← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Rafee'at data kafe yaron da ido tarr sai lokacin tayi magana.
"Wai wannan yaron shine bakwaini gaskiya wannan baiyi kamada bakwaini ba sai dai in ku kuka ɓata da lissafin".
tayi maganar cikin gatsali.
wani kallon sama da kasa Raliya ta bita da shi. Aunty Rafee'at ma irin kallon ta wasa mata tare da girgiza kai tana cigaba da yi mata wani kallon shekeke, sannan ta juya ta fita a cikin É—akin bayan ta gama ai kawa Raliya kallo masu cike da ma'anoni da yawa..
ko minti 30 basuyi a asibitin ba Mamie tace sutafi, haka dai suka fita suka koma gida.

Haushi da bakin ciki kamar Na'ima tayi yaya, wai ace kalar gaisuwar da surukar ta zata yi mata kenan, babu wani gaisuwa mai nuna tausaya wa babu wani nuna farin cikin samo mata jika da tayi.
Raliya tace "Ni da É—ina da ke gajen hakuri dan Allah kibar wannan maganar kiyi shiru, ke kam dai ba kin haihu ba ina ruwan ki da su, wan da kika haifa masa ne idan ya miki zakiji zafi,ina ruwan ki da su ba wa É—an su kika haifa ba, can ta matse musu ke meye damuwar ki, kinga wannan shegiyar yarinyar
zan nuna mata ni Æ´ar bariki ce cikakkiya ma kuwa ciki da waje na,
wai shegiyar Rafee'at É—innan kinga wani kallon da take min,
kinga wani kallon da take min kuwa, zan nuna mata halina bata sanni bane."
Na'ima tace "Him in dai wannan Rafee'at É—in ce ta wuce sammanin ki, wannan yarin yar da kike gani nima inada cikin ta kuma zanyi maganin ta, zan je musamman gurin boka domin yamin maganin ta,
zatagane da ni take rabu da ita mance da ita dan wlh sai ta gane kuskuren ta."

Jin an murÉ—a handle yasasu yin shiru da zancen nasu,
Na'ima ta gyara kwanciyar ta kamar ɗazu, ta daɗa marairace fuska da shagwaɓe fuska.
ya karaso bakin gadon yadube ta kana yace
"Ya jikin?". cikin makirci da salon iya kirsa tace
"My SALEEM kaga É—an mu ko,ya bani wahala yaron nan,
É—an ka yabani wahala My SALEEM da kyar na iya haifo shi."
gefen fuskarsa ya shafo tare da naÉ—e hannun sa É—aya a bayan sa,
"ÆŠa na."
yafaÉ—a a kasan zuciyar sa yayin da yake jin wani abu yana tsarga masa mai kama da farin ciki, can karkashin kasan zuciyar sa kuwa, jin wani abu mai nauyi yake yana kokarin tasowa sai kuma yanayi biyun suka shiga kokawa da junan su, yayin da farin cikin ya danne wancan nauyin da yake jin nauyin sa na yau yafi na kullum. har sai da yakai hannu ya dafe kahon zuciyar sa.
daga Na'ima har Raliya ido suka zuba masa ganin yan da ya dafe kirjin sa da karfi tare da rumtse idanunsa,
wani abu ne ya gilma masa cikin duhuwar kwayar idanunsa da suke a rufe, wani irin bugawa kirjin sa yayi kamar an fizgi zuciyar sa, sai yarika ganin wasu abubuwa guda uku masu haske suna yi masa yawo cikin ido yayin da bugun zuciyarsa ya tsanan ta, dai-dai lokacin da yaga abun suna daÉ—a tunkaro sa tamkar suna tahowa gare sa,
a zahiri kuma idanunsa a buÉ—e. sai kuma a sannu suka rika yin nesa dashi sai da sukayi nesa dashi sosai kana duhu takuma gilmawa sakanin su.
cikin tsananin karfi ya ware idanun sa, jin muryar Na'ima tana faÉ—in
"Ya dai My SALEEM?".
hannayen sa biyu ya cusa cikin sumar kansa kana ya burzar da wani huci mai zafi daga bakin sa
"I'm sorry."
ya faÉ—a tare da juyawa yabar É—akin da sauri, yayin da yake jin zuciyar sa naciga da yi masa nauyi, acikin Æ´an kwanakin nan hakan yana yawan faruwa da shi akai-akai, musamman in ya kwanta bacci yarika irin wannan mafarkan kenan, sai yari ganin haske guda uku suna dumfaro shi sai sunzo daf da shi sai su bashi baya yayin da duhu kuma zatazo ta mamaye hasken. abun da yake gani cikin mafarkin sa shi ke kokarin zuwa masa a zahiri, to ko bacci yafara a tsayen har ya fara mafarkin?.
yarika jefowa kansa tambayoyin da bashida amsar su..

Bayan sa Na'ima tabi da kallo cikin takai ci, a tunanin ta ɓarin jiki zaiyi idan yaji ta haihu, idan yaga ɗan kuma murna zai yi ba adadi, sai kuma gashi sai wani shashshan kamshi yake,batare da ya nuna farin ciki da hakan ba.

A can kuwa bayan komawar su Mamie suna tare a parlour kowa na faÉ—an albarkacin bakin sa.
Mamie kam sam taji wannan É—a bai kwanta mata a rai ba,
kwata-kwata taji É—an baya cikin ranta, tana yi masa wani irin kallon da ita kaÉ—ai tasan ma'anar sa.
Aunty Rafee'at fuska ta yamusa ganin su Fauzan da Nusaiba na ta murna wai matar Ya SALEEM ta haihu zasu sha suna tace
"Dalla kurufa mana baki, ni wallahi wannan É—an ma kwata-kwata bai min ba wlh ya É—auko jinin uwar sa, ni bai min kama da bakwai niba haka bakwaini yake,sau nawa nake ganin Æ´aÆ´an da ake haifarsu wata bakwai sai ace wai wannan É—an wata bakwai ne, to can ta matse mata sai taje ta ta fama taje can tayi ta haifar bakwaini ita ta sani".
kai Mamie ta girgiza.
Aunty Jaleela tace
"Ai wlh nima Aunty Rafee'at ɗan baimin kama da ɗan bakwai ba, sai dai idan ko sun ɓata lissafi ko kuma wani munafurcin ta ke kullawa ciki yafi wata bakwai tace bakwai to meye amfanin hakan, meye na cewa ciki wata bakwai bayan tasan cikin yafi bakwai ɗin".
Ummi ko cemusu tayi
"To ku in ban da abun ku ta yiwu ta ɓata da lissafin ne in mutum ya ɓata da lissafi kam shi zai rika lissafi kuma alhalin ba haka bane, ai ba wani abu bane kakan iya ɓata da lissafi, kuma ai ana iya haifar wata bakwai yayi rai me lafiya ma yatashi har yafi ɗan wata taran kwari da kuzari, kar ku mance fa a asibiti ta haihu in ba bakwai ba taya za'ayi a sashi a kwalba likitan ai yafiku sanin me yake, Allah dai ya rayashi da imani".
"To amin".
cewar su dakaji amin É—in kasan baikai can kasar zuci ba...

Bayan kwana uku
tun da sukaje sau É—aya basu kara zuwa ba sai ranar da ta cika kwana uku shima da kyar Ummi tasa Mamie suka koma asibitin, anan suka tadda Æ´an gidan su Na'ima, nan ma basu wani jima ba suka baro asibitin.
satin su Na'ima biyu a asibitin, zaune suke da kawar ta Raliya Na'ima ta dubeta tana faÉ—in
"Kai Raliya wlh nagaji da zaman asibitin nan haka,
wai shin dole ne sai mun yi wata biyu a asibitin nan, dole wai saimunyi wata biyu wlh nagaji da zaman asibitin nan, wai dole ne har sai É—an yacika wata tara kafin mu koma gida, gaskiya asan yan da za'ayi kije ki sami Dr asan yan da za'ayi gaskiya, wlh nagaji da zaman asibitin sati fiyu fa ina nan,gaskiya kije ki same shi asan yan da za'ayi nakoma gida."
Raliya tace
"Gaskiya nimafa nagaji da sintirin yau asibiti gobe asibitin nan,kullum kenan mutum na hanyar zuwa asibiti alhalin duk kanin ku lafiyar ku lau, jariri yana nan yana shan madarar sa ke kina nan kina narkar abincin ki,
nikam mafa inada wasu a hannu wlh ina da wan da na karɓi kuɗin su, akwai wan da na karɓi kuɗin sa na kwana uku gashi nan ko wuni ɗaya bamuyi da shi ba, sakanina da shi da daddare mu kwana shi da yaso muje Abuja muɗan shana,
gaskiya bari naje na samu Mukhtar asan yanda za'ayi ki koma gida, nasamu naje su fanshi kuÉ—in su".
ta karashe maganar tana mikewa tsaye ta fita ta nufu office É—in Dr.

Bayan Raliya sun gama tattaunawa da Dr Mukhtar yace
"To gaskiya akwai yadda za'ayi zata iya komawa gida abisa ita ta tirsasa tagaji da zaman Asibitin, nikuma sai na bada wasu shawarwarin da zata É—auru akai bayan ta koma gidan".
nan suka tsara yan da abun zai tafi.
a ranar da yamma suka sami sallama suka koma gida, bayan shariÉ—oÉ—i da shawarwarin da Dr ya bata a gaban Æ´an uwan ta da kuma gogan wato SALEEM.
Chapter 5 · 0% Book details