← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 90

Sashe 8

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Yau kawani uku kenan da zubar da cikin jikin Lulu da batasan da shi ba ba kuma tasan an zubar ba. Ta ɗan ƙarasa jiyyarta ta kwanaki biyu yayinda Dada ke kula da ita a duk motsinta. Yanda ta miƙe da wuri zai baka tabbacin zuwan Dada yay mata daɗi, dan akoda yaushe tana nane da ita. Duk da tana jin kewar ƴan gidansu musamman Daddy, Uncle Yousuf, Da Ammah sai take ƙoƙarin dakewa da sakama ranta haushinsu akan basa sonta. Ga kuma Dada a kaikaice tana sake cusa mata laifinsu hadda sharri. A duk sanda kuma Dada ta ɗakko zancen Smart sai Lulu taja tsaki da yamutsa fuska cikin shagwaɓa tacema Dada bata son ji, ita a daina mata koda zancensa. Hakan nama Dada daɗi da sake zaburar da ita cusa ma Lulu ƙiyayyar Smart a zuciya har ma da su Uncle Yousuf. Tun ma abin baya tasiri a ran Lulu har ya fara a randa take cika kwanaki biyar da samun lafiya a bazata sai ga Alh. Sulaiman da Tajuddeen. Lokacin tana kwance a falo tana kallo. A zahiri ta warke ragal. Sai dai tana jin wani irin kasala da son shan fruits, dan rigima ma yau sai cewa tai a mata kunun gyaɗa. Da Dada tace ina za'a samo wata gyaɗa anan sai ta sanya musu kuka na gaske. Dole Dada tai kiran wani saurayi ɗan ƙawarta da suma suke nan Canada ɗin amma asalinsu ƴan Nigeria ne ya bazama nemawa Lulu gyaɗa. Sai ko gashi ya samo, Ummita ta amsa ta haɗa mata kunun data buƙata sannan aka samu lafiya. Wannan kunu shine a gabanta har zuwa yanzu lokaci-lokaci takan zuba tasha abinta har sai taji yakai mata sannan ta ajiye. Sororo tai da ganin Uncle ɗin nata da Tajuddeen, dan ita dai ganin nasu yazo mata a bazata. Yanayinta babu yabo babu fallasa ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Sai kuma ta ɗan dubi Tajuddeen a yatsune tare da balla masa hararar kallon ƙurillar da taga yana mata. Sanye take da doguwar riga kalar ja da tabi jikinta ta lafe, sai rigar sanyi data ajiye gefenta kasancewar gidan akwai hitter dake ɗumama ko'ina. Rigar ta fisga ta sanya tare da komawa kwancenta kamar yanda take da. Sai dai ta danna wani ɗan maɓalli dake gefen kujerar ya bada ƙara sai ga Ummita da sauri ta fito da ga wani ɗaki tana faɗin, “Aunty kina buƙatar wani abu n...” ta kasa ƙarasawa saboda ganin baƙi. Batare da Lulu ta kalleta ba ta ce, “Ki sanarma Dada anyi baƙi”. Ummita data zube tana gaida su Tajuddeen ta amsa da to tana miƙewa ta nufi ɗakin da Dada da Lulun ke kwana.
     Ta wutsiyar ido Alh. Sulaiman ke kallon Lulu da nazartar ta, ba yau ya fara fahimtar girman kai da izzar yarinyar ba irin ta uwarta da ma shegen ubanta ce. Dan duk da yake amsa sunan yayan mahaifiyarta bata wani sakewa da shi, hasalima a duk sanda suka haɗu takan dinga acting like tana jin haushinsa. Hakan yasa yake zargin ko mahaigunta ya sanar mata wani abu a kansa ne. Wata ƴar ƙaramar ƙwafa yayi ciki-ciki a ransa yana faɗin (Zan dawo dake cikin hankalinki ai yarinyabke da ubanki dama duk mai daure miki ƙugu). Tajuddeen kam kai tsaye ya kafe Lulu da kallo, itako duk da tana jin idanunsa a kanta tai biris da shi tamkar bama tasan ALLAH yay zamansa a falon ba da ga shi har ubansan. Laifin Tajuddeen ne ya shafi mahaifinsa Alh. Sulaiman a wajen Lulu, dan bama shi ba, duk wasu ƴan gidan su Tajuddeen Lulu ta tsanesu a dalilin Tajuddeen ɗin ba kamar yanda shi Alh. Sulaiman ke tunanin Daddy ya faɗama Lulun sirrinsa bane.
      Cikin nuna mamaki Dada dake fitowa ta ce, “A'a wai dama da gaske ne kuna tafen ashe dai?”.
          Murmushi Alh. Sulaiman yayi da amsa ma mahaifiyar tasa da “Wlhy kuwa Dada ai na tabbatar miki babu abinda zai hanamu zuwa. Idan muka gaisheki sai mu wuce mu duba Baba kuma duk da shi Tajuddeen zai dawo nan Canada ɗinne akwai aikin da zaiyi”. Dada bata samu damar bama ɗan nata amsa ba saboda miƙewar da jikanta yay Tajuddeen yaje ya rungumeta. Lulu da duk ke saurarensu gabanta ya faɗi jin wai Tajuddeen yazo aiki ne nan Canada. To lallai dolene kam tabar ƙasar nan kenan a wannan gaɓar. Dan bataga haɗin kifi da kaska ba tsakaninta da Tajuddeen bazasu taɓa kasancewa a inuwa guda ba. Tsam ta miƙe cike da izzar nan tata sai dai rashin ƙarfin jiki na ciwo duk ya cinyeta a tsaye ta ɗauki flaks ɗin kunun gyaɗarta ta bar falon. Su duka da kallo suka bita kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. Dada ta katse shirun da faɗin, “Bara yarinyar nan ta shirya muku abinci ko. Sannunku da hanya”.
    Bakin Tajuddeen a washe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya da ga dawowa hayyacin bin kallon Lulu da yay da ido ya kalli kakar tasu. Ido ya kashe mata tare da mata nuni da ɗakin da Lulu ta shiga da baki. Dada tai ƙaramar dariya da faɗin, “To Alhaji zumuɗinka kadai bi komai a hankali, dan bamu san wane kalar barbaɗe shegen yaron nan yay mata ba, maybe bata gama dawowa cikin hankalinta ba ta kuma butsare mana a karo na biyu kadai san halin taurin kai irin na Mawaddat da shegen fitina”.
        “Karki damu Grandma, komai zai tafi dai-dai kamar yanda aka tsarashi. Indai ni ne a wannan gaɓar babu garaje. Bamma san tasan komai har sai an ɗaura auren”.
     Ƙaramar dariya Dada tayi, yayinda Alh. Sulaiman ya kura musa ido kawai, sai dai baice dasu komai ba.......✍️

_🤔To an taɓa aure akan aurene? Yau naga lukutar masifa Dada da Alh. Tsule fa babu man kai zasu iya ɗaurawa...🚴🚴🚴_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣

.......“Kai ɗin banza da zanji tsoronka Sulaiman. Ka sannni kaima ai, ni na wuce maka kanwar lasa, sannan ni ƙadangaren bakin tulune a rayuwarka data abokanka ta yanda kuka rasa yanda zakuyi dani. Ƙarshen target ɗinku shine ku kasheni dai, kuma na tabbatar muku a randa kuka kasheni wlhy ko minti ɗaya bazan cika ba da ɗaukewar numfashi kuma duniya zatai muku zafin da sai kun gwammace mutuwa kamar ni, dan sai mutanen duniyar sun san suwaye ku. Idan ba tsoro kuke ji ba miyya hanaku aikatawar a tsahon shekarun nan. Miyasa kuka kasa bayan kunada kowacce irin dama? Miyasa baku aikata bane sulaiman? Ku kashenin mana? Maza ku kashenin idan kun cika ku tsagerane dan ALLAH!!”.
      Matuƙar razana Alh. Sulaiman yayi da kalaman Daddy, cikin ɓacin rai da zafafuwar zuciya ya nunashi da yatsa lips ɗinsa na rawa. “Haka kace ko?”.
          “Haka nace Sulaiman, idan kuma bakaji ba na sake maimaita maka. Kuma wlhy na baka daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci ɗiyata ta dawo gareni inba hakaba sai na sakaka nadama irin wadda sai ka gammaci mutuwa da rayuwa. Dan duk inda kasa ƙafa ka sani ni Isma'il ƙaddararka biye nake da kai. Plan ɗinku na gaba shine sakama Yousuf cocaine a kaya yayinda da zai baro ƙasar Chaina zuwa Nigeria. Bance ku fasaba dan ALLAH, amma ku sani wannan shine mabuɗin farko na kiran mutuwarku. Ni Isma'il kallon kitse kukema rogo kawai, dan ko poisining ɗin Baba da kukayi na barku ne kawai bisa wani dalilina na tarkon dana ɗanama rayuwarku. FURAR DANƘO NAKE, A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. Mawaddat kuwa bazan sake cemaka ina take ba, in dai har ita ɗin jinina ce da kanta zata maido kanta gida bisa bigiren bijire muku. Ku muje zuwa wasan a yanzu na shirya masa....”
          Har Daddy yabar office ɗin Alh. Sulaiman da yay sumar tsaye bai iya dawowa a hayyacinsa ba. Sai da Daddyn yay banging ƙofar ne ya zabura wata zufa na feso masa a illahirin jikinsa. Bai ma san sanda ya since hular kansa ya hau fifita da ita ba jikinsa ma wata irin rawar shiga ruɗani da tashin hankali. Ji yake kamar mafarki yakeyi, shin Isma'il da ya sani ne haka wai shin ko canja shi ankayina? wagga al'amari haka kamar a mahwalki. Shiy yasan Isma'il nada zuciya kam tabbas batun yanzu ba, amma bai taɓa tabbatar da zai iya wani yunƙuri ba bayan kafiyar daya sanshi da ita kawai musamman da yaga tunda suka fara ƴar tsamar nan Daddyn nayi tamkar yana shakkarsa a koda yaushe, lallai ya yarda bakatsinan mutum abin tsorone yau. Da ƙarfi ya hankaɗa kayan saman table ɗin nasa da nuna ƙofa a kausashe ya furta “Isma'il You really are playing with fire!!!....”

       (😂Daddy ni kaina ka shayar dani mamaki, ashe jinin katsinawan dai na aiki a jininka) 

       *_CANADA_*
Chapter 8 · 0% Book details