Sashe 6
Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tun da suka koma gida yaron kullum a kwance yake idan akazo barka ma sai tace ba'a É—au kar sa sabo da likita yace, kada a rika yawan sa masa hannu, sai dai azo a ganshi a kwancen kawai acikin bargon da kullum yake dukunkune a ciki.
haka tayi ta rainon É—an da masu da ita da É—an ma'aikatan ta da kuma Æ´an uwan ta, koda waÉ—an da suke kanta sukaga nonon ta ba ruwa basu kawo komai ba sai cewa sukayi ai dama gaka wasu matan suke sai an nimi magani.
tuni aka nemo maganin wanke nono da ku ma ruwan nono, kan kace me ruwan nono yakawo tashiga shayar da É—a.
lokacin da suka cika wata biyu,wato É—an yacika wata tara kenan washegari tahaÉ—a wani gagarumin taro.
biki irin na masu ji da naira, biki akayi na gani na faÉ—a naira tayi kuka, ranar SALEEM katuwar saniya ya yanka da katon rago,
yaron yaci sunan baban Na'ima.
ko da taji sunan da ya raÉ—a masa sam bata so ba dan taso yayi wa babansa ne takwara.
yace mata shi halacci yayi mata yasa wa É—an sunan mahaifin ta.
ranar kuwa kaÉ—an ya rage Raliya suyi faÉ—a da Aunty Rafee'at kan cewa da Aunty Rafee'at tayi yaron ma ko kama da su baiyi ba duk da kuwa girman da yake ta karawa,amma ko alamar kama da su bayayi sai dai in ya É—auko zuriyar uwar sa dan ko kama da uwar tasa ma baiyi ba.
shike nan kawai suka kama zasuyi faÉ—a, wai akan me yasa Aunty Rafee'at zatace haka ai duk wan da yaga É—an yaga SALEEM, dan kuwa farin SALEEM É—in ma ya É—auko tun da kuwa yayi kama da uban sa ai ba sai yayi kama da dangin uban sa ba. cikin masifa da bala'i da tsagwaran bariki Raliya take maganar.
Aunty Rafee'at ma kuwa bata yi mata da sauki ba tayi mata wankin babban bargo.
Allah ma ya taimaka Ummi tazo sunan ita ta raba faÉ—ar. ta kora Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela tace duk su tafi an yafe musu sunan, dan ganin abun na daÉ—a girma dan har Aunty Jaleela tashiga faÉ—ar....
After 1 year
Acan kasar Saudi
Da sauri na fito daga cikin bedroom cikin hanzari jin kiran da Ukhtee take kwaɗa min, abakin kofa mukayi kiciɓus da ita, fuska na kwaɓe ganin tana yi min dariya
"Ni gaba É—aya kin firgita ni na É—auka wani abun ne".
nayi maganar cikin harshen larabcin da nake É—an tsinta a gurin ta.
murmushi tayi tare da ruko hannuna
tace "Zo ki gani ga É—an'uwan ki yazo shi yace nayi mishi magana da ke".
tayi maganar ne cikin yaren ta da kuma yanayin da zan fahimta, dan yanzu ba laifi nakan fahimci abun da ake faÉ—a da larafci har nakan iya É—an gwamusa wa wajen yin magana da bashi da tsawo mafi sauki.
ta janyo ni muka nufi parlour.
turus nayi ganin wan da yake zaune a parlour'n su Naseem da Nasmah sun zagaye shi sai zuba masa surutu suke.
sai kuma nayi murmushi tare da karasowa cikin parlou'n ina faÉ—in
"La Uncle Mahmoud kai ne yaushe ka zo?".
dan yanzu kunyar kirashi da sunan sa nake.
shima murmushin yayi yana faÉ—in
"Ban jima da isowa ba,Naseem yace min kina bacci da zaije ya taso kine nace a'a yabar hajiya ta huta".
baki nawashe ina zama kan kujera jin abun da ya faÉ—a
nace "Uncle Mahmoud kenan wai hajiya, hajiya kuma".
yace "Eh mana hajiya kai, taya za'a taso hajiya a bacci lokacin tashin ta baiyi ba ai dai gara abar hajiya tayi bacci da kyau da kyau".
dariya kawai nayi kana nace
"Sannu da zuwa ya hanya? yasu Bappa da Inna wuro da Fatu".
yace "Hanya lafiya lau, sai dai badaga gida nake ba, amma dai Duk suna Lafiya".
Naseem da Nasmah suka mike a jikin sa sukabi bayan Ukhtee aguje sukayi side É—in Mammaa.
janyo table É—in da ya É—aura system É—in sa a kai yayi, yajuyo shi ta gabana yana faÉ—in
"To hajiya komai fa ya kammala, shiya sa ma na dako musamman tun daga Nigeria zuwa nan na sarnar miki ki kuma ganewa idonki, ba sai an kira ki a waya an sanar miki ba."
Ido na kurawa system É—in, ganin bidiyoyi sunata bayyana cikin system É—in, masu É—auke da tamfasa-tamfasan gidaje wane a turai motoci gidajen mai masallatai makarantu haÉ—e da kamfanoni da dai sauran su.
cikin tsananin mamaki na dubeshi nace
"Wannan fa Uncle Mahmoud?".
nayi tambayar ina nuna cikin system É—i. yace "Ah ai kin ki ya kammala wakilci a ka naÉ—a ni domin a kawo miki kiganewa idon ki musamman nataso domin shi".
da É—in bin mamaki nakuma kallon hotunan dake bayyana kan system É—in kana na maida dubana gareshi nace
"WaÉ—an nan É—in?."
yace "Kwarai kuwa sune,nakine sun kammala yanzu ke kawai muke jira ki koma abubbuÉ—e su, sannan kuma ba a gari É—aya akayi su ba a state da dama ne nacikin kasar mu Nigeria, ga jerin sunayin garirruwan da akayi gine ginen a cikin sa".
ya daddanna system É—in,sai ga sunayen garuruwan sun bayyana da kuma abubuwan da akayi a kowa ni garin.
yace "Kin ga yanzu zaki koma Nigeria a dai-dai dan kullum sai Bappa yayi maga, yanzu ma yace mu dawo tare sai dai ni bagida zan koma ba zan wuce Uganda tare da abokan aiki na, akwai wani abun da zamuje muyi a can".
kai na jinjina dan nifa har yau ganin abun nake kamar wasa nace
"Him..Him.."
kasa magana ma kawai nayi sai Him. nake ta faÉ—a ina kallon ikon Allah,yayin da nakeyi wa Ubangiji buwayi gagara misali tasbihi a can kasar zuciya ta.
rufe system É—in yayi kana yace
"Kin ga abubuwa yan da suka kammala ko, ko mai masha Allah, yanzu wani suna kike ganin za a sakawa kamfanoni da gidajen mai dai duk sauran kaddarori, wani suna kike ganin ya dace a saka musu, domin idan akaje yin katin gayyata da sanarwa ayi amfani da wannan sunan, da zai zamo shine sunan duka kaddarorin".
Shiru nayi yayin da na saka yatsa na guda kan kuma tuna nayi sama da ido na alamun tafiya duniyar tunani, tare da É—an kyafkyafta idon.
kana nayi kasa da idon cikin washe baki nace
"Yauwa na tuno sunan da nake so a saka masa *HAM'NAS*".
nayi kaganar cikin zakuwa ina cigaba da washe baki.
yanayin yadda nake maganar sai da ya bashi dariya ya ce
"To meye ma'anar *HAM'NAS* É—in kuma".
fuskata narufe da tafin hannuna cikin muryar dariya haÉ—e da zakuwar jin yadda na haÉ—a kalmomin suka tafi normal nace
"Kaga ma anar sa, HAM sunana ma'ana HAMDAH, NAS kuma Naseem and Nasmah".
dariya sosai ya sake yana faÉ—in
"Kaga yarin ya mai basira, tabbas wannan suna yayi kuwa ba shakka *HAM'NAS* Co Fitroleum Nigeria Limited *HAM'NAS* Intranational School Of Science And Technology *HAM'NAS* Store Complex *HAM'NAS* Clinics *HAM'NAS* International Hospital, Eh ba shakka lallai sunan yayi *HAM'NAS* Allah ya taimaka yayi jagora".
tsabar zakuwa kasa kuma cewa komai nayi sai baki na da yakasa rufuwa..�
A ranar da yamma Mahmoud ya wuce Uganda........�
Mommyn Twins ce
HMD
🅿�3