← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 34

Sashe 10

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganar Bappa naji yana faÉ—in
"Muje ciki ko HAMDAH." da sauri nadawo daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba É—aya na shagalta da kallon gidan.
na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side É—in da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hankali nake taka kafata ina cigaba da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side É—in.
masha Allah É—an madaidaicin side É—in ya tsaru matuka.
side ne mai É—auke da 3 bedroom ko wanne da banÉ—aki a cikin sa, É—an madaidaicin parlour haÉ—e da dinning
da kitchen da komai da komai, an tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu.
É—akunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon É—akunan duk da shinfiÉ—ar su, sunsha lafiyayyun bedsheets.
bayan mungama zagaye cikin side É—in gaba É—aya, muka fita É—ayan side É—in dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side É—in yaji komai. kowa sai faÉ—in masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba É—aya yanayin tsarin gidan yatafi dani.
daga nan É—aya side É—in dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan,
koda muka fito daga cikin part É—in baki na washe nadubi Bappa dake ta faÉ—in
"Kai komai yayi masha Allah komai fa yayi yadda yakamata". baki nakuma washewa ina faÉ—in "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri É—aya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban".
dariya Bappa yayi kana yace "Da gaske gidan yayi kyau ko?."
"Wlh kuwa Bappa." nafaÉ—a da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side É—in nan dake a tsakiyar gidan wan da yazamana da sauran side É—in sun sashi a tsakiya.
a hankali muka isa bakin kofar da sauri É—aya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side É—in wan da yake na glass ya É—aura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass É—in yafara bada sauti É—an baya yaja kana ya dubeni yace
"Bismillah Madam É—an zo ki tsaya a nan."
ya nuna min kan step É—in da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali na matso na haura kan step É—in, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na É—aura hannuna kan nan yanuna min wani É—an zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri É—it-É—it sai kuma yakuma danna wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na É—aga hannuna.
ya juyo yana duba na kana yace
"Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum É—aya ke amfani da shi, sai kuma wancan". yanuna wata kofar dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace
"Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi."
ya murÉ—a handle É—in kofar yabuÉ—e muka shiga ciki.
sai gamu mun bayyana cikin wata katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!".
nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi,
Bappa ko karamar dariya yayi tare da jijjiga kai.
suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba É—aya na buÉ—e wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faÉ—an tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai misaltuba, yaji kayan alatu da more rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side É—in da muka shiga babu haÉ—i ko kaÉ—an.
bedroom É—in dake cikin parlour'n muka rika shiga É—aya bayan É—aya, bedroom ne zafafa har guda huÉ—u masu É—auke da tsalatsalan bathroom,
daga gefe da parlour'n kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe.
sama muka hauwa wan da shi kanshi step É—in haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima an kawatashi na musamman.
wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai banbancin kalolin kayan dake cikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da É—an ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu.
Antsara komai yadda yakamata sai tashi da sassanyan kamshi mai haÉ—e da kamshin sababbin kaya yake.
kai gidan ya haÉ—u fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa.

Kowa sai yaba kyau da tsaruwar gidan yake, É—aya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce
"Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?."
kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na maida dubana ga Bappa danaji yana faÉ—in
"Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana."
da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su suna nan".
ido na waro kamar a mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gyaÉ—awa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina faÉ—in
"Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii".

Dariya Bappa yayi yace "To sake min hannu kada ki ɓala".
ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake.

Mutumin yacigaba da faÉ—in
"To masha Allah wannan side É—in shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai."

Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na dubi Bappa ina waro ido nace
"Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "DaÉ—ina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina faÉ—in "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki ne." ido na waro tare da sa dariya nace
"Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi.
rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su.
da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?."
yace "Suna can ruga". nace "Bappa shine bakazo da su ba kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa."
nafaÉ—a ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma faÉ—a ganin yayi shiru bai ce komai ba,
yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima".
ido nakuma warowa da karfi nace "Bappa ni kaÉ—ai za'a barni a wannan gari gudan, da ni kaÉ—ai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna."
nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro zai rika bani ni kaÉ—ai a cikin sa, kaji Bappa?."
nafaÉ—a ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba."
na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH."
dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na washe baki,
yace "To meyasa bakisa hakorin hajji ba acan?."
"Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa."
"Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya."
yayi maganar yana mikewa tare da cigaba da faÉ—in
"To ni bazanje masallaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah".
da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita.

Da sauri na mike inata daÉ—a waigen cikin parlour'n inshiga wan É—akin in fita inshiga wancan haka narikayi, daga nan kuma naja hannun Nasmah muka haura sama ina faÉ—in
"Bari naje na zaɓi bedroom ɗin da yafi min."
koda muka haura ɗakunan duka na shiga kana nazaɓi ɗaki ɗaya, nan cikin bedroom ɗin nabuɗe bathroom ɗin sa na shiga mai girma da tsaruwa kamar ɗakin kwana.
kayan jikina na tuɓe duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin daɗin ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin bathroom ɗin, sannan nafito.
Na sami Nasmah gaban mirror ta É—auki janbaki sai murkawa take a bakin ta.
dariya nayi ina faÉ—in
"Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki".
itama baki ta washe tana cigaba da kwaɓula janbakin a bakin ta.
da sauri na sauka kasa akwatin kayan mu na janyo nadawo É—akin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina buÉ—e wa ido na ware cikin wardrobe É—in ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sai dai ba a É—inke suke ba,a hankali na zaro É—aya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan...
Chapter 10 · 0% Book details