Sashe 24
Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shan gaba na yayi a fusace cikin muryar da yake nuni da tsantsar gargaÉ—i ya ce
"Yazamo na karshe fitar kalmar nan daga bakin ki, idan kika sake kika sake furta kalmar durkuso cikin rayuwar su, bazan sa ayi miki hukunci ba ni zan yi miki hukunci da kai na! ki sake nanata kalmar basu da uba kigani!."
yayi maganar cikin
fusataccen amon sauti, a zaburi namatsa gefe dan maganar nashi ta shige ni rabon da ayi min ihu da tsawa irin haka har na mance, shiyasa abun yazo min a sabo.
ba zato naji kafata ta ta dama ta wuce cikin abu kamar rami, da sauri na juyo sai kawai na tafi luuu gaba É—aya, idanuna na rumse da karfi ina jiran najini a kasa, sai jina nayi zundum cikin ruwa,
kara na ƙwalla wan na hakan yayi sana diyyar wucewan ruwa cikin bakina,
fafutukan niman numfashi nashiga yi, da niman ceton kaina, duk buÉ—e bakin da zanyi sai ruwa ya wuce ciki, nayi-nayi na iya mike wa tsaye na kasa, duk da kuwa zurfin ruwan idan zan shiga da kafata iya kirji na yake zuwa min.
Shiko Ahmad da sauri ya faÉ—a cikin swimming pool É—in ganin yan da ta ke bubbuga hannu da yin sama da shi
da alamun niman ceto.
hannu na ya ruko da karfi ya É—ago ni yamikar da ni tsaye.
ruwan da ke kunshe cikin bakina dana ki haÉ—iye shi dan cikar da ciki na yayi, na furzar da shi tare da sauke tagwayen numfashi, ina damke cikina da ruwa yacika shi, a wahalce na na É—ago hannuna É—aya na share fuskata tare da tattaro gashi na daya rufe min fuska, na mai da shi baya,
ida nuna na sauke kansa, dai-dai lokacin daya kai
hannu ya share ruwan dake fuskar sa, sai a lokacin na lura ruwan dana furzar daga baki na a fuskar sa na fesa.
shima idanun sa a kai na tun daga gashin kaina yake bina da kallo har kasa, kasan cewar rana ya taso ya haske cikin ruwan ana iya kallon abun da ke kasan ruwan.
dogon tsaki na ja dan nakasa magana tsabar haushi, bugu da kari yan da cikina ya cike tam da ruwa.
a hankali na soma tafiya cikin ruwan har na isa bakin gaɓar gun matattakalar shiga da kuma fita daga cikin swimming pool ɗin,
a sannu na soma hawa maganar sa na jiyo,
"Ki tsaya a taimaka miki kirage ruwan da kika sha."
cigaba da haurawa ta nayi batare da
waige ko tsayu ba,
ina karasa fita da sauri nayi hanyar part É—ina jin zuciya ta na tashi, cikin sauri na shige cikin side É—in direct sama na haura,
ina shiga bedroom É—ina da sauri nashige bathroom, ai tun kan na karasa bakin toilet nafara sheka amai tsakiyar bayin, zallar ruwa narika aman sa.
da kan sa aman ya tsaya kamar yadda yazo bazato ba sammani, numfashi narika sauke wa ina tallafe da cikina da yanzu nake jin sa wayam, sai dai É—an murÉ—ar da yake min.
a daddafe na tsaftace bayin na tuɓe kayan jikina da suka jike gaba ɗaya na wurgasu cikin wishing machine, nafito doguwar riga mara nauyi na zura, kana na isa bakin gado na zauna ina mai cigaba da sauke numfashi,
tsaki narika ja a-kai-a-kai tsabar haushin da nake jin kaina ciki, har lokacin kasa iya furta komai nayi.
idan na tuna ruwan da na hambuÉ—a a cikina sai naji kamar nayi ihu, sauki na ma É—aya jiya-jiyan nan nasa aka fidda ruwan dake cikin swimming pool É—in, aka wanke cikin sa a ka kuma zuba wani, ban kuma yi amfani da shi ba.
wani dogon tsakin naja yayin da na kai bayana na kwanta kan gado.
mamakin karfin hali da takaicin mutumin nan suka rika zuwar min,
wai ni yake yiwa gargaÉ—i kan Æ´aÆ´ana,
ya kuma yi sanadiyyar faÉ—uwa ta cikin ruwa, badun kwanana na gaba ba wata kila da yanzu ana kan shirin kai ni makwanci.
Dole nasa jami'an tsaro cikin lamarin dan ban amin ta da mutumin nan ba, awani dalili zai rika shiga min cikin gida kai tsaye har yarika yimin barazana kan Æ´aÆ´ana.
Mikewa zaune nayi tare da É—aukar waya ta, number Mr Aliyu nakira wato P.A na, ko da ya É—aga bayan mun gaisa na É—aura da faÉ—in
"Mr Aliyu ina so a saka min jami'an tsaro a gidan nan."
da sauri ya ce "Madam meke faruwa akwai matsala ne?."
yayi maganar cikin nuna damuwa sosai kana yaci gaba da faÉ—in
"Ai Madam tun farko shiyasa nace azuba jami'an tsaro gida kamar wannan dole sai da manyan Security masu rike da bindiga, kikace abar mai gadi kaÉ—ai ma ya isa, ina kuwa zai isar wa gida kamar wannan, yanzu kuwa zan fita in sha Allahu anjima zamu zo da su."
na ce "To Allah ya kaimu."
nakashe wayar, ina katse kiran kiran Bappa na shigowa, na daga da sallama daga cikin wayar Bappa ya ce
"HAMDAH ko kina bacci ne?." na ce
"A'a ba bacci nake ba Bappa." ya ce
"To kizo yanzu maza." da sauri na mike jin yana faÉ—in haka ya kashe wayar.
cikin hanzari na nufi side ɗin su Bappa da sauri na dan Bappa bai taɓa min irin wannan kiran ba nasan komai akayi akwai wata masalar, da ire-iren waɗan nan tunanin nashige cikin side ɗin.
turus naja na tsaya yayin da jikina ya kama ɓari ganin Yakubu durkushe yana kuma rungume da uniform ɗin su Nasmah,
cikin tsanani tashin hankali na karaso cikin parlour'n gaban Yakubu natsaya cikin rawar murya da kuka keson kwace min na ce
"Ina yara na?!."
nayi maganar cikin rawar murya sosai tuni hawaye yacike ido na.
Bappa da ke zaune kan kujera ya dube ni tare da faÉ—in
"Zo zauna nan HAMDAH." yanu na min kujerar da ke kusa da shi, ban iya bin umurnin Bappa ba dan kuwa hankali na yakai kololuwa wajen tashi, duba da yan da Yakubu yake ɓari yakuma rungume uniform ɗin gam-gam.
Inna Wuro ce ta mike tazo taruko faÉ—ata ta jamyo ni ta zaunar da ni kan kujerar, tuni hawayen da suka cuko idona suka fara zuba. Bappa ya girgiza kai yana faÉ—in
"Muma mun shiga irin yanayin nan da kika shiga a yan da yashigo mana kamar an rakoshi a guje,
tam bayar da na fara mishi shine ina yaran suke ganin uniform É—in su a hannun shi, da kyar ya iya ba mu amsar suna nan kuma suna makaranta, yaji tsoron ya tinkare ki kai tsaye shiyasa yazo nan."
kai Yakubu yashiga gyaÉ—a wa yana É—an rarrafowa da guiwar sa yana kuma faÉ—in
"Dan Allah dan Annabi Bappa Malam ka rokar min afuwar ta wlh duk yan da naso na hana faruwan haka bai yuwu ba, wlh fin karfi aka nuna min muraran."
Bappa ya katse shi ta hanyar É—aga masa hannu ya ce
"Ya isa." kana Bappa ya juyo da kallon sa gare ni ya ce
"Lokacin da suka fita zai kai su makaranta a hanya suka haɗu da Ahmad Tijjani Sabil ya sai da su, yake tambayar su ina zasuje ganin ba hanyar makarantar su suka nufa ba, sannan kuma ga wata uniform ɗin daban a jikin su, to shine shi Yakubun ya shai da masa in da zasu, shikuma Ahmad yace kada ya kuskura ya kaisu wannan makarantar yawuce ya kaisu wan can makarantar su, to dai a takaice tare suka tafi da shi wancan makarantar da aka cire su yasa aka basu wani uniform, yakuma tuɓe musu najikin su shine yabashi wan da yacire musun yace ya mai do shi gida,
to shine ya dawo hankali tashe yakuma ji tsoron yaje ya tinkare ki da batun shine ya zo nan,
kafin na kira ki sai da na kira shi Ahmad ɗin sabo da ina da lambar sa dan ranar da yazo nan na karɓi lambar sa, ashe dai zatayi amfani gaba akuma irin wannan ranar,shine na kira sa dan ji dalilin sa na yin hakan,
ya bani tabbacin dalilin sa na yin haka, kuma na gamsu, yace yawai ta canza musu makaranta a karancin shekarun zai iya birkita musu ƙwaƙwalwa gara abar su idan suka gama can ɗin kan lokacin sun daɗa wayo sai suyi gaba, kuma nima nayi nazari naga hakan yafi abarsu a can ɗin, nayi masa maganar dalilin ki na canza musu makarantar yace za'a kara tsaro sosai babu wata matsala."
Yakubu da tun da Bappa ya soma maganar yake ai kin gyaÉ—a kai da buga bayan hannun sa cikin É—aya tafin hannun sa, yayi kalar tausayi, Bappa na gama maganar shima ya É—aura da faÉ—in "Wlh tallahi Hajiya na rantse miki da Allah, ba laifi na bane, na dage wajan ganin ba'a kuma samin wata matsala ba kamar yadda nayi miki alkawari, wlh Hajiya dana buÉ—e baki zanyi masa musu dawani yafito daga cikin motar sa, ya shake ni sai da naji kamshin kabari, shi ya hana mutumin da yanzu na sheka,
ki gafar ceni Hajiya ki tai maka kibar ni a bakin aiki na."