← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 34

Sashe 11

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltuba, muna zaune har su Bappa suka dawo muka sauko parlour'n kasa muna ɗan taɓa hira dakuma kallon tv.
duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina faÉ—in
"Bappa ina zuwa."
sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na É—auko na buÉ—e jakar naciro wayoyin da jiya aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM É—in da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace
"Kagani Bappa jiya mutanen nan suka É—auke ni sukayi ta kaini bankuna sukayi ta buÉ—e min account, muna dawowa kuma suka bani waÉ—an nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga kuÉ—in da sukayi ta shigowa kawai kuÉ—i sunata shigowa cikin accounts É—in".
nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki.

Murmushi Bappa yayi irin nasu na manya kana yace "HAMDAH kenan ai kuÉ—in kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk waÉ—annan mutane dasuke ta zirga-zirga da É—awainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an É—aurasu ne jagora akan lamarin, shiyasa kikaga duk waÉ—an nan abubuwa suke faruwa duk abun da kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shiyasa sukace kihuta yanzu."
kai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min.
knocking É—in da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking É—in, na isa jikin kofar na buÉ—e,
wani nagani tsaye rike da basket har guda biyu a hannunsa, É—an risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya É—ago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel É—in su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki.
dinnig table ya isa ya aje kayan abincin kana yayi mana sallama yafita.
muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem.

Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka iso,
suna zaune a parlour nikuma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka É—unguma.
yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daÉ—an rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje É—ai-É—ai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.
daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi ɓaro-ɓaro.
idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buÉ—e,

Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu É—auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu É—auke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.

Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faÉ—a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..

Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije É—auko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side É—in dana matsawa Bappa sai ya zabi É—aya daga cikin side É—in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side É—in.
hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika É—aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,
ganin su yaÉ—an rage min kewa da begen family na.

Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka É—auki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai É—aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, É—aya motar kuma mutane huÉ—u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin ƙarfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka É—au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.

Sati biyu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faɗin
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin É—aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki É—aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba É—aya.
A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faÉ—in
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"Sannu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha Allahu".
yayi maganar tare da buÉ—e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar haÉ—e da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.

Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba É—aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin...
da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.
Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da ɗan karamin ƙwarya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace
"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya bacci".
Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".
ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaÉ—auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a É—aya É—akin dake kusa da nawa.
washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...
muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side É—in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faÉ—in
"Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban taɓa zuwa ba".
nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan
Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....

bayan kwana biyu
Chapter 11 · 0% Book details