← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 90

Sashe 46

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Duk wani masoyin Arsenal ya halarci babban stadium ɗinsu da ke a cikin birnin London. Wasuma da ga ƙasashen ƙetare suka zo domin ganin sabon yaron na Arsenal da za'a gabatar saboda soyayyar da sukema club ɗin. An cika matuƙa da har sai da Smart ya dinga jin kansa na sara masa. Ga kuma masu kallo a television. Amma ya daure bakinsa na cikin ambaton ALLAH ya fuskanci masoya. Wani irin ihu da stadium ɗin ya ɗauka lokacin da yake shigowa fuskarsa ɗauke da sassanyan murmushi yana mai ɗaga musu hannayensa biyu yay dai-dai da wanda su Mubeen suka ɗauka suma a cikin falon gidansu da Lulu ce kawai babu tana can ɗakinta tana barci. Hatta AA na a hannun Daddy dan har shi ake wannan kallo. Fitowa tai a ruɗe, sai dai ganninsu duk suna kallon ƙwallo a tv kuma duka gidan ya sata tsayawa turus cikin dafe kai da jan tsaki. Babu ma wanda yasan tanayi dan hankalinsu bama ya wajen. Cikin jin haushi ta juya ta koma duk da tayi mamakin ganin harda Daddy da su Iya Tabawa wai ake kallon ƙwallo yau a gidan. Abu ne ita dai da bata taɓa gani ba. Ta dai san Mubeen nayi da su Hussain idan sun zo. Amma kosu Amrah ta sha jin suna faɗa da Mubeen idan zai kalla ƙwallo ya hanasu su kalla film. Amma wai yau sai gashi ƙwai da kwarkwatar gidan ta gani. Abinda ma Lulu bata lura da shi ba shine harda masu wanki duk suna a falon, dan suna da ga ƙasa ne zaune yasa bata gansu da ƙyau ba... Kamar yanda a gidan Daddy suke kallo a gidan su Smart ɗin ma hakane. Dan su Mubarak ne suka cika gidan da abokansu da samarin anguwa. Yayinda ba'a bar Abba a baya ba da ga shi har Ammah da sauran yaran gidan sun cika a falonsa danƙam dan shi yasa a tattaro kowa yazo. Ran Umma da Mama a mutuƙar ɓace yake. Zuciyar Umma bata nema fitowa ta baki ba sai da aka nuna Smart na shigowa cikin tsakkiyar tarin tawagar turawan nan yana ɗan wasa da ƙwallo, stadium ɗin ya ɗauki ihu kamar zai tsage. Sai kuma sanda aka ɗaga rigarsa mai lamba tara yanda suka ɗauki ihu mai jijjiga kunne ita zuciyarta suke jijjigawa, dan a bazata kawai sai ta fashe da kuka. Da farko babu ma wanda ya lura da ita sai da Huwaila ta ce, “Ummah ke kuwa miya sakaki kuka? Ko duk farin cikin ganin Yaya Hydar ɗinne?”.
     Lokacinne hankalin kowa ya koma kan Umma. Sai dai kafin ma wani ya iya cewa wani abu ta miƙe cikin rangaji kamar wadda tasha tai marisa ta nufi ƙofar fita. Ƙayataccen murmushi Abba da Ammah suka saki kusan lokaci guda. Yaranta dama duk wanda ke wajen zasu ɗaga hankalinsu su bita Abbah ya ce kowa ya koma ya zauna, idan kuma wani ya bita sai ransa ya ɓaci. Dole sukabi umarninsa. Da ga baya ma abinda ke faruwa ya ɗauke hankalinsu kowa ya manta da batun wata Umma can....

Sosai Smart ke jin farin ciki a ransa mara misali dan harda hawayen farin ciki ganin yanda waɗan nan ɗunbin al'umma suka amshesa da taruwa domin shi. Bakajin komai sai ambaton sunansa a wajen, _Smart Mawashi, Smart Mawashi_ dai. Yanda ma suke ambaton Mawashi ɗin abin dariya. Abinda ya ƙara tabbatarwa da mutane Smart Mawashi ya amsu yanda a yinin ranar kawai an saida copy na rigar JC mai ɗauke da sunansa kawai ta kai kimanin dubu hamsin. Wannan al'amari ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da gidajen jaridu. Yayinda masu fashin baƙi akan harkar ƙwallon ƙafan keta nasu aiki. Gida Nigeria musamman arewaci kuma garin Kano sun shiga matuƙar alfahari da ganin ɗan su yau a wani mataki na rayuwa da sai ɗan baiwa mai Sa'a kawai ne ke takawa. Hatta da social media babu abinda ke kai kawo sai hotunan Smart Mawashi da tarihin rayuwarsa. Hatta da hotunan bikinsa ranar sai da suka dawo sabbi a yawon media. Sai a lokacin ne Lulu tasan wainar da ake toyawa. Ita kasa ma fassara al'amarin tayi sam. Cikin sauri ta shiga bincike-bincike a media. Sai ko gashi ta ga duk abinda take buƙatar. Tsabar yanda al'amarin ya dakar mata zuciya bata iya furta komai ba. Dan datace ma zata tsananta tunani ko maganar Smart ɗin matsanancin ciwon kai da tsanarsa da take ji ke dawo mata sabuwa. Dan ma Alhmdllh zuwa yanzu akwai ɗan sassauci a a al'amarin kasancewar addu'a da aka duƙufa yi babu dare babu rana. Yau ɗin ma dai ta yini da ciwon kan, dan har dare tana kwance tana fama har sai da Daddy ya shigo yay mata addu'oi....

Bayan Smart ya fito da ga stadium hirarsa da ƴan jarida ta zama abu na biyu da ya sake zama babban topic a kansa a wannan yini. Ya bada tarihin rayuwarsa da yay matuƙar taɓa zukatan mutane harda masu hawaye, dan ma ya ɓoye kaso tara cikin goma ya bayyana abinda yake da buƙatar duniya ta sani ne kawai. Ya bayyana irin yanda ya tashi da son ƙwallo a zuciyarsa da taimakon da Abdull-Hameed Coach yay masa a rayuwa da matsalolin da ya samu da ga baya. An masa tambaya akan dalilinsa na zaɓar team ɗin Arsenal duk da sauran clubs biyu da suka riƙe wuta a zawarcinsa sun sake ƙara kuɗi amma yace Arsenal ɗin dai. Sai yay murmushi da faɗin “Arsenal club ne da tun yana yaro yake matuƙar so, sannan club ne mai ɗunbin tarihi da kuma ya ajiye tarihi da tarin masoya a duniya, sannan club ne one of the best in the world. Sannan yana da ƴan wasan da yake matuƙar so da kallo a matsayin madubinsa a cikin club ɗin irinsu Terry Herry. Patrick Vieira da sauransu.......”✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣

........A wajen Daddy ta karya kamar yanda ta faɗa. Sunata hirarsu cike da nishaɗi. A cikin hirar ne yake cemata yana son ya je ya ɗan huta kwana biyu da ga nan zaiga doctor ɗinsa da kuma wani business da zai yi a England. Batare da ta kawo komai a ranta ba dan harga ALLAH bata san a ina Smart yake ba yanzu, ta ce, Daddy badan ina akan gaɓar wani case ba ALLAH nima dana bika na ɗan huta kona 1week ne. Da ga nan ina son na shiga U.S ma duba wasu takarduna a gidan can”.
       Da ƴar tsokana Daddy ya ce, “To ko na jiraki ne Sweetheart. Kin san fa na daɗe bamuyi tafiya tare ba ina jin kewar hakan”.
      Dariya tayi da faɗin, “Daddy karka sa Naseer ya ɗauka na ƙwace masa fadarsa ta autanci fa.”
   Shima darawar yay cike da nishaɗi yana faɗin, “Ai yace yanzu shi ba auta bane. AA ne Auta. Banda ƙarfin hali an taɓa ƙwace ɗan wani gida a bama wasu.”
          Murmushi Lulu tai da cewa, “Nakune ai Daddy, wake da iko da shi sama da ku?”.
      “A'a fa Mawaddat son kai da maida ɗan wani naka. Da haka ne ai da kema na haƙura na barma su Dada. Mahaifinsa na sane da abinsa kafin ya waiwayone kawai. Yanzu dai ki duba idan kinada dama zuwa hutun sai na jirakin, dan nima zan shiga U.S ɗin insha ALLAH. Nanny ɗinki ma ta kirani wai bata da lafiya sosai zata koma ƙasarsu Gambia tai jiyya. Amma nace ta ɗan jirani har naje sai ta wuce”
     Sosai Lulu ta nuna tausayawa da mata addu'ar samun lafiya. Da ga haka suka cigaba da hira har lokacin fitarta yayi. Tare suka fito da Daddy ɗin har da Mommy data samesu itama. Ta samu Ummita na jiranta, dan haka bata ɓata lokaci ba ta ɗan tattaɓa AA da masa kiss tana jaddada ma su Amrah su ɗauki saƙon Ammah a ɗakinta idan zasu wuce kai AA ɗin yini can yau kasancewar juma'a ce duk sati can ake kaisa dama. Sun amsa mata da to ta shiga mota suka wuce....

     ________★
Chapter 46 · 0% Book details