← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuka take sosai tana faÉ—in zasu yanka ta,
Na'ima kuwa carap tayi tace "To ni zan rike miki É—an ni ina son shi nasan idan kika fita yaddashi zakiyi ko ba haka ba?".
tafaÉ—a tana duban ta.
da sauri yarin yar ta gyaÉ—a kai tace
"Wlh in natafi da shi gida ne za'a yanka ni in naje dashi gida ne."
Na'ima ta ce "To ya isa, in kika je da shi gida ne za'a yanka ki idan kika fita da shi daga nan kuma yaddashi zakiyi to ni ina son shi zan rike shi".
hannu ta saka ta buÉ—e jaka ta ciro kuÉ—i masu yawa gudan dubu-duba ne a É—aÉ—É—aure É—auri uku,wacce a kalla ko wani É—auri guda yakai 100k ta mika wa yarin yar tana faÉ—in
"Karɓa in kinje kya nima abun da zaki rika ci wan da yakamata masu jego suci, ba sai kin jira iyayen ki sun yi miki ba tun da nasan cewa bayimiki zasuyi ba, da ma ace ɗan da uba ne tun da bashi da shi kuwa ba mai saurarar ki, gashi sai kije kiyi jego shikuma ɗan ina son shi zan rike shi, dan bazan iya zuba ido ina gani azalinci ɗan da baiji ba baigani ba ku mutane kurika jin tsoron Allah, ɗan da bai san komai ba aje a jefar da shi ko a kashe shi."
da sauri yarin yar ta mika hannu ta karɓi kuɗin har hanunta na rawa ganin yawan kuɗin, kana ta yimusu godiya ta mike da sauri ta fita,
har takai bakin kofa Na'ima tace
"Idan kikaje gida aka tanbaye ki ina abun da kika haifa sai kice yana ina?."
"Ya mutu tun a ciki!."
tayi maganar cike da karfafawa tana daÉ—a dunkule makudan kuÉ—in da ta bata.
murmushi Na'ima tayi tare da faÉ—in "Da kyau." da sauri yarin yar tayi waje ta haye abun hawa ta wuce gidan su cikin zillumi da tsoro..
bayan fitar yarinyar Raliya da Dr Mukhtar suka tuntsire da dariya, cikin muryar dariya Dr Mukhtar yace
"Kin ji Na'ima har da É—an guntun wa'azin ta wai ku mutane kurika jin tsoron Allah tun da kin samu a sama ai dole kijefo wa'azi ciki hhhhh."
"In da kuÉ—i meye bazan samu ba kai bakaji takashe É—an nata tun a ciki ba, wannan kuma ni na haifa."
tayi maganar tana leko fuskar yaron da yake baccin sa.
Dr mukhtar ya gyara zama tare da sauke numfashi sannan ya ce
"To yan zu ya za'ayi ne?."
tace "Dr ni da na haihu kuma me yazaunar da ni a nan a kaini labour room mana."
dariya ya sheke dashi Raliya ma dariyar tayi tana faÉ—in
"Ai kuwa mai jego a gado yakamata a same ta a kwance ba'a zaune a office É—in likita ba."
nan suka mike suka nufi labour room bayan sun gama shirya duk yan da abun zai tafi.
suna shiga ta haura gado ta kwanta, tayi shame-shame kamar wacce ta haihu da gaske.

Waya Na'ima ta mikawa Raliya tace
"Kirashi a waya".
Raliya ta amsa ta danna number SALEEM......!

Mommyn Twins ce

🌺 *HAMDAH* 🌺
*WASA FARIN GIRKI!!*✍�

*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book 3)_

Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta.
domin biyan kuɗin littafin sai ka-ki tuntuɓi wannan number 08034690723

🅿�2

Wayar tayi ta ringing har ya yanke bai É—aga ba, ta dubi Na'ima tace
"Bai É—aga bafa. "
ta ce "Sake kiran shi kin san shi ai murÉ—aÉ—É—en mutum ne idan baiyi ra'ayi ba bazai É—aga ba yanzu haka wayar tana kusa da shi É—agawar ne dai baiga dama ba."
kuma kiran nasa tayi namma har ya yanke bai É—aga ba, sai da ta kirashi har sau uku a na huÉ—u ne ya É—aga.
ganin ya É—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da faÉ—in
"Asslamu'alaikum SALEEMA Raliya ce muna asibiti da Na'ima tahaihu."
SALEEM dake zaune a office yana ta tarkasa Æ´an kayakin sa dan locin tashin sa yayi har ya wuce ma, Æ´an wasu aiyuka ne suka tsaida shi. yamike zumbur yana faÉ—in.
"Haihuwa kuma? yaushe cikin nata yakai na haihuwa cikin ya fita kenan?."
yajero tanbayar da alamun hankalin sa a É—an tashe yake.
ta ce "Eh haihuwa ce ba fita cikin yayi ba sai dai bakwaini ta haifa É—a na miji."
numfashi yasauke jin akasin abun da yake zato,shi gaba É—aya jin lamarin na bazata ya mantar da shi zata iya haifar cikin tun da yakai wata bakwai, ya ce
"Ina jaririn yake yanzu yana cikin wani hali yana dai lafiya ko?."
"Eh gashi can a cikin kwalba."
katse wayar yayi batare da yace komai ba, Na'ima da take jin duk abun da yake faÉ—a kasan cewar tasa wayar a amsa kuwa ne ta ce
"Lallai ma wannan wato shi ta jaririn yake bazai fa taɓa sauyawa duka ba."
dariya Raliya tayi tare da faÉ—in
"SALEEMA kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi bafa zai sauya ba dan kuwa a jinin sa yake."

SALEEM na kashe wayar, wayar Mamie ya kira, zaune Mamie take da su Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Ummi kiran sa ya shigo.
bayan sun gaisa yake faÉ—a mata Na'ima ta haihu.
"Haihuwa." Mamie tafada da karfi
kana ta ce "Wani irin haihuwa ciki wata bakwai." ya fuskanci yanayin da yashi ga lokacin da Raliya ta sanar masa da haihuwar shi Mamie ta shiga yanzu.
yace "Eh ta haihu bakwaini ta haifa tana asibiti ma yanzu."
"To Allah ya raya." Mamie ta faÉ—a a takaice tare da kashe wayarta.
gaba daya hankalin Æ´an cikin parlour'n yakoma kan Mamie, Ummi ce da sauri tace
"Wa ta haihu Na'ima ce?".
Mamie tace
"Wai haka, wai ta haihu". Mamie ta faɗa tana taɓe baki.
Ummi ko baki ta washe tana fadin
"Ikon Allah, kaji ikon Allah ko to Allah dai yasa abun da aka haifa nacikin koshin lafiya".
baki Mamie takuma taɓewa tare da faɗin
"Ina kuwa zai zama cikin koshin lafiya ciki wata bakwai sai dai yabada wahala dai".
a ɓangaren Aunty Jaleela ma fuska ta yamutsa tana faɗin
"Gayyan wahala dai ciki wata bakwai ai ba arziki."
"Ina kuwa arziki duk uban iyayi da cikin ashe dai rabin halitta za'a haifo ba arziki."
Aunty Rafee'at ta faÉ—a, tana tura É—ankwali gaban goshi.
duk kanin su in ka gansu babu wani mai farin ciki da jin daÉ—in haihuwar, akasin Ummi da fuskarta ke É—auke da annuri bakin ta ya kasa rufuwa sai faÉ—i take
"Kai masha Allah Allah dai ya raya mana."

mikewa Ummi tayi tana cigaba da faÉ—in
"Kai masha Allah zamu wuce asibitin ba yakamata mu tafi asibitin yanzu".
Mamie ta kawar da kai gefe tare da faÉ—in
"Ummi'n Fauzan ni gaskiya ba yanzu zanje asibitin nan ba gaskiya inaga kamar ina da abun yi, ai dare yayi yanzu ga magriba yakawo kai."
Ummi ta girgiza kai tana faÉ—in
"Kai Mamie'n Nusaiba yakama ta dai muje yanzu ace babu wani nashi a can gaskiya baiyi ba."
fuska Aunty Rafee'at takuma yamutsawa tana faÉ—in "Um ni kamma kucire ni a tafiyar dan yanzu Abba'n Adeel zaizo ya É—auke mu."
dakuwa Ummi tayi mata tare da faÉ—in
"Maza tashi kushirya ke Jaleela tashi maza muje".
Aunty Jaleela da tazo har wuya ta kwaɓe fuska kana tace
"Ni wlh ina ji ma kamar kar inje dan nima Daddy'n Fadeel nasan zai zo yanzu."
haɓa Ummi ta rike tana sallallami da kyar dai ta tirsasa musu ta samu suka fita, suka nufi asibitin bayan sun sanar wa su Abbu.

A asibitin suka tadda SALEEM shima isowarsa kenan a tare suka shiga cikin asibitin.
direct É—akin hutu suka nufa in da nurse tayi musu jagora zuwa ciki,take sanar musu da cewa an mai da Na'ima can domin ta huta.
nan suka tadda Na'ima kwance tana ta sauke numfarfashi Raliya na tsaye a kanta tana ta yi mata sannu.
da sauri Ummi ta matso in da take tana faÉ—in
"Sannu sannu kinji Na'ima, kin sami kanki kalau?".
dakyar ta buÉ—e baki cikin yanayin mutum yasha wuya murya can kasan makoshi tace
"Lafiya lau."
Mamie ko kallo É—aya tayi mata kana tace mata Sannu.
namma da kai ta amsa.
Aunty Rafee'at kam ko kallo bata ishe taba, Aunty Jaleela ce ma a sama tace mata sannu ita ma.
Ya SALEEM da ya naÉ—e hannu a baya yana tsaye tagurin kafafun ta yadan dubeta kana yace
"Ina yaron yake?". Raliya tace "Yana can ansashi a kwalba.
kai ya jinjina cikin yanayin nan nasa, ya maida duban sa kan nurse É—in da ta yimisu jagora yace
"Muje a nuna mana in da yake, ina Dr yake?".
ta ce "Yana office".
fita sukayi duka har da Raliya,
Raliya tayi saurin shigan office É—in Dr tare suka fito da shi, ya mikawa Ya SALEEM hannu suka gaisa ba yabo ba fallasa Ya SALEEM ya amsa masa gaisuwar, kana ya gaida su Mamie sannan ya wuce dasu É—akin da aka ajiye jaririn wan da yake karkashin kulawar na'urori..

Can suka hango jaririn cikin kwalba
wan da ake saka jariran dabasu kai watannin haihuwa ba, yanata wutsul-wutsul da kafafunsa.
murmushi Raliya tayi a kasan ranta dan ganin shirin su yana tafiya yan da ya kamata.
da sauri Ya SALEEM ya karasa jikin kwalbar yana leka cikin kwalbar.
su Ummi ma gaba É—ayan su suka karaso jikin kwalbar,
Ido Mamie ta kurawa jarijin da ake kiran sa da bakwaini gashi dai ba wani girma yake da shi ba É—an kankani ne, sai dai yanayin sa da wayon faskarsa ya girmi na bakwaini.
kai ta girgiza tare da juyawa ta kalli likitar tace
"Wannan shine bakwaini an ya ma kuwa anyi lissafin cikin nan dai dai ko dai tara ne an ɓata lissafin kaga yaron da wayon sa."
da sauri Raliya tace
"Bai cika tara ba bakwai ne ai ko jiya ma sai da mukayi lissafin watannin da ita, yau kuma sai ga haihuwa kingan shi ai É—an misilili da shi".
Ummi tace "Ai kuwa gashi É—an kankani irin su idan suka tashi girma sai an gansu dan sai anci tuwo an koshi kafin a iya É—aukar su".
Ya SALEEM kam duk baya jin su dan ya gama shagalta da kallon yaron wai shine yau da É—a, wannan É—an nasa ne, wani murmushi yayi a kasan ransa wan da har sai da yabayyano kan fuskarsa.
Chapter 4 · 0% Book details