← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 34

Sashe 12

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,
mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waɗan da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan ɗauke su ai ki irin gidajen masu kuɗi ɗin nan, a cikin su na zaɓi guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.
É—aya na É—auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side É—in,
na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma É—ayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar side É—in su dakuma girkin su.
nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba É—aya.
mun zauna da su na É—an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.

Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin buÉ—e masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar su kwarai da gaske wajen ganin an É—ibi ma'aikata masu inganci.

Bayan wani lokaci

Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai yatafi dai-dai.
tuni nasa aka baiwa Fatu uniform a É—aya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan.

Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a É—iba, a karkashin paudasion É—ina domin basu tallafin wasu kuÉ—aÉ—en da zai jamusu jari domin dogaro da kansu, matasa hamsin da kuma mata hamsin,na tura da kuÉ—aÉ—en tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion.
a hankali na mike tsaye tare da yin mika haÉ—e da salati, wayoyina na tattara haÉ—e da sabuwar system É—ina, na haura sama,
kan bedside na ajiye su kana na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side É—in su Bappa.
har na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lagos,
mikewa nayi na fita dan ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan.
da gudu Nasmah ta shigo tana faÉ—in
"Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji".
Naseem shima dagudu yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da faÉ—in "Naseem kabari kar ka sa mata".
da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!�

Mommyn Twins ce

5

"Kai Naseem me zaka sa mata kai ka bari zata faÉ—i fa kabari."
nayi maganar ina É—ago Nasmah cak na rungume ta a jikina, shiko dariyar yake yana matsowa in da muke ya É—aga hannun sa sama tare da yin É—agelgel da kafa, yana washe baki,
na ce "Idan ka zo nan sai na mare ka, zo kagani zo ka samata kagani,
dariya sosai yarika yana faÉ—in
"Mommy dan tamata ne dan ta mata wannan."
"To ka samata kagani sai na maka bulala."
kiran Talatu mai kula dasu nashiga yi ina faÉ—in
"Talatu zo ki kaishi wa É—awisu ta cakwaÉ—e shi tun da dai shima sa mata jiji zaiyi."
Talatu ta iso da sauri tana faÉ—in
"Ayi hakuri Hajiya kar a kaishi wa É—awisu zata cake shi, zo nan Naseem kada kasa mata ko, so kake a kaika wa É—awisu ta cake ka,zo ko É—an lele na mene ne zaka sawa Nasmah É—in?."
É—an karamin tafin hannunsa da ya dunkule ya buÉ—e kaÉ—an ya nuna mata kana ya kuma dun kulewa yana cigaba da dariya, "Lalala shine zaka sa mata?."
cewar Talatu tayi maganar haÉ—e da dariya, kai ya gyaÉ—a yana washe baki, duban Fatu nayi ina faÉ—in
"Wato Fatu keda Naseem kuke sawa Nasmah ta abin tsoro ko? to bazata sake wasa da ku ba."
dariya Fatu tayi tare da faÉ—in
"Allah Adda HAMDAH kin ga bansan in da yasamo ba kawai ganin sa nayi ya shigo da shi a hannunsa,malam buÉ—e takarda ne fa."
"Au malam buɗe takarda ne ya ɗauko shine yake so ya sa mata to bari yagani sai an kaishi wa ɗawisu shima, shine baki karɓa ba ko Fatu kika tayashi tsoratar da ita."
"Allah Adda HAMDAH binshi nake na karɓa shine yagudu."
Talatu ta É—auke shi tabuÉ—e hannunsa taciro abun tana faÉ—in
"Kawo shi nan a yasar da shi kada ka saka mata kaga tana jin tsoro, kaima kada ka sake É—auka a hannun ka."
tana rike da hannunsa tafita waje ta yasar da shi kana suka dawo ciki.
karaso wa cikin parlour nayi na zauna kan kujera tare da zaunar da Nasmah kan cinya ta, na dubi Fatu nace
"Fatu Bappa na ciki ne?."
tace "A'a yafita". sai kuma ta turo baki gaba tare da faÉ—in
"Adda HAMDAH nifa wannan sunan Fatun nace ki dai na faÉ—in shi, Fatun nan fa a can Ruga ne fa ake kiran Fatun nan tun da yanzu mutum yazo birni har yanzu ayi ta ce mishi wani Fatu, gaskiya Adda HAMDAH ni wlh na canza suna Fatu ai duk su Inna wuro ne suka wani lankwasa min suna yaya Mahmoud dake shi a birni yake ai Fatima yake cemin,haka jiya wata Æ´ar ajin mu tana ta min dariya wai ni Fatu, aradun Allah na canza suna ko a ajin mu ma na faÉ—a na canza suna".
dariya muka tuntsire da shi, Talatu tace
"To Fatu man yan gari me kike so ace miki kenan?".
"Ai sunana da yawa masu daÉ—i ma, Nana, Fatima, FaÉ—imatu, Faty Zarah duka gasunan masu daÉ—i sai a rika cewa mutum wani Fatu kamar rugo".
nace "To lallai kam kamar kin sani da ma kam wannan sunan bai dace da ke ba yanzu dai kawai Faty za'a rika ce miki."
tace "Yauwaaa Adda HAMDAH Faty wlh yama fi amma kuna ta cemin wani Fatu kamar rogo".
"Hhhhh Faty kenan Allah bakida dama".
tace "Yauwa Adda HAMDAH gashi kin iya faÉ—in sunan dai-dai mai daÉ—i".
kai kawai na girgiza ina dariyar ta.
tace "Zo muje muyi wasan mu o Nasmah."
nace "O'o kuje bazata biku ba kuje kusata kuka bazata biku ba kam kutafi ku."
"Allah bazan barshi yasa mata ba". fuskata na kawo dai-dai fuskar Nasmah nace
"Zaki bisu?". kai ta gyaÉ—a "To muje daga gun na duba ko Bappa ya dawo".
nafaÉ—a ina mikewa na direta kasa tare da ruko hannunta muka nufi side É—in su Inna wuro.
a parlour muka tadda Inna wuro Bappa bai dawo ba sai na zauna muna ɗan taɓa hira da ita.
muna nan zaune har Bappa ya shigo yazauna muka cigaba da hirar da shi, acikin hirar nake yi masa maganar yace kwarai kuwa ya dace kam aje domin a ganewa ido, in yaso satin sama sai a je, duk da akwai idanu da yawa akan lamarin. nace "Toh Allah yakai mu."
muna zaune sai ganin Naseem mukayi ya kin kimo school bag ɗin Faty, a tsakiyar parlour'n ya zauna ya tuttuɗe littatafan cikin jakar kasa ya ɗauki littafi guda ya buɗe yana ta gwalaɓe wai shi yana karatu.
dariya duka muka saka, Faty ko da gudu ta mike taje ta tattari litattafan ta tana ta faÉ—in
"Kai kasan meye a ciki ka iya karatu ne".
Inna woro tace "To ai karatun yake baki gani ba".
cikin muryar dariya nace "Um karatu yake ko gwalaɓe har da wani mike kafa kamar mai karatun gaskiya."
"Ah to gaskiya za'a saku a makaran ta tun da har ka iya É—auko littafi kazauna ka buÉ—e kana karatu".
cewar Bappa yana yi masa dariya.
"Wlh Bappa nima dama ina so a turasu makaranta amma a sona sai sun cika shekara uku da rabi, amma gashi nan bakin su ya buÉ—e kawai sutafi yanzu."
Bappa ya jinjina kai kana yace
"Kwarai kuwa ya kama ta kam tun yanzu, tun da ga bakin su nata kan buÉ—e wa a kai su makaranta yakarasa buÉ—ewar a can"....

A cikin satin akayi musu komai da komai nashiga makaranta, sai dai wata makarantar daban badaga cikin nawa ba, dan *HAM'NAS* International School Of Science Of Technology. suna da nisa saka nin mu, duk da dai shima makarantar da aka sasun yana da É—an nisa sai dai baikai su nisa ba,
Islamiyar da a kasasu kuma anan unguwar tamu yake.
ranar da zasu fara zuwa kuwa zo kaga murna wajen su, da misalin karfe 7 na safiya Talatu taga ma shirya su tsaf, Zulai kuma ta shirya musu lafiyayyen breakfast É—in su.
ina rike da hannun su muka fito in da Talatu ke biye da mu rike da school bag É—in su da baske, parking lot muka nufa, tun kan mukaraso Yakubu direba dake goge mota yayi hanzarin buÉ—e marfin motar, cike da ladabi yaÉ—an duka yana faÉ—in
"Barka da safiya Hajiya."
"Yauwa barka." nafaÉ—a cikin É—an jin nauyin yan da suke yimin idan zasu gaida ni, duk kanin ma'aikatan gidan sun girme min nesa ba kusa ba wasu ma sun haife ni sun juya,nakan ji nauyi a duk san da sukayi min irin wannan gaisuwar.
Nasmah naÉ—aga nasaka ta cikin motar, Naseem kam cemin yayi shi da kan sa zai shi, Talatu tayi dariya tana saka musu school bag É—in cikin mota tace
"Naseem iyayen rigima kai bazaka bari a saka ka ba da kan ka zaka shi ka girma ashe".
kai ya gyaÉ—a yana gyara zama tare da faÉ—in
"Eh nagima da kaina naciga."
tace "To babban zance ke kuma Nasmah yaushe zaki girma?". Nasmah ta cuno É—an karamin bakin ta gaba tace "Gobe dan gima ai".
murmushi nayi tare da shafa gefen suskar ta nace
"Au ke sai gobe zakiyi girman naki?". kai ta gyaÉ—a tana murmushi, kansu na shafa dukansu nace
"To sai an dawo ayi karatu sosai kunji".
sukace to. direba yaja mota ina É—aga musu hannu suma suna daga min
mai gadi yawangale get suka fita..
Chapter 12 · 0% Book details