← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🌺 *HAMDAH* 🌺
*WASA FARIN GIRKI!!*✍�

*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book 3)_

_(Bismillahirrahmanurrahim.) Alhamdulillah ina yiwa Ubangiji buwayi gagara misali godiya da ya kuma bani iko a karo na uku nakuma dawowa domin kawo muku cigaban labarin HAMDAH ina rokon Allah ya bani ikon kammala shi lafiya👏🏻_

(Afwan a karshen book 2 nasaka (After 1 year)
I'm so sorry typing ero ne👌🏻)

Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta.
domin biyan kuɗin littafin sai ka-ki tuntuɓi wannan number 08034690723

🅿�1

Bayan wani lokaci.
Tuni ai kin hajji ya karato gamasu niyya tuni aka fara shirye-shiryen tafiya ai kin hajji. kan kace me kasar Saudiyya tacika tayi makil da al'ummar Musulmi.
yanzu bama samun wani zama kullum muna hanyar zuwa bautar Ubangiji, ba dare ba rana kullum Bappa na tasani gaba wani sa'in tare muke tafiya da su Naseem da Nasmah,wani sa'in kuma na barsu wa Mammaa mahaifiyar Ukhtee kawata da nayi anan cikin masarautar Saudi jika ga Masarautar Saudi. dan tare muke tafiya da Ukhtee ita kuma Mammaa ciwon kafa ke damun ta bana bazata samu daman fita afara aikin hajji da itaba.
acewar ta sai an zurfafa ibada sosai kan lokacin Abdul Malik yayan Ukhtee da yake karatu can jami'ar Madina yashigo zai fita da ita guraren ibada a kan keken zama irin na masu ciwon kafa. kasan cewar na yaye su Nasmah kuma suna cin komai gashi sun saba da matar sosai, shi yasa wahalar su ta É—anyi min sauki ko zamu fita ban cika tafiya da suba....
cikin yarda da buwayar Ubangiji aka kamla ai kin hajji na wannan shekaran lafiya.�
tuni mahajjata suka fara komawa kasashen su,nan muma muka fara shiri damin ko mawa kasar mu.
ana gobe jirgin mu zata É—aga. tun safiyar ranar jama'ar dake cikin masarautar sukayi ta zuwa sallamar mu. duk wan da yazo sai ya nuna baison tafiyar mu wasu ga fuskokin su wasu kuwa sai sun kai ga furtawa. Ukhtee da Mammaa da tun safiyar ranar muke tare da su a side É—in mu,
suka tirje wai sam sai dai Bappa ya barni a nan, ai ko nan kowa yace ya barni shi ya tafi bayan wani lokaci sai na koma.
ni dai dariya kawai nake binsu da shi, sai dai zuwa yanzu jikina yayi sanyi ganin yan da Ukhtee take kuka.
bilhakki ta rungume Nasmah tana faÉ—in bazan tafi ba.
Bappa ko ido yake binsu da shi cike da mamakin ganin zunzurutun kauna gun waÉ—an nan larabawan.
ana cikin haka kiran Mahmoud ya shigo wayar Bapp.
nan yake sanar wa Bappa yasami masaniya daga shugaban kasar mu anfara duk ayyukan dana lissafa kuma bazai É—au wani lokaci ba insha Allah za'a gama,
Bappa yayi fatan alheri kana yakashe wayar.
koda naji labarin daga bakin Bappa nayi matukar mamaki dan ni har yau ganin abun nake kamar wasa bazai yiwu ba.
Bappa ya mai da hankalin sa kan mutanen da suke cikin parlour'n, abun da ya lura shine suna matukar son ba'i musamman wata kabilar, bugu da kari wan da Allah ya É—aukaka a cikin su, babu garin da zai waye wasu daga wasu unguwanni daban-daban wasu kuma daga É—an garuruwan dake gefen gari basu shigo ganina ba, na zamo abun kallo da hira a gurin su, haka zasuyi ta hotuna da ni da su Naseem.
numfashi Bappa ya sauke ganin gabaki É—ayan su kalma guda suke nanatawa..
dun dole Bappa ya amsa musu badun yaso ba da sharaÉ—in zasu sako ni a jirgi nan da É—an kwanaki kaÉ—an.
ai kuwa ihun murna Ukhtee ta sake ta rungume ni tana sunbata. gaba ki É—aya parlour'n yakaceme da murna...
washegari da misalin karfe 4 na asuba jirgin su Bappa ya ɗaga suwa kasar mu ta gado wato Nigeria�.
kafin ya tafi sai da yayi ta min nasihohi da jan hankali mai ratsa jiki..
tun da Bappa ya koma kusan kullum sai munyi waya ta wayar Ukhtee har da su Inna wuro.
Alhmdllh bazan ce komai ba game da zamata anan cikin masarautar Saudi batun samin kula da tarairaya ni da Æ´aÆ´ana kuwa ba'a magana...

A can kasar Nigeria cikin garin Bauchi state.

Na'ima ce da kawar ta Raliya,tafe cikin mota suka É—au hanyar wani asibiti dake nan cikin G.R.A wan da shine Na'imar ke zuwa awo.
Raliya ke jan motar Na'ima na zaune a gefen mai zaman banza.
Raliya ta É—an muskuta ta dubi kawar tata kana ta mai da idanun ta kan titi tare da faÉ—in
"Aminiya yanzu yanda kika tsaran nan kina ganin hakan zai yuwu kuwa baza'a sami wata matsala ba dai ko?".
Na'ima tasauke numfashi tare da gyara zaman ta cikin karfafawa da gaskata muradin ta tace "Kada ki damu aminiya Nice fa Na'ima baza'a sami wata matsala ba tabbas zai yiwu zai yiwu, yau É—in nan kuwa zan haihu, Raliya ina cikin haÉ—ari dole ne kawai na ai watar da hakan, kinsan kuwa jiya da daddare muna kwance da SALEEM yaÉ—aga rigata yana duban cikin yace shi har yanzu baya ganin garman cikin ciki wata 7 amma har yanzu bai taso ba,
kin san me yafi firgitani kuwa?".
tayi tambayar tana duban Raliya.
Raliya ta girgiza kai cikin takai ci taci gaba da faÉ—in
"Aminiya sunan wancan ɓatacciyar yarin yar, ya kira min har da min misali da ita, wai lokacin da take da ciki bai cika wata huɗu bama amma yaɗan taso".
ido Raliya ta waro tace
"What! ya akayi har ya iya tunota? to gaskiya kawata kada kiyi wasa".
Na'ima cikin damuwa da bakin cikin tuno da HAMDAH da SALEEM yayi tace
"Shiyasa nake son bin duk wata kofar da zaibi ya tuno da wancan banzar ɓatacciyar da ko a muce ko a raye oho, duk wata kofar zanbi na toshe duk da nasan bayida wani kataɓus, ko da ya tuno tan ma, amma ni kwata-kwata bana son na rikajin kwatankwacin irin sunan ta a bakin sa,
bakiji abun da boka yace min ba, yana son yara sosai hakan zai iya yin tasiri wajen rika tuno ta da ita da abun da ke cikin ta duk da hakan ba wani abun damuwa bane amma ni dai sam bana son jin kalmar sunan ta kan laɓɓan sa,
to ko yau da safen nan ma muna kwance dashi yaÉ—aga rigata yana shafa cikin yace wai anya abun da ke cikin nan yana da lafiya kuwa shi baya ganin yana girma,
nace masa ai jikina yabi Allah ya taimaka ma ina da tumbi,ke nifa kullum a narka abinci nake aciki na in kika ga abincin da nake ci yanzu wai dun kawai tumbi na ya kara girma,
yanzu Raliya cikin nan wata 7 ne yana daf da shiga wata 8 yazama dole na ɗau mataki in ba hakaba komai zai iya ɓaci,
kin ga wancan hatsabibiyar kanwar tasa Rafee'at ranar da muka haÉ—u a gidan su har habai ci take min wai mai cikin tuwo, ni har na fara zargin ko ta gane ne".
Raliya ta saki dariya har tana dukan sitiyarin motar tana faÉ—in
"Ai wannan Rafee'at É—in shegiyar gaske ce sai ana taka mata burki".

dai-dai nan suka isa get É—in asibitin, hon Raliya tayi mai tsoron bakin get É—in yawan gale musu get.
Chapter 1 · 0% Book details