har kuma yanzu wani kullin tare suke tufke shi. acikin su shine kaÉ—ai yaÉ—an maida hankali kan karatu har yake cin moriyar karatun da yanzu yake a matakin Dr, asibitin mallakin sa ne wan da mahaifinsa yagina masa bayan zamowar sa Dr.
duk hirar da suke Dr Mukhtar idanunsa a kan Raliya,yakafe kirjin ta da ido wan da É—inkin rigar jikin ta ya bayyanar da nonuwan ta kusan rabi a waje.
fiki-fiki yayi da ido cikin yanayin shiga tarkon Raliya yadubi Na'ima kana yace
"Na'ima kawarki Raliya takini fa taki na ganta kwata-kwata yanzu ko waya na kirata muÉ—an haÉ—u taki ta bani da ma mu haÉ—u, sabo da tasami manya wan da suka fimu bata hurÉ—a da mu".
yakarashe maganar da mai da idanunsa kan Raliya wacce tadaÉ—a bankaro kirji tana wani fari da ido.
dariya Na'ima tayi tace
"Kai haba aminiya ai ko ba komai dai zakizo wannan haÉ—aÉ—É—en office É—in kiÉ—an rika É—ebe maba kewa."
fuska Raliya ta yamutsa cikin salon kwarewa a harkar bariki takuma bankaro kirji yayin da yatsarta guda ke saman wuyan ta tana É—an yawo da shi har zuwa kirjin ta, ta saman nonuwan ta,ido ta kanne a kansa kana tace.
"Dr kenan ku abun naku ai sai a hankali in ka shirya yanzu Na'ima ta wuce ta bamu guri amma yanzu zaka ajiye min rabin miliyan anan shima É—in dai-dai azo sallama ne".
tanuna saman table É—in gaban sa.
ido ya waro da karfi ya furta
"500k ai ko ai kina na wata guda bai kai rabin miliyon ba".
dariya duka suka saka.
Dr Mukhtar yace
"Ina kinji ko Na'ima kawar ki tafi karfi na sai dai mugani kawai mu latse baki, ko za'a É—an taimaka min naÉ—an lallasa ne basai ciki ba iya waje kawai". yakarasher maganar da dariya haÉ—e da tsigar zolaya.
baki Raliya ta taɓe tana faɗin
"Yanzu dai muyi abun da yakawo mu, Dr muna da damuwa fa".
Na'ima ta karɓi zancen da faɗin
"Kwarai kuwa Dr akwai matsala".
yace "Wani damuwa kuma ai ni a tunani na yanzu bakuda wata sauran ragowar damuwa ke Na'ima da kike da SALEEM a hannun ki".
"A'a Dr gaskiya da saura nasame shi kam amma da saura munaso mukuma samin shi sosai yazamo nawan da gasken gaske".
zaman ta ta gyara da kyau ta daÉ—a fuskantar shi kana tace
"Dr yau nazo haihuwa".
ido yawaro yace
"Haihuwa kuma antaɓa haihuwar da ba ciki?". yafa da dariya
sai kuma yakuma sakin dariyar shakiyyanci
yace "To ai cikin naki baikai na haihuwa ba tukun".
wani goron numfashi ta sauke kana ta daÉ—a gyara zaman ta da kyau tace "Dr tunani na kenan ranar da cikin nan zaikai na haihuwa, ace ciki yayi wata tara yaya zanyi narasa yanda zanyi,
rabon da naji wani abu yasani shiga damuwa irin haka na mance, Dr taya zanyi nasami É—a kune manya aikin kune kunfimu sanin yadda za'ayi".
jakar hannunta ta aje gefe kana taÉ—aura hannayenta biyu kan teburin gaban su sannan tacigaba da faÉ—in.
"Ko nawa ne zan biya har idan nima bukatata zata biya".

ÆŠan shiru yayi yayin da yake É—an juyawa kan kujerar da yake kai, sannan yasauke numfashi kana yace
"Gaskiya wannan buka taki babbace a gaskiya yanzu samin É—a a cikin asibitin nan da kamar wuya, yanzu an saka matakan tsaro iri-iri, kinsan kwanaki fa munyi ta shari'a da wasu mutane wan da mukayi musu canjen É—a,munyi ta samin matsala dan ma allah ya rufa asiri,
amma mezai hana tun da kince kinason É—an cikin gaggawa kije gidan marayu, gidan marayu yakamata kije, akwai wan da suka haifi Æ´aÆ´a zaki iya samin wan da yau ma ta haifa ta yar aka samu aka kai shi gidan marayun,
to inaga kije ki É—auka a can É—in zaifi".
kai Raliya ta jinjina alamun gamsuwa da shawarin nasa tace
"Eh gaskiya hakan ma kawai za'ayi gidan marayun zamuje mu samo É—an acan kagama babu wanda ya isa ya zarge mu, sukuma hukumar gidan marayun zamusan yadda zamuyi da su tun da akwai Æ´aÆ´an banki".
Shiru Na'ima tayi yayin da ta zurma cikin tunani naÉ—an wani lokaci kana ta ce
"To shike nan amma kuna ganin baza'a sami wata matsala ba ko?, dan nifa bana so maganar tafita naso ace munyi shi anan sakanin mu basai ansako wasu ciki ba".
Dr Mukhtar yace "Ai samun É—a a gidan marayu shine kawai mafita kuma rufin asiri, tun da jakar ku na cike da makullin kulle bakin wasu ai an gama,
idan mukace a nan ne zamu samu to za'a iya samin matsala dan har yanzu asibitin nan idon hukuma yana kansa sun saka ido sosai suna jiran suji wani abun yakuma fita su sami mafakar hujjojin da suka tara, wan da naki bada damar hujjar tasu tayi aiki idan da kuÉ—i meye bazamuyi ba".
ido Raliya ta kanne tace "Wai wan da kayiwa ai kin nan nawa ne yabaka haka?".
wani munafukar dariya yayi kana yace
"Miliyan 10 tabani kuma ko wani wata ina É—aukar albashi daga gurin ta".
"Bayan 10 million tana kan baka wani kuÉ—in kuma?".
Na'ima tayi maganar da fuskar mamaki.
yace "To ai kin wasa nayi mata kaɗan fa yarage yataɓa nawa aikin dan ma Dad yatsaya da gaske kan lamarin, canjin ɗa ai bakaramin kasada bane, jigo na canza mata da shi ɗa na miji na musan ya mata da mace, to kuɗin wasa suke samu a kasar nan 10 million wani kuɗi ne agurin su,
duk wata 300k nake É—au ka a gurin ta tukuicin godiya."
dariya suka sheke da shi cikin muryar dariya Na'ima tace
"Kai Mukhtar wlh bakada dama shine ko É—an salalan nan babu."
"Haba wani salala ke me zakiyi da kuÉ—i yanzu kinada jakar kuÉ—i a gefen ki, kinada ABDALLAH IDRIS ABDALLAH me kuma zakiyi da kuÉ—i, ai nine abun a taimaka dan ko Raliya kuÉ—in da take samu bani samun irin sa".
mikewa Na'ima tayi tana faÉ—in
"Kace dai bazaka bamu ba kawai musan in da muka ajiye ka, aminiya tashi mutafi gidan marayun nan yanzu ba'a bori da sanyin jiki".

zai yi magana sai kuma yayi shiru sakamakon hayaniyar da yaji ke É—an tashi daga can waje da alama a cikin parlou'n asibitin ne in da mutane ke zama dan jiran ganin likita.
wata nurse ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izinin shigowa,
ɗan rusunawa tayi tace "Sir gawasu sun zo da alama haihuwa ce sai dai basuzo da kayan haihuwa ba, nace sukawo kuɗin kayan haihuwar sunce basuda kuɗi,nace to su koma suzo da kuɗi sunki tafiya, kuma yara ne dukan su nayi ta tuhumar su ina iyayen su sunyi shiru na ce suje su kira babba san nan su taho da kayan karɓar haihuwa ko kuɗin kayan tunda akwai anan sunki tafiya,kuma da alamu labour take sosai zata iya haihuwa cikin mintuna kalilan gasu can zaune a parlour sunki tafiya."
Dr yace "Yara kuma? akira su su shigo."
tace "Okay sir."
tajuya da sauri ta fita, jim kaÉ—an suka shigo,
tana gaba Æ´ammata biyu na biye da ita É—aya da ciki rukuku É—ayar kuma tana tallafe da ita, sanye da uniform ajikin ta. da kaga mai cikin da alama nakuda take sosai dan sai tauna baki da yarfe hannu take tana ta faman zubda kwalla da faÉ—in "Wayyo nashiga uku."
Dr yadubi wacce suke tare da mai cikin yace
"Me yake faruwa wace matsalar ke tafe da ku?."
tace
"Haihuwa tazo shine na rako ta."
Na'ima da Raliya kuwa ido suka zubawa yaran wan da akalla shekarun su bazai wuce 16 ba.
Dr Mukhtar yace
"Ke kaÉ—ai kika rakota haihuwar ina iyayen ku?".
shiru yarinyar tayi tana duban mai cikin da sai daÉ—a shiga yanayin nakuda gadan-gadan take.
sai kuma ta dubi likitan cikin rauni tace
"Iyayen ta suna gida nima kawai tazone tace narako ta asibiti."
É—an shiru Dr mukhtar yayi idanunsa a kansu kana yace
"To ina mijin ki?." yayi maganar idanunsa akan mai cikin.
duk kanin su shiru sukayi sai raba ido suke, ido ya kure su da kyau yakuma faɗin "Nace ina mijin ta? ita kaɗai zata taho haihuwa babu wani babba ko shi mijin baisan haihuwar yataso bane kirashi a waya yanzu yazo dan bana karɓar haihuwa sai an ajiye kuɗi an kuma sa hannu tukun".
Chapter 2 · 0% Book details