← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 34

Sashe 31

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da misalin karfe 4:30Pm na farka na ɗan ji daɗin jiki na sabo da baccin da nayi amma dai hanci na na nan a toshe ciwon kan ma haƙa.
ahankali nayi ƙoƙarin ɗaga kan Nasmah a hannun na na maida shi kan pillow sai ta farka, sai na ɗago ta nayi da ita bayi wanka nayi mata kana nafito da ita, ni ma na koma nayi.
bayan na idar da sallar la'asar na saka kaya itama na saka mata, kana na ruko hannun ta muka fito, kasa muka sauka muna shiga cikin parlour'n Naseem da Faty suka shigo, zama nayi ina faÉ—in
"Gara da bakuzo tun É—azu ba sai da muka gama baccin mu."
dariya Faty tayi tare da faÉ—in
"Kai Adda HAMDAH ai har munfito É—azu zamu zo, sai kuma muka wuce gun lilo, da mun hana ku bacci."
murmushi nayi na ce "Gara da kuka tsaya can gun lelon ai da yanzu kun hana mu yin bacci ku bakuyi ba mu ku hana mu yi."
Talatu data dire tray'n abinci saman kan table É—in gaban mu, ta ce
"Barkan ku da hutawa, uban É—aki na muje kayi wanka naga gimbiya kam da wankan ta ta sauko, kai ne ka tsaya gun lilo ko ka É—ebo rana."
tayi maganar tana ruko hannun Naseem.
sukayi cikin bedroom...

Washegari ya kasance ranar Monday bayan su Naseem sun tafi makaranta bacci na koma,
cikin bacci naji wayata tana ring, idanuna a rufe na mika hannu na janyo wayar, na É—ago shi tare da buÉ—e idanu na kan shi, ganin sunan daya bayyana kan screen É—in wayar.
yasani ware idanuna sosai, sunan shugaban makarantar su Naseem ne.
nayi saurin É—aga kiran tare da kai wayar kunne, muryar sa na jiyo hankali tashe yana faÉ—in
"Madam gamu a asibiti Nasmah ta."
É—ip wayar ta yanke cikin tsananin firgici na mike zaune nan da nan na nimi baccin da nake ji É—in na rasa,
hannunna na ɓari na dan na number sa na mai da masa kiran, yayin da nake jin kirji na na dukan uku-uku.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." na furta a fili, wayar tayi ta ring har ta kusa yanke wa kafin aka É—aga da sauri cikin matukar firgici da tashin hankali na ce
"Ina Nasmah take me ya same ta?!." ya ce
"Gata nan kwance ta......!

Mommyn Twins ce

12

Da sauri cikin matukar tashin hankali tun kan ya karasa abun da zai faÉ—a na ce "Tamutu tamutu ko?!!."
nayi maganar hankali a mugun tashe dan nagama tsinkewa da yan da naji yake maganar.
ya ce "A'a Madam ba mutuwa tayi ba, dama bata da lafiya ne?,
tun zuwan su School É—in Aunty'n su tace taga yanayin ta kamar batajin daÉ—i, shine ta tambaye ta sai tace mata wai kan ta keyi mata zafi, to tafita taje ta É—auko magani a office kenan ta dawo ta samu tana rike da kanta tana kuka tana faÉ—in kanta zafi, kan tayi aune ma ta faÉ—i kasa a sume, tun É—azu muna asibiti ban so kira na sanar ba sai ta farfaÉ—o amma har yanzu likitoci sun kasa shawo kan ta."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un wlh lafiyar ta lau ta bar gida."
na furta da karfi yayin da jikina ke cirawa cikin azama na duro a gadon wayar na kare a kunnena ina tambayar sa wani asibiti ne, yana faÉ—a min nakashe wayar batare da na tsaya sauraran abun da yake cigaba da faÉ—a ba.
wardrobe na buɗe na janyo mayafi na takalmi mara tudu na saka da sauri nafita na nufi ƙasa, bibbiyu nake haɗa steps,ina sauka na nufi kofa har ina haɗawa da sassarfa.
su Talatu suna zaune cukin parlour'n da sauri suka mike ganin yanda na sauko a firgice, tambaya ta me ke faruwa suka shiga yi suna biyo ni a baya,
tuni nayi waje ban tsaya basu amsa ba, har parking lot suka bini, suna tambayar abun da ya faru. sai a lokacin na ce da su "Nasmah ce ke asibiti asume."
salati suka shiga yi suna tambayar garin yaya.
wan nan karon ban tsaya basu amsa ba dan ji nake tsayuwa basu amsa ma ɓata lokaci ne.
kan kace me sabbin Security É—in da aka zuba cikin gidan sun iso in da muke, ganin yan da su Talatu suketa rafka salati, suma duk tambayar da suke ban tsaya basu amsa ba, su Talatu ne suka sanar musu abun da ke faruwa.

Yakubu nashiga kwaÉ—awa kira,
da sauri haÉ—e da gudu yafito daga cikin É—akin su, da sauri na shige cikin mota, yana ganin haka ya koma É—akin da sauri ya fito rike da makullin motar cikin hanzarin yashige motar.
cikin matukar da muwa da rawar murya nace
"Yakubu kayi sauri ko ka bani key É—in motar ni naja."
key yayi wa motar tare da figar ta aguje, da gudu mai gadi ya buÉ—e get muka fita a gidan, sai da muka haura titi kafin yake tambaya ta in da zamu nafaÉ—a masa sunan asibitin.
duk gudun da Yakubu yake gani nake kamar bayayi asibitin tayi min nisa.
Number da aka kira ni da shi aka sanar min da tana asibitin na kuma kira wayar tayi ta ring ba'a É—aga ba,
kuka ne naji ya zo min nayi saurin toshe baki na a raina nake faÉ—in
"Shike nan ta mutu."
kokarin mai da kiran nake dai-dai nan najiyo muryar Yakubu yana faÉ—in
"Hajiya mun iso."
da sauri na É—ago dan ban san har mun iso ba.
da sauri na buÉ—e motar na fito batare da na jira faÉ—in da yake bari ya zo ya buÉ—e min motar ba.
da sauri haÉ—e da sassarfa nayi cikin asibitin, a kofar shiga cikin parlour'n asibitin na haÉ—u da Aunty'n su Nasmah tana kokarin fitowa cikin sauri take tafiya da ka ganta gaba É—aya hankalin ta a tashe yake.
tana gani na ta juya da sauri tana faÉ—in
"Madam ta farfaÉ—o amma tana ta kuka."
da sauri nabi bayan ta ina faÉ—in "Ina take."
tun da ga cikin parlour'n nake jiyo kukan ta, da gudu nanufi kofar room É—in da nake jiyo kukan ta ciki,
wasu daga cikin ma'aikata asibitin sukayi yunkurin dakatar da ni, ban ko saurare su ba
na tura kofar na sa kai ciki.
ina ji Yakubu daya biyo ni yana sanar musu da ko ni waye.

Likitoci har guda uku a tsaye a kan ta suna rirrike da ita sai ihu take tana bige-bige, da gudu na isa in da take na kusa sakanin su na rungume ta,sai kawai nima na fashe da kuka ina faÉ—in
"Nasmah me ya same ki, me ya same ki Nasmah?!!."
kuka sosai na ke ina rungume da ita, itama kukan take tana ta fisge-fisgen nan kamar wacce bata cikin gayyacin ta.
Chapter 31 · 0% Book details