← Book details Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Hamdah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga can waje nake jiyo muryar su Bappa ina kokarin mike wa suka turo kofar, Bappa na gaba Inna Wuro Faty Yakubu da Sule direban su Bappa, suka shigo.
hankali tashe Bappa yake faÉ—in
"Subhanalillahi garin yaya me ya same ta haka?."
dai-dai nan suka karaso bakin gadon da Nasmah take kwance.
Bappa ya leko fuskar ta yana cigaba da faÉ—in
"Amma ta farfaÉ—o ko."
Ahmad ya ce "Eh ta farfaÉ—o yan zu dai bacci take."
"Masha Allah, kaji ikon Allah ko yarin ya tabar gida lafiya sai kuma ga ciwo, kai sannu Nasmah."
Inna Wuro ta faÉ—a tana shafa kanta. Bappa ya dubi Ahmad yana faÉ—in
"Sannu Ahmad sannu fa da kokari Allah ya saka da alheri."
murmushi yayi kana suka
shiga gaisawa, bayan gaisuwa da jajen abun da yafaru Bappa ke faÉ—in
"Wai haka kawai ta suma kuma me likita ya ce ke da mun ta?."
Ahmad da idanun sa ke kan Nasmah dake ta baccin ta har yanzu kana ya ce
"Typhoid ne har yayi mata (C) da mamaki ace wai ciwo irin haka har yayi yawa a jikin yaro irin haka ba'a sani ba, har yakai matakin da zai iya sumar da ita wai duk ba'a sani ba."
Bappa ya ce "Ikon Allah amma kuwa abun da mamaki, wai da ma bata da lafiya ne HAMDAH? ko irin zazzaɓi a tsatstsayen nan ne take?."
ya karasa maganar yana duba na. da sauri ganin yan da wannan Ahmad É—in yake taso ya mai da alhakin ciwon ta kaina.
na ce "Lafiyar ta lau bata kuma zazzaɓi a tsatstsaye."
"Kuma bata taɓa ce miki wani gurin ta na ciwo ba, yaro ke nan Allah sarki kuma kema baki taɓa lura da yanayin ta ya sauya ba."
cewar Inna Wuro, tayi maganar cikin jimami da alhinin ciwon nata.
"Babu wani alamar da na taɓa gani na ciwo tattare da ita, kuma bata taɓa cemin wani gurin ta na ciwo ba, in ban da shekaran jiya da nake
kwance kai na na ciwo ita ma tazo ta ce min kanta na mata zafi, kuma nasan a lokacin É—in dan nima na ce kai na nayi min ciwo ne shi yasa ita ma ta faÉ—a."
nakarasa maganar ina É—aga hanci sama dan ganin yan da É—an shishshigin nan keta wani girgiza kai. da sauri na mai da idanuna kan sa jin yana faÉ—in
"Ashe dai ta ma faÉ—a miki bata da lafiya amma bakiyi serious a kai ba, dan ta faÉ—i kan ta na zafi lokacin da naki yake ciwo sai ya zama nata karya ne?,
taya za'ayi ki fahimci hakan tun da baki da wayon sanin haka."
ido na waro baki buÉ—e jin yakuma jifata da kalmar rashin wayo,wai shin wannan mutumin me yake jin kansa ne,shi ji yake yafi kowa wayo kowa yi masa kallon rashin wayo yake?.
a kufule na buÉ—i baki zanyi magana, Bappa ya katse ni da faÉ—in
"Ai shi yaro idan ba lura kayi da yananin saba wani É—an bashi da azancin faÉ—ar abun da ke damin sa, ko da yana jin wani gurin sa na ciwo, sai dai in kai ka gane hakan daga yanayin sa na yau da kullum, kirika lura da yanayin su tanan zaki rika fahimtar ciwon su,
Allah sarki da gaske kan nata nayi mata ciwon ne sai tace yana yi mata zafi, Allah yabaki lafiya Nasmah."
Amin duk aka amsa da shi, baki na tura gaba muna gaÉ—a ido dashi na murguÉ—a masa baki, wani murmushi ya sake sai da dimple É—in sa suka bayyana,ya mai da idanunsa kan Nasmah yayin da fuskarsa ke nan É—auke da murmushin nan.
ido na ɗan kurawa fuskar sa wan da dimple ya daɗa kawata shi. baki na taɓe ina mai ɗauke idanuna a kansa...

Muna nan cikin É—akin kiran sallar azahar ne yasa su Bappa fita dan zuwa masallaci, har da shi, yarage daga ni sai Inna Wuro da Faty.
Inna Wuro ta shiga toilet É—in cikin É—akin ta yi al'wala tafito tace da ni naje nima nayi muje masallacin cikin asibitin muyi sallah, tun da ga Faty in muka dawo sai itama taje tayi... muna isa masallacin ana idar da sallah, su mazan suka koma ciki mukuma muka shige cikin masallacin.
ko da muka idar muka koma ciki, abakin gadon na kusa da Nasmah in da É—azu yake nan yanzu ma yake zaune.
zaman mu baifi da minti 20 ba akayi knocking É—in kofa, Yakubu dake tsaye ta kusa da kofar yabuÉ—e.
wasu maza guda biyu suka shigo niki-niki da kayan abinci duk kanin su sanye da rigonan irin na ma'aikatar hotel.
cikin girmamawa suka shiga gaida Ahmad kana suka gaida Æ´an cikin É—akin, suka dire manyan basket É—in dasuka shigo dashi, nan suka shiga zuba abinci suna mikawa kowa, da mamaki nake kallon su dan nidai a sani na ban bada umurnin kawo abinci daga wani hotel ba.
maganar É—aya daga cikin mutanen naji ya na faÉ—in
"Gashi hajiya." É—ago idanuna nayi daga kan wayar da nake natsawa na dube shi, plt É—in abinci yake miko min, kai na girgiza tare da faÉ—in
"Nakoshi."
"A'a me kikaci HAMDAH nasan tun fitar ki ba abin da kika ci."
cewar Bappa yana duba na.
"Bana jin yunwa." nafaÉ—a ina mai da idanuna kan wayar. "Zama da yunwa bashi da amfani wan da gashi komai yazo da sauki kici abinci itama bakiga tana baccin ta ba, sauki ce ke samuwa cikin bacci insha Allah."
Inna Wuro ta ce "Insha Allahu kuwa lafiya nata kan samuwa."
ni dai ban kuma cewa komai ba,
plt É—in abincin suka mikawa Faty dake kusa da ni.
wani É—an ma dai-dai cin basket daga cikin waÉ—an da suka shigo da su, abincin cikin sa na musamman shi suka zuba masa suka mika masa hannu ya daga tare da faÉ—in
"Akarawa kowa yaci."
Bappa da yakai loman abinci yahaɗi ye ya ce "A'a Ahmad ai wannan ma ya ishe mu maza karɓi ka ci wannan ya ishe mu haka ga abibci nan idan bamu koshi ba duk zamu kara, Allah ya saka da alkhairi an gode sosai Allah yakara buɗi."

Jin yan da Bappa yake ta zuba masa godiya yasa nasan cewa shi yayi odar abincin, baki na taɓe a raina nake faɗin
"Sai kace ance masa bamu ci abinci bane ko yunwa ke damin mu."
wayar sa ce tayi kara yamike yafita batare da ya karɓi abincin ba,
Bayan sa nabi da kallo
"Gulma shi da yasa a kawo dan tsabar gulma shi ne yaki ci to da waya mai da mayunwata."
Faty dake daf da ni ta juyo tare da faÉ—in
"Adda HAMDAH me kika ce?."
"A'a bada ke nake ba da wancan É—an gulmar nake."
"Wafa?." ta faÉ—a tana kallon waÉ—an da suke cikin É—akin.
"Ba kowa." na faÉ—a ina mai da idanuna kan waya.
tun da ya fita bai dawo ba ganin ya jima sosai bai dawon ba yasa nayi tunanin ya tafi ne, gara ma ya tafin É—an shishshigi.
har wajen la'asar muna nan zaune Nasmah bata farka ba zuwa lokacin kam bakin gadon na dawo na zauna. akai-akai likitoci ke zuwa duba ta, tun bayan fitar sa.
ana kiran sallar la'asar su Bappa suka fita bayi Inna Wuro ta shiga ta É—auro al'wala tafito ta shinfiÉ—a sallayar da nasa Yakubu ya É—auko a mota, ina nan zaune kusa da Nasmah da har lokacin take ta kan bacci, ido na tsura mata gaba É—aya yanzu na kagu ta farka. na É—au alwashin duk likitan da yakuma zuwa zai saka wani allura cikin drip É—in dake shigan ta zan hana, dan na lura kamar shi ke da É—a sata cigaba da baccin. ban tashi ba har sai da Faty ta idar da nata sallar, kana nashiga toilet É—in room É—in bayan nayi al'wala nazo na gabatar da salla.
ko da na idar ina nan zaune kan sallayar ina lazumi,da sauri na É—ago kaina jin Inna Wuro tana faÉ—in
"Nasmah kin farka ne?."
da sauri na mike ganin tana É—an motsa hannun ta, da sauri Inna Wuro dake gefen ta ta roko hannun nata da aka mata karin ruwa da shi take ta kokarin É—aga shi,
cikin hanzarin na iso bakin gadon ina faÉ—in
"Nasmah Nasmah tashi kada ki sake komawa baccin nan."
a hankali ta buÉ—e idanun ta na bin cikin É—akin da kallo.
sannu Inna Wuro da Faty suka shiga jera mata.
É—aya hannun ta na roko da murmushi ganin idanun ta wasai naci gaba da faÉ—in
"Sannu Nasmah kan naki ya dai na yi miki zafin?."
fuska ta kwaɓe sai kuma ta fashe da kuka.
"Subhanallahi yi hakuri kinji Nasmah yi shiru kinji idan kikayi kuka kan zai ci gaba da yi miki zafin fa yi shiru abin ki."
Inna Wuro ta faÉ—a da alamun rarrashi.
kai na gyaÉ—a tare da faÉ—in
"Eh kin ji yi shiru abin ki Nasmah." sautin kukan nata takuma karawa tana ta kokarin fizge kannulan da ke hannun.
da sauri ya turo kofar ya shigo , cikin hanzari ya iso bakin gadon. ta gefen da nake ya tsaya tare da ruko hannun ta da hannuna ke kai, da sauri na ɗauke hannuna dan yan da ya sauke hannu nasa kan nata sai da ya taɓa nawa hannun.
É—an matsawa nayi ganin yan da mukayi daf da juna.
"Shiiit ya isa haka bar kukan nan."
ya faÉ—a yana shafa kanta kana ya É—ago wayar sa ya daddanna ya kai kunnen sa "Na shigo." yayi maganar yana sauke wayar.
kan ta yaci gaba da shafawa yana kuma cigaba da faÉ—in
"Yi shiru bari azo a cire miki wannan abun ki huta."
Chapter 33 · 0% Book details